A MAKON gobe furodusan nan na Kannywood, Alhaji Abubakar Bashir Maishadda, zai ƙaddamar da wani katafaren shagon sayar da tufafi a Kano mai suna ‘Maishadda Textile’.
A sanarwar da ya fitar kan taron da za a yi, furodusan ya miƙa saƙon gayyata ga dukkan masoyan sa da abokan sana’ar sa zuwa wurin bikin.
A sanarwar da ya wallafa a Instagram, Maishadda ya ce: “Da sunan Allah, mai rahama, mai jinƙai.
Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W.).
“Ni Abubakar Bashir Maishadda ina farin cikin gayyatar dukkanin masoya na da su ke faɗin Nijeriya, da ma abokanan sana’a ta zuwa wurin buɗe shago na, ‘Maishadda Textile’, na saida yaduka, shaddoji, huluna, jakunkuna, takalma, dogayen riguna da sauran su.”
Za a buɗe wannan shago a ranar Juma’a, 30 ga Satumba, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, a shago lamba 5, MYCA Plaza a kan Titin gidan Zu a Kano.
Furodusan ya ce: “Haƙiƙa, halartar ku wurin na da matuƙar muhimmanci a gare ni. Allah ya ba da ikon halarta, amin summa amin.”
Sai dai ya ce duk wanda bai samu damar zuwa ba zai iya taya shi da addu’a.
Comments 1