• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
August 24, 2023
in Taurari
0
Safna Lawan

Safna Lawan

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SAFNA Lawan, wadda jaruma ce a  Kannywood, ta nuna takaici a game da rashin samun dama da ƙananan jarumai su ke yi a cikin masana’antar, ba kamar yadda ake yi a Hollywood da Bollywood ba.

A a lokacin tattaunawar ta da mujallar Fim, jarumar ta ce, “Yanzu kamar a Indiya ne, idan ƙaramar jaruma ta shigo za su yi yadda za su yi ne su sa duniya ta san ta har a yi alfahari da ita. To a nan ne za a gane ƙwarewar ta.

“Don haka abin da ya kamata a riƙa yi wa ƙananan jarumai idan sun shigo Kannywood a riƙa ba su sin ɗaya biyu a cikin fim, ko da kuwa kurman sin ne. A nan za a ga ƙwarewar sa har a ba shi babban fim.

“To a gaskiya mu na da ƙarancin wannan ga kuma jarumai mata ɗin. Mun yi yawa, don haka ya kamata a duba wannan matsalar.”

Safna Lawan

Dangane da nasarorin da ta samu dangane da harkar fim kuwa, Safna ta ce, “A gaskiya na samu nasarori da yawa domin na shiga manyan finafinai kamar ‘Laure’, ‘Izzar So’, ‘Ina Da Buri’, sannan na samu damar shiga fim ɗin ‘Sarah’.”

Safna ta ce tun ta na ƙarama harkar fim ke burge ta. A cewar ta, “Da man tun ina ƙarama na ke da burin shiga harkar fim, kuma sai na samu kai na a cikin maraici inda na tashi a cikin maraicin rashin uwa. Hakan sai ya ƙarfafa mini gwiwa, domin ina  son na faɗakar da jama’a kuma a yanzu ga shi na samu dama.

“Don haka a yanzu babban burin da na ke da shi na ga na samu zama babbar jaruma da duniya ta san da ita. Don haka ina fatan Allah ya cika mini burin da na ke da shi.” 

Dangane da daɗewar da ta yi a cikin harkar fim kuwa cewa ta yi, “To gaskiya a yanzu zan kai wajen shekaru takwas, amma dai a baya da na fara na kowa gida Kaduna na ci gaba da zama, sai daga baya na dawo. Kuma yanzu da dawowa ta ban fi shekara ɗaya ba. 

“Sai dai  a dawowar da na yi ina ganin alamun nasara sosai, don yanzu ina samun aiki, ana kira na duk wani babban aiki da za a yi. Wannan ya sa na ke ganin nan da ɗan lokaci kaɗan da yardar Allah zan cimma buri na na zama babbar jaruma.”

Loading

Previous Post

Waƙoƙin mu ba na batsa ba ne, na faɗakarwa ne – Hadiza Maikano

Next Post

Marubuciya Hadiza Salisu Sharif ta rasu

Related Posts

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Cewar Fanan Buzuwa: "Ba zan iya auren ɗan fim ba"
Taurari

‘Yan fim kada mu riƙe sana’a ɗaya – Fanan Buzuwa

June 11, 2023
Ahmad Muhammad Umar (D. Prince)
Taurari

Gwagwarmayar jarumi, mawaƙi Ahmad D. Prince a Kannywood

April 20, 2023
Next Post
Marigayiya Hadiza Salisu Sharif

Marubuciya Hadiza Salisu Sharif ta rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!