FURODUSA kuma ɗan kasuwa a Kannywood, mazaunin Kaduna Alhaji Rabi’u Koli, zai yi aure bayan rasuwar matar sa da shekara kusan biyu.
Za a ɗaura auren sa da sahibar sa Malama A’isha Usman a ranar Asabar, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, bayan sallar azahar a wani masallaci da ke Titin Fulani, unguwar Badarawa, Kaduna.
A saƙon gayyatar, Rabi’u Koli ya ce duk wanda bai samu damar zuwa ba, ya yi masu addu’a.
Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta taɓa ba ku labarin cewa a daren ranar Asabar, 30 ga Satumba, 2023 Allah ya yi matar sa, Hajiya Sabira Ishaq Koli, rasuwa.