• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Minista Idris: Gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin gyara kurakuran baya, ba jawo wahala ba

by WAKILIN MU
August 7, 2024
in Nijeriya
0
Cewar Minista Idris: Gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin gyara kurakuran baya, ba jawo wahala ba

Alhaji Mohammed Idris a lokacin da yake gabatar da jawabi jami'an diflomasiyya a Abuja a ranar Laraba

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babban abin da gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali a kai ba shi ne ta ɗora wa ‘yan Nijeriya wahala ba, sai dai ta gyara munanan tsare-tsare da matakan da ba su dace ba waɗanda a tarihi suka kawo cikas ga cigaban Nijeriya.

A wata sanarwa da Mataimakin Ministan na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabi’u Ibrahim, ya fitar, Idris ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Laraba yayin da yake ganawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar dangane da zanga-zangar da aka yi a faɗin ƙasar.

Ya jaddada ƙudirin Shugaba Tinubu na aiwatar da gyare-gyare da nufin samar da cigaba mai ɗorewa da kuma inganta rayuwa ga ɗaukacin ‘yan ƙasa, yana mai cewa ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu na wucin-gadi ne.

Ministan ya ce, “Yana da muhimmanci mu fara da wannan bayanin: cewa Shugaba Tinubu bai zo ofis don ya jawo wahalhalu ko kuma wahalar da ’yan Nijeriya ba. Ya zo ne don warware matsalolin baya; tare da yunƙurin gyara da yawa daga cikin tsare-tsaren da ba su da kyau da kuma matakan da ba su dace ba da suka kawo mana koma-baya a matsayin mu na ƙasa shekaru da yawa.”

Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa ya hau karagar mulki ne a ɗaya daga cikin lokuta mafi ƙalubale a tarihin Nijeriya, inda ƙasar ke kashe kashi 97 na dukkan kuɗaɗen shigar ta wajen biyan basussuka; tare da yawaitar talauci, hauhawar rashin aikin yi, lalacewar ababen more rayuwa, da rashin tsaro. Yayin da take fuskantar waɗannan abubuwa masu ban tsoro, gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai tare da aiwatar da gyare-gyaren da aka daɗe ba a yi ba domin ceto tattalin arziƙin ƙasar daga durƙushewa.”

Wani na mahalartan taron lokacin da Minista yake jawabi

Ministan ya bayyana cewa kawar da tallafin man fetur ya zama dole don karkatar da kuɗaɗen zuwa sassa masu muhimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, da tsaro, wanda ke tasiri kai tsaye ga jin daɗin ’yan ƙasa da ci gaban ƙasa.

Ya amince da cewa ana shan raɗaɗin sauyin da ke tattare da wannan matakin kuma ya yi nuni da cewa Gwamnatin Tarayya ta tsara shirye-shiryen shiga tsakani don magance waɗannan ƙalubale.

“Mun dage sosai kan tabbatar da cewa an aiwatar da waɗannan ayyukan domin kawo sassauci ga ‘yan Nijeriya,” inji Idris.

Yayin da yake magana kan zanga-zangar da aka gudanar a faɗin ƙasar nan, ministan ya ce gwamnati na mutunta ‘yancin yin taro cikin lumana da ‘yancin faɗin albarkacin baki, waɗanda su ne ginshiƙin dukkan al’ummomin dimokiraɗiyya, amma ya jaddada cewa abin da ya fara a matsayin zanga-zangar lumana a wasu jihohi da kuma Babban Birnin Tarayya shi ne ba da jimawa ba wasu da suka kutsa kai cikin zanga-zangar suka karɓe ragamar tare da shirya tarzomar da ta lalata rayuka da dukiyoyi.

“An samu rahotannin ƙone-ƙone, ɓarna, sace-sace, da kuma arangama da jami’an tsaro a garuruwa da dama. Abin takaici, waɗannan al’amura sun yi sanadin asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba da kuma asarar dukiya mai yawa,” inji shi.

Idris ya tabbatar wa da jami’an diflomasiyya cewa Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da bincike kan tashe-tashen hankalin da aka yi a lokacin zanga-zangar domin a gano tare da gurfanar da duk masu hannu a cikin lamarin.

Ya ce: “Mun himmatu wajen hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.”

Alhaji Mohammed Idris a lokacin da yake gabatar da jawabi jami’an diflomasiyya a Abuja a ranar Laraba

Loading

Tags: Bola TinubuMinistaMohammed IdristarzomaYaɗa Labaraizanga-zanga
Previous Post

Mun yi gargaɗin cewa zanga-zanga za ta iya zama tarzoma – Idris

Next Post

Tsohuwar jarumar Kannywood Halima Adamu Yahaya ta yi rashin mahaifi

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Tsohuwar jarumar Kannywood Halima Adamu Yahaya ta yi rashin mahaifi

Tsohuwar jarumar Kannywood Halima Adamu Yahaya ta yi rashin mahaifi

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!