DARAKTA Amir Mairose, wanda ya daɗe ana damawa da shi a Kannywood, ya yi kira ga ‘yan fim da su taimaka su riƙa sanya shi a finafinan su kamar yadda ya riƙa yi masu a baya.
Mairose dai ya rikiɗe ne ya koma jarumi a cikin shirin nan mai farin jini na ‘Daɗin Kowa’ da ake nunawa a Arewa24 inda ya ke fitowa a matsayin wani ɗan daba mai suna Garzali.
A tattaunawar da mujallar Fim ta yi da shi, sabon jarumin ya ce, “Kamar dai yadda aka san ni ina yin daraktin tun wajen shekaru ashirin, wato tun daga fim ɗin ‘Jarin Ibro’, sannan kuma ni furodusa ne tsawon wannan lokacin, to har kullum ita rayuwa al’amuran su na canzawa. Wannan ya sa na ga a yanzu ni ma lokaci ne da ya kamata a ce na canza ɗin, kuma na gano su jarumai su na da wata alfarma idan sun je wani waje.”

Ya ci gaba da cewa, “Hakan ce ta sa na rubuta labaran da na ke ganin zan hau su a matsayin jarumi. To amma dai ban samu yi ba sai kawai na samu kai na a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ a matsayin jarumin duk da cewa farkon lokacin da zan fara sai da ƙwalla ta zo mini, na ga a baya ni na ke sawa a yi, kuma a yanzu na dawo ni zan tsaya a ba ni umarnin abin da zan yi, kuma aka ɗauko wani rol na daba da ban san shi ba aka ba ni, amma dai na koma na sabar wa kai na yanayin ɗan daba mai shaye-shaye, kuma alhamdu lillah na yi abin da ake so a gani a fim ɗin.
“Kuma daga nan duniya ta ɗauka, duk inda na je ana kiran sunan Garzali, har ta kai a yanzu na samu karɓuwar da ban taɓa tunanin ta ba. Don ko da na je Nijar a kwanakin baya sai da aka ɓoye ni! Kuma daga nan na gano shi fim alfarma ce a duniya.”
Amir ya bayyana farin ciki da samun wannan damar da ya yi. Ya ce a yanzu har an fara kiran sa zuwa wasu finafinan.
“Ina fatan ‘yan fim da na taimaka wa a baya a yanzu za su rama wa kura aniyar ta,” inji shi.
Haka kuma Amir Mairose ya yi godiya ga mutanen da su ka karɓe shi a matsayin jarumi, tare da fatan za su ci gaba da kula da shi idan za a yi fim kamar yadda ya riƙa yi wa sauran jarumai a baya.