• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Buri na a ji amon tambari na a duk duniya, inji Zaliha ‘Yar Chamas

by DAGA ABBA MUHAMMAD
March 25, 2020
in Mawaƙa
0
Zaliha Haruna Dass ('Yar Chamas)

Zaliha Haruna Dass ('Yar Chamas)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ZALIHA Haruna Dass, wadda aka fi sani da suna ‘Yar Chamas ko Zaliha Mansura a harkar waƙa, ta na ɗaya daga cikin mawaƙa matasa masu haskawa a harkar waƙa, musamman a Jihar Bauchi.

 Mawaƙiyar ta na da nasibi sosai, domin ta ƙware wurin rubuta waƙoƙi iri-iri, kuma ta na rerawa. 

 ‘Yar Chamas, mawaƙiya ce mai ladabi da biyayya, ga girmama na gaba da ita, har da ma na ƙasa da ita.

 Wakilin mujallar Fim ya samu zantawa da ita, inda ta yi mana bayanin yadda aka yi ta fara waƙa, tarihin ta, waƙoƙin da ta yi da sauran muhimman abubuwa game da ita.

 FIM: Ki faɗa wa masu karatu cikakken sunan ki da tarihin rayuwar ki a taƙaice.

 ‘YAR CHAMAS: Da farko suna na Zaliha Haruna, wadda aka fi sani da Mansura ko ‘Yar Chamas. An haife ni a a garin Dass da ke Jihar Bauchi. na yi firamare a nan garin Dass, na sakandare daga aji ɗaya zuwa aji uku a Dass, daga nan  na wuce garin Nabardo na ƙarasa karatun sakandare na a can.

 FIM: Me ya ba ki sha’awar shiga harkar waƙa?

 ‘YAR CHAMAS: Gaskiya tun ina ƙarama ina da sha’awar harkar, don ina rubuta waƙa tun kafin in fara rerawa. Sannan lokacin ina yawan sauraren waƙoƙin, don ko raina a ɓace ya ke in ina jin waƙoƙi ya kan ɗan rage min ɓacin rai. A haka ina rubuta nawa, da ya ke ina da ra’ayin abin, har Allah ya ba ni iko na shiga cikin harkar.

 FIM: Ta wace hanya ki ka bi don shiga harkar waƙa?

 ‘YAR CHAMAS: Akwai wata ƙanwa ta, ta riga ni fara waƙa, a lokacin da ta yi sai na ji abin ya tsuma ni. Ganin haka sai na je situdiyon da ta yi aikin ta ni ma na fara a nan. Shi ne fa na miƙe har zuwa yanzu.

 FIM: Da wace waƙa ki ka fara?

 ‘YAR CHAMAS: Wata waƙa ce mai taken ‘So Gamon Jini’.

 FIM: Waƙoƙin da ki ka yi za su kai nawa zuwa yanzu?

 ‘YAR CHAMAS: Zuwa yanzu za su kai hamsin zuwa saba’in.

 FIM: Ki faɗa wa masu karatu wasu daga cikin waƙoƙin ki.

 ‘YAR CHAMAS: Akwai ‘Ƙanwar Maza’, ‘Matan Birni Da Na Ƙauye’, ‘Auren Sha’awa’, ‘Kowa Asalin Sa Ƙauye Ne’, ‘Halin Mu’, ‘Matan Aure’, da dai sauran su.

 FIM: Kasancewar a Jihar Bauchi ki ke, ya ki ke gudanar da harkar waƙar ki, musamman ganin a jihohin Kano, Kaduna da Jos aka fi gudanar da harkar?

 ‘YAR CHAMAS: Gaskiya yanzu a iya Bauchi na ke gudanar da harkoki na na waƙa. Ka san mu ma can mu na da ‘yan wasa a Bauchi, duk da dai ba su kai na Kano da sauran jihohin ba bunƙasa ba, amma dai su na ƙoƙari a kan harkar, kuma mu ma mu na da kishin abin, shi ne mu ma mu ke yi a nan gida, har Allah ya kai mu lokacin da za  mu fita wajen mu yi suna kowa ya san mu.

 FIM: Menene burin ki game da harkar waƙa?

 ‘YAR CHAMAS: Babban buri na in faɗaɗa sana’a ta ta waƙa, a san ni a ko’ina, sannan waƙoƙi na su shiga lungu da saƙo a faɗin duniya. Ka san ɗaukaka abin so ne, za ka ji daɗi a ce duniya ta san ka, kuma ta na alfahari da kai.

 FIM: Wanne fitaccen mawaƙi ne ki ka taɓa waƙa da shi?

 ‘YAR CHAMAS: Gaskiya babu a maza, sai dai mata. A cikin su akwai Fati Khalil, Zubaida Mu’azu (Zuby), Khairat Abdullahi, Sadiya Yarima, Farida Ajebo, da dai sauran su.

 FIM: Su Fati Nijar, Murja Baba, Maryam Fatimoti da sauran su fa? 

‘YAR CHAMAS: E, ina da burin yin waƙa da su. Ita Maryam Fantimoti ma ina da kyakkyawar alaƙa da ita, don ina iya cewa uwarɗaki na ce a yanzu haka.  Na yi mata wasu waƙoƙi, kuma ta nuna mani kulawa sosai. Ina sa rai nan ba da jimawa ba za mu yi aiki da ita.

 FIM: Yawancin mawaƙa mata ba su rubuta waƙa da kan su, sai dai a rubuta masu, wasu kuma har ɗora masu ake yi daga baya su zo ɗora nasu muryoyin. Sai ga shi ke kuma kin fita daban, da kan ki ki ke rubuta waƙa, har ma ki na rubuta wa wasu. Menene sirrin?

 ‘YAR CHAMAS: Sirrin kenan, baiwa ce daga Allah. Ka san idan Ubangiji ya yi maka kyauta, sai godiya kawai. Cikin ikon Allah, ba a taɓa koya min waƙa ba, kuma wani bai taɓa yi min rubutu na zo na yi ba; da kai na na ke yi. Na gode wa Allah da wannan kyauta da ya yi mani da ba kowa ba ne ke da shi. 

FIM: Ke wace yare ce?

 ‘YAR CHAMAS: Bajara ce ni.

 FIM: Kin taɓa waƙa da yaren ki?

 ‘YAR CHAMAS (Dariya): A’a gaskiya.

 FIM: Ki na da tunanin yi?

 ‘YAR CHAMAS: Kai, ina! Saboda ka san abin ne sai a hankali. 

 FIM: Kenan in na fahimce ki ba ki iya yaren ba? 

‘YAR CHAMAS: Gaskiya ban iya ba. Amma zan yi idan na koyo.

 FIM: Ina ki ka samu sunan ‘Yar Chamas?

 ‘YAR CHAMAS (Dariya): Wani mawaƙi mai suna Auwal Lefter ya sa min sunan a garin Jos, saboda ƙanƙanta ta, shi ne ya ke kira na da ‘Yar Chamas, tun  daga nan sunan ya bi ni.

 FIM: Ki na ɗaya daga cikin masoyan tsohuwar jaruma Mansurah Isah. Ya ki ke jin Mansurah Isah a ran ki?

 ‘YAR CHAMAS: Gaskiya in na fara jinjigo maka bayani game da soyayyar Mansurah Isah sai mun cika mujallar Fim tun daga farko har ƙarshe! Tun da na fara kallon fim, ba a taɓa yin jarumar da duk abin da ta yi ya na burge ni ba kamar Mansurah Isah. Saboda haka ne ma ake kira na da Zaliha Mansurah. Mansurah jaruma ta ce, ni ‘yar ga-ni-kashe ni ɗin ta ce ma.

 FIM: Kin taɓa haɗuwa da ita?

 ‘YAR CHAMAS: Mun sha haɗuwa, ba ma taɓawa ba.  

FIM: Ku na mu’amala sosai kenan?

 ‘YAR CHAMAS: Sosai kuwa. Domin duk lokacin da ta zo Bauchi sai ta neme ni; haka ni ma duk lokacin da na je Kano ina zuwa gidan ta. 

Zaliha Mansurah (‘Yar Chamas)

FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu a harkar waƙa?

 ‘YAR CHAMAS: Alhamdu lillahi! Nasarori shi ne masoya da Allah ke yi wa duk wani ɗan’adam kyautar sa, musamman mawaƙi. Cikin ikon Allah, duk wanda ya ji waƙoƙi na sai ya yaba. Sannan ma wasu da ba ka san su ba za su yi ta kiran ka a waya su na jinjina maka, su na ba ka lambar yabo.  

FIM: Ɓangaren ƙalubale fa?

 ‘YAR CHAMAS: To, ka san mutane, kai ka na sabgar ka can daban, amma su na yanke maka hukunci, har su yi maka hisabi a kan abin da ba shi ba ne. Ka san kowa da irin yadda ya ke ganin mutum, wani zai gan ka, ba zama da kai ya yi ba amma sai ya ba kan shi daman yanke maka hukunci da ba shi ba ne. Za ka ji ana maganar cewa mata mawaƙa ba su son aure, fasiƙai ne da sauran irin waɗannan mugayen kalamai. 

 Ni abin da na sani, idan mutum fasiƙi ne ko ba a harkar waƙa ba, zai je ya yi iskancin sa. Ko a ina ba a rasa na Allah. Amma wasu kawai sai ka ga sun yi jam’i idan su ka tashi magana. 

 A kowane irin sana’a a duniya, za ka samu ‘yan iska, za ka samu na kirki, don ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Na samu matsaloli irin waɗannan.

 Amma abin farin ciki tsakani na da iyaye na alhamdu lillahi. Su sun fahimce ni, saboda sun fi kowa sanin wacece ‘yar su, kuma sun san irin tarbiyyar da su ka ba ni.  

FIM: Kin taɓa fitar da album?

 ‘YAR CHAMAS: A’a, tukunna dai. In-sha Allahu cikin shekarar nan na ke sa ran zan fitar. 

FIM: Ina maganar aure?

 ‘YAR CHAMAS: Mu na kan gaɓa, in Allah ya kawo za mu shiga daga ciki.

 FIM: Wane kira za ki yi ga mawaƙa ‘yan’uwan ki? 

‘YAR CHAMAS: Kira na ga mawaƙa ‘yan’uwa na bai wuce in ce mu haɗa kai mu zama ‘yan’uwan juna. Mu gudu tare, mu tsira tare. Sannan kuma mu tsarkake zuciyar mu. Allah ya taimaka mana a kan sana’ar mu. 

FIM: Me za ki ce wa masoyan ki?

 ‘YAR CHAMAS: Babu abin da zan ce masu sai godiya. Na gode da so da ƙaunar da su ke nuna mani. Allah ya bar mu tare, ya kuma ba ni damar ci-gaba da yi masu waƙoƙin da za su nishaɗantar da su.

Zaliha ‘Yar Chamas (a hagu) tare da Khairat Abdullahi

Loading

Previous Post

Cutar COVID-19: MOPPAN ta dakatar da shirya finafinai

Next Post

Ni ba fitinanniya ba ce, inji Adama matar Kamaye

Related Posts

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar
Mawaƙa

Za a yi bikin naɗa Rarara Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa a Daura ranar Asabar

December 11, 2025
Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Next Post
Hajiya Zahra'u Sani, Adama matar Kamaye

Ni ba fitinanniya ba ce, inji Adama matar Kamaye

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!