• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 8, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Dinar K-WAN: Za mu ƙwaci ‘yancin mu daga mazan Kannywood – Hauwa Edita

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
May 17, 2021
in Labarai
1
Dinar K-WAN: Za mu ƙwaci ‘yancin mu daga mazan Kannywood – Hauwa Edita
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAR ƙungiyar matan masana’antar finafinan Hausa (Kannywood Women Association of Nigeria, K-WAN), Hajiya Hauwa A. Bello (Edita), ta bayyana cewa ‘ya’yan ƙungiyar sun shirya tsaf domin fatattakar maza daga dukkan ayyukan da ya kamata a ce mata ne su ke gudanar da su a masana’antar.

Ta faɗi haka ne  a jiya Lahadi, 16 ga Mayu, 2021 a wajen wata gagarumar walimar Sallah da ƙungiyar ta shirya wa ‘ya’yan ta a ɗakin taro na otal ɗin Ni’ima da ke Kano.

Taron shi ne irin sa na farko da ƙungiyar ta shirya tun da aka kafa ta.

Lokacin da ta ke ƙarin bayani ga mujallar Fim a yayin taron, shugabar Hauwa Edita ta bayyana maƙasudin shirya wannan taro da cewa, “Mun haɗa wannan taron saboda mu haɗa kan matan da ke cikin wannan masana’anta ta shirya finafinai, mu yi zumunci da kuma kawo muhimman batutuwa kan yadda zai sa matan ciki su samu abin da ya kamata saboda ga baki ɗaya duk wani abu da ake yi ba a ba wa mata fifiko, ko da kuwa shugabanci idan aka kalla za a ga ba a fiya ba wa mata muhimmanci ba.

“To amma kuma idan matan ne su kaɗai su za su sarrafa yadda za su tafiyar da abubuwan su da kuma yadda ya kamata su gabatar da al’amuran su.

“Duk da cewa wannan ƙungiya har yanzu jaririya ce kuma mu na nan mu na ririta ‘ya‘yan ta, yanzu haka ƙoƙari ake a ga an haɗa kan mata, kuma duk inda ake so a haɗa kan mata sai an haɗu domin a faɗa masu irin manufar abin da ya sa ma aka ƙirƙiri wannan ƙungiya.

“Kuma wannan shi ne taron mu karon farko da mu ka shiga mu ka gaya wa mata manufar wannan ƙungiyar. 

“Taron da aka yi ina da yaƙinin zai ƙara zaburar da sauran mata wajen ganin sun zaburo domin a yi da su.

Hauwa A. Bello (a tsakiya) tare da Maryam Fantimoti (a hagu) da Asma’u Sani

“Kuma wani abu ma, wannan ƙungiyar jagora ce ta ko ka shigo ko ba ka shigo ba, matuƙar ki na Kannywood, wannan ƙungiya taki ce.”

Shugabar ta ƙara da cewa, “Abin da mu ka hanga tun farko ba mu haɗa wannan ƙungiyar ba shi ne a duk duniya yanzu ba abin da ake so kamar mata masu shirya fim, kuma a harkar fim akwai wurare da dama da mata ne ya kamata su yi amma duk baki ɗaya an je an tare an ce sai maza. To mu yanzu so mu ke mu fatattaki maza a wuraren nan.

“Misali, idan aka ɗauki kwalliya, yanzu mata mu ke so su dinga yi saboda yanzu mata a gari su na da yawa waɗanda su ka iya kwalliya amma ba sa zuwa masana’antar fim in za a yi fim a ɗauke su. To, so mu ke mukori mazan matan su dinga yi.

“Amma mu ba mu ce a ba mu na maza ba, amma kuma na mata mata mu ke so su yi.

“Abinci ma mata mu ke so su yi.

“Saboda haka akwai abubuwa da dama da mu ke so mu ƙwata mata su dinga yi.”

Hauwa ta yi nuni da cewa hoɓɓasan da su ke yi a ƙungiyance ya fara haifar da kyakkyawan sakamako. Ta ce, “Duba da yadda mu ka tashi a tsaye, kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu saboda yanzu  K-WAN mun yi abin da ba a taɓa yi ba a masana’antar nan. Shi yanzu mu ke yi, mu ka kuma haɗa kan mu har ta kai ga mun samu furodusa a cikin wannan ƙungiya sama da ashirin. Ko da wannan ma ai kwalliya ta biya ƙuɗin sabulu.
“Kuma wannan ƙalubale ne mu ke jefawa zuwa ga maza; su ma ya kamata su yi ƙoƙari su yunƙura. Ya kamata a ce su na haka su na haɗuwa su na yin aiki ɗaya da masana’antar tamu yanzu ta fi haka.” 

Bayan kammala taron, mujallar Fim ta ji ta bakin wasu daga cikin mahalarta walimar kan wannan taro. 

A tsaye: Sadiya Muhammad (Gyale) (a hagu) da Siddiqa Jibrin Sarki, sai furodusa Hafsat Sulaiman (a zaune)

Shahararriyar marubuciyar nan Fauziyya D. Sulaiman ta bayyana jin daɗin ta bisa wannan hoɓɓasa da K-WAN ta yi wajen ganin an haɗa kan matan masana’antar, kama daga mawaƙa, marubuta da ma sauran jarumai baki ɗaya wuri guda domin a gudu tare a tsira tare.

Hannatu Bashir, ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yan wannan ƙungiya, ita ma ta bayyana wa mujallar Fim cewa, “Wannan taro da mu ka yi ba abin da za mu ce sai godiya, saboda taron ya bada mamaki fiye da yadda ake tsammani. Mata sun fito sun nuna mana goyon baya sosai. 

“Ina kuma amfani da wannan damar na yi kira ga mata da su zo su rungumi wannan ƙungiyar hannu biyu-biyu saboda wanna ƙungiyar wata inuwa ce da za ta taimake mu mu mata, saboda wani abu ne da ba a yi, yanzu aka fara, da man kuma ƙungiyar ta ƙunshi tsoffi da matasa da ma yara baki ɗaya. 

“Sannan wannan ƙungiyar za ta taimaka musamman kan wasu matsalolin da aka samu a baya na ƙananan jarumai masu tasowa, wanda kuma  rashin shiga cikin manyan su duk shi ya janyo, amma yanzu wannan ƙungiyar mu na fatan za ta yi ƙoƙarin haɗa kawunan mu da kuma samar mana mafita a lokacin da ya kamata.’’

Taron dai ya samu halartar ɗimbin mata daga ko’ina daga faɗin wannan ƙasa. 

Mujallar Fim ta yi tozali da jarumai mawaƙa da marubuta irin su Sadiya Gyale, Hafsat Idris, Saratu Giɗaɗo, Aishatu Mahuta, Asma’u Sani, Fauziya D. Sulaiman, Ruƙayya Dawayya, Hauwa Waraka, ‘Yan Biyun Daɗin Kowa, Fati Slow, Hadizan Saima, Maryam CTV, Teema Makamashi, Hannatu Bashir, Ladidi Abdullahi (Tubeless), Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi), Hadiza Kabara, Hadiza Maitama, Aisha B. Umar da su.

A ƙarshen jawabai, an nishaɗantar da mahalarta taron ta hanyar rawa da waƙa, sannan an ci an sha an sada zumunci

Su Teema Makamashi, Hafsat Idris da Hadizan Saima
Lokacin rawa
Wani sashe na mahalartan taron
Mata na cashewa a taron

Loading

Previous Post

Asase ya kafa gidauniyar taimakon matasa don su guji daba da shaye-shaye

Next Post

Abin da ke jawo ƙwacen akawun na Fesbuk

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Abin da ke jawo ƙwacen akawun na Fesbuk

Abin da ke jawo ƙwacen akawun na Fesbuk

Comments 1

  1. Abubakar says:
    4 years ago

    Slm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!