AN ɗaura auren furodusa kuma ɗan kasuwa a Kannywood, Alhaji Rabi’u Koli, a ranar Asabar a Kaduna.
An ɗaura auren nasa da sahibar sa, Malama A’isha Usman, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, bayan sallar azahar a wani masallaci da ke Titin Fulani, unguwar Badarawa, a kan sadaki N200,000.
‘Yan fim ba su samu damar halartar ɗaurin auren ba, sai dai da dama sun tura masa saƙonnin fatan alkhairi.
Abokan sa da suka halarta sun haɗa da Alhaji Aminu Sokoto, Alhaji Ali Mato, Surajo Ɓoyi Dutsin-ma, Mustapha Mista La, Sani Bazalla, sai kuma ma’aikatan NNPC da shugabannin direbobin motocin sufuri da ke NDA Bus-stop.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.