ALLAHU Akbar! A jiya Laraba, Allah ya ɗauki ran mahaifin tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Halima Adamu Yahaya.
Alhaji Al-Mustapha Idris Gabari ya rasu ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe, a Babban Asibitin Murtala da ke Kano, bayan ya shafe tsawon shekara ɗaya ya na fama da jinya.
An yi jana’izar sa a unguwar Kwanar Gaba, Kano Municipal, Jihar Kano.

Dattijon, mai kimanin shekaru 120 a duniya, ya rasu ya bar matan aure biyu da ‘ya’ya 20 da jikoki 152. Halima ce ta 11 a cikin ‘ya’yan.
Hajiya Halima ta shaida wa mujallar Fim cewa sunan da ta ke amfani da shi, Adamu Yahaya, sunan yayan mahaifiyar ta ne wanda ta taso a wurin sa.
Allah ya jiƙan Alhaji Al-Mustapha, ya kuma albarkaci dukkan abin da ya bari.