• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Dole ne a haɗa addini da siyasa don cigaban ƙasa – Idris

by WAKILIN MU
March 8, 2025
in Nijeriya
0
Dole ne a haɗa addini da siyasa don cigaban ƙasa – Idris

Alhaji Mohammed Idris yana gabatar da jawabi a taron Laccar Ramadan a Kaduna a yau

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada cewa dole ne imani, siyasa, da mulki su tafi tare domin gina makomar Nijeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Kaduna yayin da yake jawabi a taron Laccar Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), da Muryar Nijeriya (VON) suka shirya.

Taron, wanda ke da taken “Imani, Siyasa da Mulki: Shiga Malaman Addini Siyasa da Tasirin sa,” ya ba da damar tattaunawa kan rawar da shugabannin addini suke takawa a harkokin mulki.

Idris ya ce: “Ina da yaƙinin cewa wannan jerin bitoci za su ci gaba da haifar da sauyi mai kyau a ƙasar mu.

“A cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda iyalai ke taruwa don yin addu’o’i, nazari, haɗin kai, da tausayin juna, tasirin abubuwan da ke cikin jigon yau—wato addini, siyasa, da mulki—yana da alaƙa da jiya, yau, da gobe. Babu shakka, wannan abu ne da dole mu ci gaba da fahimtar shi da sarrafa shi.

“Amma yayin da muke tafiya a cikin waɗannan al’amura, muna fuskantar sauye-sauyen siyasa na cikin gida da na waje da ke shafar fahimtar mu kan haɗin kan ƙasa.”

Dandazon jama’a a wurin taron laccar

Ministan ya yaba da halartar manyan baƙi a wajen taron, ciki har da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani; da Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Malam Idi Mukhtar Maiha, da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, wanda shi ne uban taron.

Haka nan, ya jinjina wa fitattun malamai irin su Sheikh Morufu Onike Abdulazeez da Farfesa Isma’ila Shehu, yana mai cewa gudunmawar su tana da matuƙar muhimmanci.

Idris ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan wata mai alfarma na Ramadan don yin nazari, haɗin kai, da sabunta aniyar su ta cigaban ƙasa.

Ya kuma jaddada nasarorin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta samu, musamman amincewa da kasafin kuɗi na naira tiriliyan 54, wanda ya mayar da hankali kan ɓangarori masu muhimmanci kamar tsaro, ilimi, ababen more rayuwa, kiwon lafiya, da noma.

Ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa bisa ƙirƙiro Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi, yana mai bayyana hakan a matsayin wata babbar manufa da za ta kawo cigaba ga tattalin arziki da zaman lafiya a ƙasa.

“Yayin da muke tafiya a cikin harkokin siyasa da mulki, da tasirin su kan yanke shawara, yana da matuƙar muhimmanci mu riƙa yin zaɓi nagari,” inji shi.

Ministan ya kammala da yin kira ga ‘yan ƙasa da su rungumi ɗabi’un ƙauna, tausayi, da juriya a lokacin watan Ramadan da bayan sa.

“Allah ya albarkaci iyalan mu, ya shiryar da mu, ya kuma ba mu hikima a dukkan al’amuran mu. Ramadan Kareem,” inji shi.

Ministoci tare da Gwamna Uba Sani da Sarkin Zazzau a wurin taron

Loading

Tags: Alhaji Mohammed IdrisLaccar Ramadan
Previous Post

An naɗa Iskeel Janar-Manajan tashar talbijin ta Tozali

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin rasuwar masanin aikin hulɗa da jama’a Kabir Ɗangogo

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin rasuwar masanin aikin hulɗa da jama’a Kabir Ɗangogo

Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin rasuwar masanin aikin hulɗa da jama'a Kabir Ɗangogo

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!