ZUWA safiyar yau Talata an tabbatar da cewa mutum 2,482,215 ne su ka kamu da cutar koronabairus a faɗin duniya, yayin da mutum 170,471 su ka mutu har lahira ta sanadiyyar ta. Duk wannan abu ya faru ne tsakanin Disamba 2019 zuwa wannan wata na Afrilu 2020. Kuma cutar ba dakatawa ta yi ba bare a sa ran za ta tsaya. Ta na cigaba da laƙume rayukan bani Adama ba tare da ƙaƙƙautawa ba.
Shin daga ina aka samu wannan cuta mai firgitarwa haka?
Daga Allah? A’a!
Aya ta 30 ta surar al-Shu’ura ta ce: “Kuma duk abin da ya same ku na daga masifa to daga abin da hannayen ku su ka ƙaddamar ne, kuma (Allah) ya na yafe akasari.”
Ayoyin Ƙur’ani da dama sun kawo irin haka ta sigogi daban-daban, wala’alla domin tabbatar wa ɗan’adam Musulmi cewa masifa, bala’i, cuta da dangogin su ba daga Allah su ke zuwa ba. Daga mutane ne. Ba kuma lallai sai mutum a ƙashin kan sa ya ja wa kan sa ba, a’a, wani mutumin can daban ma zai iya ja masa.
Fabio Giuseppe Carlo Carisio, Editan ‘Gospa News’, wata jaridar labarai ta Kiristoci da ke Italiya, ya rubuta wani dogon bahasi kan yadda, baya ga cewa ɗan’adam ne ya ƙirƙiro cutar korona, to kuma dai sai ya gwama ta da wasu sinadarai na cutar HIV/AIDS. Editan kawo dalilai da hujjoji waɗanda ya jingina wa wani kamfanin binciken magunguna na ƙasar Indiya.
‘Veterans Today’ ta wallafa wannan bahasi. A duba wannan shafin:
https://www.veteranstoday.com/2020/04/18/covid-19-created-in-lab-with-hiv-medicine-nobel-confirms-indian-research-disclosed-by-vt/
Tunda ba daga Allah cutar ta ke ba, to daga ina ta ke? Me aka aikata ya haifar da ita? Ko kuma wa ya ƙirƙiro ta?
Amsar irin wannan tambaya kai-tsaye aba ce wadda in ba mutum ne da kan sa ya yi da’awa ba, ko kuma wani bincike ingantacce ya tabbatar ba, to fa ba mai sauƙi ba ce.
Sai dai kuma a wurin Robert Francis Kennedy Jr., ɗan shekara 66, wanda ya kasance ɗan ɗan’uwan tsohon shugaban ƙasar Amurka John F. Kennedy, ya na da ra’ayin cewa hamshaƙin mai kuɗin nan da ke da kamfanin ‘Microsoft’, Bill Gates, shi ne ya ƙirƙiri wannan cuta ta korona da haɗin gwiwar wasu masu faɗa a ji a ƙasar Amurka, domin bunƙasa kamfanin sa da ke ƙirƙirar magungunan rigakafi kuma domin samun ikon juya harkar lafiya ta duniya. A duba wannan shafin:
https://www.globalresearch.ca/gates-globalist-vaccine-agenda-win-win-pharma-mandatory-vaccination/5709493
Shi ma Edita Fabio Giuseppe Carlo Carisio ya ɗauki wannan ra’ayi cewa Bill Gates, tare da haɗin bakin CIA, su ka ƙirƙiri wannan cuta ta korona. Ya rubuta wani dogon bincike da ya gabatar a jaridar sa ta yanar gizo, ‘Gospa News’. A duba wannan shafin:
https://www.gospanews.net/en/2020/03/11/coronavirus-predicted-in-bill-gates-forum-with-former-cia-massacres-italy-and-iran-after-ai-deal-teheran-bio-warfare/
A ranar 13 ga Afrilu, 2020, jaridar ‘New York Post’ ta wallafa wani labari mai taken: ‘Roger Stone: Bill Gates may have created coronavirus to microchip people’, inda jaridar ta ruwaito Roger Stone ya na zargin yiwuwar Bill Gates a matsayin wanda ya ƙirƙiro cutar korona don magungunan sa na rigakafin cutar.
Roger Stone, ɗan shekara 68, marubuci ne kuma ƙwararren wanda ake tuntuɓa ne a harkar siyasar Amurka. Kafar buzzfeednews.com ta ce labarin nan nasa da ‘New York Post’ ta wallafa ya samu karɓuwa a duniya tun a ranar. Ta ce kafafen yaɗa labaran Rasha sun ce da wa Allah ya haɗa su in ba da wannan magana ta Roger Stone ba. Kazalika gidan talbijin na ‘RT’ ya fassara maganar zuwa harshen Ispaniyanci. Sai dai kuma kafar buzzfeednews.com ta soki ‘New York Post’ da ‘RT’ a kan rashin adalcin jin ra’ayin ɗaya ɓangaren a kan wannan zargi na Roger Stone.
Saboda yawaitar zargin Bill Gates da mutane daga sassa daban-daban na duniya ke yi kan alaƙa da wannan cuta ta korona, fitacciyar mujallar nan ta harkokin kuɗi da kasuwanci ta Amurka, ‘Forbes’, ita ma ta bi ayarin kafafen da ke ƙaryata zargin da ake wa Bill Gates da cewa ai ba komai ba ne face nazariyyar makirci (‘conspiracy theory’). Ta wallafa maqala musamman a kan haka a ranar 19 ga Afrilu.
Ko akwai abin kamawa daga wannan zargi na ƙirƙirar cutar korona da ake wa Bill Gates?
Marubucin nan ya yi nazarin dalilai uku kamar haka:
1. Tun kafin bullar cutar korona da shekaru kusan shida, Bill Gates ya yi da’awar fantsamar wata cutar annoba bayan Ebola mai bin iska wadda za ta gallabi duniya. Ya ce za ta riƙa kama jama’a cikin sauƙi alhali ba sa jin alamar rashin lafiya a jikin su, har ma za su iya hawa jirgi ko su je kasuwa. Jaridar ‘ USA Today’ ta kawo batun. A duba wannan shafin:
https://www.usatoday.com/story/news/factcheck/2020/03/22/coronavirus-fact-check-did-bill-gates-predict-outbreak-2015/2890900001/
Jaridar ‘Business Insider’, wallafar ranar 10 ga Afrilu, ta ce a shekarar 2018, yayin wani taron ‘Massachusetts Medical Society’, Bill Gates ya ce, “Nan da shekara goma masu zuwa, wata cutar annoba za ta bayyana mai kama da murar nan da aka yi a shekarar 1918 wacce ta ci ran mutum miliyan 50, ya ce wannan annoba za ta ci ran mutum miliyan 30 a cikin wata shida.”
Yaya aka yi Bill Gates ya san wannan bayanin dalla-dalla game da cutar nan a matsayin sa na masanin komfuta ba masanin cututtuka ba? Me ya sa ya yi ta tattauna batun a tsawon shekarun nan? Wane shiri ne ya so duniya ta yi wanda bai fayyace mata ba kamar yadda ya fayyace nau’in cutar dalla-dalla? Waɗannan tambayoyi su na tilasta zargi.
2. Tarihin Bill Gates ba tarihi ne da ke iya ɗauke masa wannan zargi ba. Saboda rahotanni da dama sun samu magungunan sa na rigakafi da cutarwa tare da halakar da kaso mai tsoka na waɗanda aka taɓa ba wa. Ga misalai uku daga ciki:
a) A ranar 31 ga Agusta, 2014, jaridar ‘Economic Times of India’ ta wallafa wani rahoto mai taken: “Controversial vaccine studies: Why is Bill & Melinda Gates Foundation under fire from critics in India?” A ciki, rahoton ya kawo yadda aka yaudari iyayen wasu ‘ya’ya mata 16,000 a garin Gujarat na Indiya da rigakafin Bill Gates wanda daga bisani ya kassara yaran, ya halaka wasun su, lamarin da sai da ya kai gaban kotun ƙolin ƙasar. A duba wannan shafin:
https://m.economictimes.com/industry/healthcare/biotech/healthcare/controversial-vaccine-studies-why-is-bill-melinda-gates-foundation-under-fire-from-critics-in-india/articleshow/41280050.cms
b) A ranar 6 ga Janairu, 2013, kafar LALEVA.ORG ta wallafa wani labari kan yadda rigakafin ciwon sanƙarau ya yi wa yaran ƙauyen Gouro da ke arewacin ƙasar Chadi illa a watan Disamba na 2012. Kafar ta ce ta samu labarin ne daga wata jaridar Faransanci, ‘La Voix’, wacce ta ruwaito cewa a cikin yara 500 da aka yi wa rigakafin cutar ta sanƙarau, ɓangarorin jikin yara 40 da ke tsakanin shekara 7 zuwa 18 daga cikin su sun shanye. Kazalika yaran sun kamu da cutuka dangin farfaɗiya.
Rigakafin na sanƙarau ya na ɗauke da sunan MenAfriVac, kamfanin da bincike ya nuna cewa Hukumar Lafiya ta Duniya da ‘Gidauniyar Bill da Melinda Gates’ ne su ka mara masa baya. A duba wannan shafin:
http://www.laleva.org/eng/2013/01/minimum_of_40_children_paralyzed_after_new_meningitis_vaccine.html
c) A ranar 1 ga Afrilu, 2007, mujallar ‘African Affairs’, juzu’i na 106, bugu na 423 ta wallafa wata maƙalar bincike daga Maryam Yahya wadda ta nuna matakin dakatarwa da arewacin Nijeriya ya ɗauka kan cigaba da rigakafin shan’inna a watan Yuli 2003 mataki ne da bai yi hannun riga da hankali ba. Saboda wasu rahotanni sun bayyana ga Majalisar Ƙoli ta Shari’a a Nijeriya cewa rigakafin ya na kashe ƙwayoyin haihuwa ga mata kuma ya na ɗauke da wasu sinadarai na cutar HIV a cikin sa.
Shugaban majalisar, Dakta Datti Ahmad, ya ce zargin sa ga rigakafin bai taƙaita da nan gida Nijeriya ba, ya ce daga wasu ingantattun rahotanni da bayanan da ya samu a shafukan yanar gizo ne. A duba wannan shafin:
https://academic.oup.com/afraf/article/106/423/185/50647
3. Bill Gates ya na da kamfanin da a yanzu haka yavke aikin ƙirƙiro magungunan rigakafin cutar don ya sayar wa duniya. A duba wannan shafin:
https://www.weforum.org/agenda/2020/04/bill-gates-7-potential-coronavirus-vaccines/
Kenan bisa la’akari da yadda Bill Gates ya yi ta maganar aukuwar wannan cuta tun kimanin shekara shida baya, da yadda tarihinvsa ya nuna shi mutum ne ba amintacce ba game da lamarin magungunan rigakafi, da kuma yadda a yanzu bayan fantsamar cutar ta korona ya duƙufa ga ƙirƙiro magungunan rigakafin cutar, mai zargi ba zai yi laifi ba idan ya zargi hamshaƙin ɗan kasuwar da hannu dumu-dumu cikin ƙirƙirar wannan cuta. Ko ba komai dai masana hikimar rayuwa sun ce yayin da wani mummunan rikitaccen lamari ya taso, aka rasa gane kan sa, to a duba wanda zai amfana ko yavke amfana daga hakan.
Bill Gates zai amfana da batun rigakafin cutar nan. Kuma burin sa na raguwar mutanen duniya zai tabbata daga samuwar cutar. Kazalika muradin sa na ID2020 (wata ƙwayar na’ura mai kama da kan barjajjiyar ƙwayar shinkafa) wacce za a sa a jikin kowane mutumin duniya don sanin juna, zai cika. Kamfanin sa na ‘Microsoft’ na daga cikin masu ɗaukar nauyin wannan babban aiki. A duba wannan shafin:
https://secure.avaaz.org/en/community_petitions/yes__id2020/?atfyoqb&newuser=1&lgpdname
Bisa ga duk waɗannan ne tambayar sama ta ke nanata kan ta: Shin Bill Gates abin yarda ne game da batun cutar nan ta korona?
* Muhammad Bin Ibrahim shi ne Babban Editan TAWADA