TSOHUWAR jaruma a Kannywood, Fauziyya Sani, wadda aka fi sani da Fauziyya Maikyau, ta shirya wani taro na musamman domin murnar zagayowar ranar haihuwar ta.
A jiya Asabar, 7 ga Oktoba 2023 aka yi taron a gidan ta da ke unguwar Badawa cikin garin Kano, inda ƙawaye da abokan arziƙi su ka taru domin taya ta murna.
Waɗanda su ka halarta sun haɗa da Samira Ahmad, Mansurah Isah, Sadiya Gyale da Fati Yola.

A jawabin ta kan taron, Fauziyya ta nuna farin ciki da Allah ya nuna mata wannan ranar da ta zama muhimmiya a cikin rayuwar ta.
Kuma ta yi godiya ga dukkan masoyan ta da su ka halarta don taya ta murna da ma waɗanda ba su samu damar zuwa ba.
