1. Dare sahibi na zo ka ɗauken ka tai da ni,
Tunanin ka ya zo min da shauƙin ka tun tuni.
2. Idan na yi aiki har ya kai na ji na gaji,
Na kan ce aboki zo da sauri ka cin mani.
3. A nan zan ga rana na shirin za ta bar gari,
Ta koma fatsi har rawaya sai ka ce rini.
4. Idan na ga tai yamma da girman ta ya daɗu,
Ta faɗa sujuda gun sa Allahu, ya gwani.
5. Da yara da manya sa da sarki da dogarai,
Da attajiri, malam, direba da maigini.
6. Gama kantuna duk za a kama a rurrufe,
Da shago na kaya ko kemis inda magani.
7. A kan daina duk harka gama Rabbu yai kira,
Idan ya yi umarni fa ba wanda zai hani.
8. Idan tun da safe mun ta harka mu na biɗa,
Laka za ta ƙare ko mu na ji mu na gani.
9. Waya ce a ce aiki ta ke duk wuni zubur,
Fa cajin ta zai ƙare, maridi da ba jini.
10. Mu ruga wajen caji da sauri mu na bari,
Hakan nan mu ke tarbar dare babu lamuni.
11. Dare sahibi na zo ka cajin mu ‘yan’adam,
Mu kwanta mu huta zahiri har da baɗini.
12. Na lumshe idanu kunnuwa duk su daina ji,
Gaɓuɓɓa su mimmiƙe su huta na zamani.
13. Gari kaf ya ɗau sanyi duhu duk ya mamaye,
Fa bacci ya ɗau kowa da babba da ƙanƙani.
14. Idan alfijir ya zo fa cajin mu ya cika,
Subahi ya numfaso—kalamin sa mai sani.
15. Mu farka mu na murna kuzarin mu ya haɗu,
Mu shirya mu ɗau himma ta nema cikin wuni.
16. Mu gode wa Allah mai dare Jalla mai wuni,
Mu bauta wa Sarki shi kaɗai ba mu sa wani.
Bauchi
22 ga Maris, 2021
2:22 na safe
Dakta Tilde shi ne Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi