* Bayan zarrar da ta yi a fagen waƙa, Fati Nijar ta rikiɗe zuwa jaruma inda ta ke da buruka guda huɗu. Ko muradin ta zai biya kuwa?
BINTA Labaran ta na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙa a ƙasar Hausa. Fasahar ta ta karaɗe har wajen da ba a jin Hausar. Hajiyar, wadda aka fi sani da Fati Nijar, ta yi fice a waƙoƙin fim masu yawan gaske tun kafin mawaƙa su riƙa fito da fayafayen waƙoƙin su, wato album. To amma waƙar ta ta ‘Girma-Girma’, wadda a album ta fito, ita ce ta ƙara ɗaga tauraruwar ta sama har kowa na iya ganin ta. Bayan wannan album ɗin, ta fito da wasu fayafayen, ciki har da na gani. A yau, masu kallon talabijin su kan gan ta a akwatunan talabijin ɗin su, ta na yin waƙoƙi.
Bugu da ƙari, Fati ta yi fice wajen waƙoƙin siyasa da na bukukuwa, sannan mutane da dama sun gan ta ido-da-ido a bukukuwan aure da tarurrukan siyasa, inda ta samu maƙudan kuɗaɗe. Ana iya cewa Fati ta na daga cikin ’yan fim masu arzikin dukiya duk da yake ta na nuƙu-nuƙu da samun ta, ba ta so a gane.
Idan kun tuna, a hirarrakin mu da Fati a baya mun taɓa kawo maku wata hira inda ta bayyana ƙudirin ta na zama ’yar wasa, wato ba ta tsaya a fagen waƙa ba kaɗai. To, a yanzu dai ta rikiɗe zuwa jarumar fim wadda nan gaba kaɗan ta ke sa ran ta zamo a cikin jerin fitattun jarumai. A ’yan kwanakin nan, hotunan ta sun yi ta yaɗuwa a intanet tare da fitattun jarumai irin su Ali Nuhu da Sadiq Sani Sadiq su na ɗaukar fim. Hakan ya nuna wa duniya cewa Fati dai ta tsunduma cikin ɓangaren fitowa a wasannin fim.
Wakilin mujallar Fim ya samu Fati a ofishin ta a Kano domin ya ji dalilin ta na rikiɗa daga zabiya zuwa ’yar wasa. A cewar ta, kamfanin ta, wato ‘Girma-Girma Kreative Investments Ltd.’, zai shirya finafinai aƙalla goma. Ga shi har sun shirya na farkon, mai suna ‘Sakatariya’. To, ta bar waƙar ne ko kuma haɗawa za ta yi da fim? Ga mu ga Fati:
FIM: Fati Nijar, ke ba ɓoyayyiya ba ce a wannan masana’antar, to amma duniya ta fi sanin ki a fagen waƙa. Yanzu kuma sai ga shi ki na neman sauya akalar ki zuwa fitowa a matsayin jarumar fim. Ko me ya jawo hakan?
FATI NIJAR: To, (dariya) ina son mutane su sani, ina da wani buri da na ke da su guda huɗu da na ke son na ga na cim musu. Na ɗaya, ina so na yi koyi da mawaƙan duniya saboda duk wata mawaƙiyar da ta shahara a duniya, daga ƙarshe za ka ga ta yi fim.

Na biyu kuma shi ne, idan zan fara yin aktin, na fara da Ali Nuhu. Na uku, ina so na shiga cikin harkar fim ɗin na ga yadda harkar ta ke don in ga waƙa da fim wanne ya fi wahala.
Sai kuma na huɗu, ina ganin ga karɓuwa ta a wajen jama’a don na ga masoyan wanne su ka fi so: na yi waƙar ko kuma fim?
Don haka na ke son masoya na a duk lokacin da su ka ga na fito a fim, su yi min addu’a ta fatan alheri kuma a ba ni goyon baya.
FIM: Ganin kin shafe tsawon lokaci a masana’antar fim ki na waƙa, wai tun da farko kin zo ne da tunanin ki yi fim ko da niyyar waƙa kawai ki ka zo?
FATI NIJAR: To gaskiyar magana dai dukkan su biyun babu wanda na taso da burin na yi, sai daga baya waƙar ma Allah ya sa ina da abinci a ciki na shiga ciki. Kuma fim ba wai ina da burin na fito a ciki ba ne tun farkon shigowa ta harkar; yanzu ne dai kawai na ke so na gwada na ga wanda ya fi, kamar yadda na faɗa maka a baya.
FIM: Daga lokacin da ki ka furta za ki fara fim zuwa yanzu, ya ki ka samu kan ki, ganin cewar da waƙa ki ka saba?
FATI NIJAR: Gaskiya ne. Kawai da farko na ji kamar ba zan iya ba saboda fim magana ce, ita kuma waƙa za ka shiga situdiyo ka na rerawa. To, gaskiya na so na gamu da matsala saboda idan magana ta yi min wahala, amma dai daga ƙarshe na fahimci yadda tsarin ya ke.
FIM: Ɗaya daga cikin muradan ki guda huɗu shi ne ki yi fim da Ali Nuhu. Yanzu kin cimma burin kenan?
FATI NIJAR: E, na samu dama, yanzu a wannan ɓangaren buri na ya gama cika.

FIM: Fim ɗin naki ne na kan ki? Kuma wanne burin ki ke so ki cimmawa a game da finafinan naki?
FATI NIJAR: E, yanzu na fara da fim na guda ɗaya kuma na kamfani na ne. Sannan ina da burin nan gaba na yi fim kamar guda goma a kamfani na. Amma dai ban sani ba nan gaba idan wasu su ka ga ina yi kuma na burge su su kira ni na yi musu. Amma dai ni nawa ba zan wuce na yi goma ba a kamfani na.
FIM: Kenan dai a yanzu kin ware wasu kuɗi ne a kamfanin ki wanda za ki yi fim ki nuna wa masoyan ki ke ma fa za ki iya taka rawa a fim?
FATI NIJAR: Gaskiya ne. Ka san harkar nan wata irin harka ce wadda idan har ba ka da jari a cikin ta, to zai zama duk wani abu da za a yi to sai a yi babu kai. To sai na ga ni Allah ya hore min, zan iya yin fim nawa na kai na, don haka na ware kuɗi domin na yi wa kai na fim.
FIM: Ko za ki faɗa mana sunan finafinan da kamfanin ki zai shirya?
FATI NIJAR: To da yake abin ya na da yawa, sai dai na faɗa maka wanda mu ka fara a yanzu. Sunan sa ‘Sakatariya’. Shi ne mu ke kan aikin sa a yanzu.
FIM: Ke ce za ki rinƙa fitowa a matsayin jarumar finafinan kamfanin ki ko za ki rinƙa saka wasu matan?
FATI NIJAR: E to, ya danganta da labarin. Don ya kasance finafinai na ne ba zai yiwu ba a ce ni zan ja fim ɗin. Kawai dai ni dai buri na shi ne na fito a cikin fim ɗin, amma ba lallai ba ne ya zama kowanne ni ce jarumar, sai dai wanda ya dace na fito a matsayin jaruma.

Ka san akwai kurakuran da mutanen mu su ke yi; sai ka ga labari ko ya dace da su ko bai dace ba sai su ce tunda kuɗin su ne su za su ja fim ɗin. Ka ga wannan ba tsari ba ne.
FIM: To shi wannan fim ɗin da ki ka fara ke ce jarumar sa?
FATI NIJAR: E, ni ce jarumar, kuma daraktan ne ya ce fim ɗin ya dace da ni. Kuma fim ne da ya ke ƙunshe da cin amana da yaudara, sai kuma sadaukarwa. Shi ne jigon labarin.
FIM: Kin saba ki tsaya a situdiyo ki na rera waƙa, ta yadda har abin ya zame maki jiki. Sai kuma ga shi yanzu kin samu kan ki a wani aiki da ya zama umarni za a riƙa ba ki. Ko yaya ki ke ji a lokacin ɗaukar fim ɗin?
FATI NIJAR: Gaskiya ne. To wannan shi ne bambanci da sana’ar waƙa da ta fim. Waƙa kai za ka tsara abin da ka ke so da kan ka, yayin da fim kuma umarni za a rinƙa ba ka. To gaskiya akwai bambanci sosai.
FIM: Ya ki ka samu kan ki a harkar fim kasancewar ki baƙuwa a fagen?
FATI NIJAR: E, gaskiya na ji wani abu daban saboda rashin sabo. Idan kuma ka ce za ka yi shi a lokaci guda, za ka sha wahala, don haka sai ka ji kamar ba za ka iya ba. Kuma na ji hakan, don na yi tunani kafin ma a fara zuciya ta ta na gaya min kamar na fasa, kawai dai sai na daure na yi.
FIM: Wanne irin matsayi ki ke so ki kai a fagen fim?
FATI NIJAR: A gaskiya dangane da fim ina so na sha gaban duk wata jaruma, na danne ta; don kowane mutum shi ne burin sa ya fi kowa a harkar da ya sa a gaba. To ni ma buri na in wuce kowace jaruma.
FIM: Amma kin ce za ki riƙa zuwa ki yi fim idan aka gayyace ki. Ba kya ganin za a ga kasancewar ki fitacciyar mawaƙiya za ki yi tsada?
FATI NIJAR: E to, (dariya) tsada ai ya danganta. Zan iya yin tsada kuma zan kasance mai sauƙi, don haka ya danganta dai da mutumin da za mu yi mu’amala da shi idan harkar fim ɗin ta taso, don a cikin harka za ka ga akwai wanda taku ta zo ɗaya da shi, wanda akwai alfarma.
FIM: Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu ko kin fuskanci wasu matsaloli?
FATI NIJAR: To ni dai har zuwa yanzu ban samu wata matsala ba. Kuma ai yanzu ma ne na farko, ban shiga cikin ta gaba ɗaya ba. Sai dai ko nan gaba.
FIM: Tunda an san ki a waƙa, ga shi kuma kin koma fim, wanne kira za ki yi ga masoyan ki?
FATI NIJAR: To kira na da kuma fata na ga masoya na shi ne su taya ni da addu’a. Kuma kasancewar na fara yin fim ba shi ne na bar waƙa ba, zan ci gaba da yi.

FIM: Menene saƙon ki na ƙarshe?
FATI NIJAR: Saƙo na shi ne ina yi wa masoya na fatan alkhairi, kuma su taya mu da addu’a Allah ya sa mu dace, kuma ina godiya a gare su.