GASAR Hikayata, gasar rubuta ƙirƙirarrun hikayoyi na Hausa ce wadda gidan rediyon BBC Hausa ke shiryawa musamman domin mata matasa. A duk shekara ake shirya gasar kuma a yi gagarumin bikin raba kyaututtuka ga gwarazan gasar mutum uku a Abuja.
A bana, ana cikin karo na takwas na gasar. Hasali ma dai a yau ne za a yi bikin karramawar da ba da kyaututtuka ga zakaru uku da su ka zo matakin ƙarshe a gasar.
Kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito, gwarazan uku kowacce sunan ta A’isha, wato: A’isha Adam Hussaini daga Kano, A’isha Abdullahi Yabo daga Gusau, Jihar Zamfara, da A’isha Sani Abdullahi daga Jos, Jihar Filato.
Mujallar Fim ta tattauna da waɗannan zaratan marubutan onlayin ɗin a ofishin BBC da ke Abuja ɗazu da yamma a kan tarihin su, yadda su ka zama marubuta, yanayin rubutun su, yadda su ka shiga gasar Hikayata, da burin su a rayuwa.
Ga yadda tattaunawar ta kasance:
FIM: Ki faɗa mana sunan ki da da tarihin ki a taƙaice.
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Ni dai suna na A’isha Sani Abdullahi. Ni haifaffiyar Jihar Filato ce, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Na yi firamare da sakandare a Maria Memorial College da ke Jos. Sannan yanzu ina neman gurbin karatu a Jami’ar Jihar Jos.
FIM: Shekarar ki nawa?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Ashirin da ɗaya.
FIM: Wato matakin karatu na sakandare ki ka yi, ki na neman mataki na gaba kenan?
A’ISHA SANI ABDULLAH: E.
FIM: Ke kuma yaya sunan ki da tarihin ki a taƙaice?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Suna na A’isha Adam Hussaini. An haife ni a unguwar PRP, Nassarawa Local Government da ke Kanon Dabon Nijeriya. Shekaru na ashirin da bakwai. Na yi karatu na tun daga firamare har zuwa NCE a nan Kano, sannan yanzu haka ina digiri ɗi na a FCE Kano. Ina da aure da yara biyu.
FIM: Ke ma yaya sunan ki da tarihin ki a taƙaice?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Suna na A’isha Abdullahi Yabo. An haife ni a garin Gusau, Jihar Zamfara. Shekaru na talatin. Na yi karatun Islamiyya a Zawiyyar Shehu Balarabe Gusau.
FIM: Iya karatun da ki ka yi kenan?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: E, iyaka ta karatun Islamiyya.

FIM: Ba ki yi karatun boko ba?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: A’a.
FIM: Ke da ki ka yi makarantar Islamiyya, ba ki yi boko ba, ya aka yi ki ka koyi rubutu da haruffan boko?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Gaskiya ba na ce wai ga wanda ya koya min ba. Kawai dai abin da na sani, na yi karatun islamiyya a Zawiyyar Shehu Balarabe Gusau, wanda da ma idan dai abu ne na Hausa, karatu na Hausa, in ka na da karatun ka na Islamiyya, kuma daidai gwargwado ka sani ka fahimta, to ba zai yi maka wahala ba. Shi wannan karatu da na yi na Islamiyya nan Zawiyyar Shehu Balarabe Usman, shi ne dai ya ba ni dama na kai matsayin da na ke da shi a kai yanzu. Ina yawan karanta littafan Hausa. A kwana a tashi har hakan ya sanya na fara fahimtar yaya zan yi rubutu, kuma ta yaya zan rubuta abin da zai isar da saƙo ga al’umma.
FIM: Kamar waɗanne littattafai ne ki ka riƙa karantawa, wanda su ka saka maki shauƙin ke ma ki zama marubuciya?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: To, farko littafin da na fara karatu shi ne ‘So’, littafin marigayiya Hadiza Salisu Shu’aibu. Daga nan ina karatun littafin su Anti Fauziyya D. Sulaiman, Anti Baby ‘Yan Awaki da Anti Maimuna Beli. Littattafan su ne gaskiya na ke karatu; da Balkisu H. Muhammad, duk littattafan su ne na ke yawan karatu har na ji ina sha’awar ni ma wata rana a ce na zama marubuciya da zan faɗakar da al’umma. A lokacin ina ganin kamar ba zan iya ba idan na tuna cewar ai ban yi boko ba, to da ya ke abin na Allah ne, sai ga shi yau na tsinci kai na a matsayin marubuciya, kuma daidai gwargwado ina rubutun abin da jama’a su ke alfahari da shi, wanda ga shi har ya kai ni matsayin da ban taɓa tunani ba, ban yi mafarkin zan kai ba.
FIM: A’isha Adam Hussaini, ke ya aka yi ki ka zama marubuciya?
A’ISHA ADAM HUSSAIN: Ni ma dai na kasance ina ‘yan karance-karance tun daga irin su ‘Magana Jari’ da irin su ‘Ruwan Bagaja’. Gaskiya daga kan waɗannan, su ‘Baba Da Inna’, na fara sha’awar ni ma me zai hana in ɗan fara gwada nawa rubutun. To, akwai lokacin da na karanta wani littafi ‘Fitsarin Faƙo’, da kuma ‘Sanadin Boko’, lokacin ina ‘secondary school’, littafin ‘Sanadin Boko’ ya ɗan taɓa ni sosai! Halima K/Mashi ce ita ta rubuta ‘Sanadin Boko’. To labarin ya taɓa zuciya ta sosai, a lokacin sai na ke ganin ni ma bari in yi ƙoƙari in ɗan gwada wani abin da zai faɗakar. Sai na fara rubutu a lokacin. Na kan ɗan rubuta a 40-leaves in samu littafi ina ɗan rubutawa a lokacin. Ta haka dai na fara, gaskiya.
FIM: Ke kuma yaya aka yi ki ka zama marubuciya? Me ya ba ki sha’awar ki yi rubutu, wanda har yau ga shi Allah ya kai ki wani mataki na zama ɗaya daga cikin gwarazan marubuta na Arewa?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: E to, gaskiya ina son yin rubutu ba tare da na ma iya rubutun ba. Yaya ta ce ta ke karanta littafi a gida haka, sai ta na ba mu labari, to tun daga lokacin sai kawai na ji ni so na ke na riƙa rubutawa da kai na, ba wai a riƙa ba ni labarin wasu ba. Sai ya kasance na shiga sakandare daga JS1, sai ni da wata ƙawa ta mu na ƙin kashe kuɗin ‘break’ ɗin mu, mu sayo littafi a kan za mu yi rubutu. Ina ga mun sayi littattafan nan ba adadi, amma ba mu iya ‘sentence’ ɗaya ma da Hausa, saboda ba mu san ya za mu fara ba, ba mu iya Hausar ba, kuma ba mu san yadda ake yin rubutu ba.

Sai da mu ka je SS1 wani malamin mu ya sa mu a Hausa, da ya ke a firamare ba a yi mana Hausa, amma da mu ka je sakandare ana yi. To a nan ne na ɗan fara iya Hausa, sai ya samu ya ce dole sai mun rubuta labari, shi ne ‘test’ ɗin mu, don da farko ma mun ƙi yi, mun ɗauki abin shirme; ta ya za a yi a ce mu ƙirƙiri labari? Ta ina za mu fara? To da ya dage ya ce wannan shi ne C.A. (continuous assessment) ɗin mu, duk wanda bai yi ba kuma ya rasa. To a lokacin kowa ya na ji ba ka so ka ga kai ne a baya, mu ka dage mu ka rubuta littafi. Ina ga shi ne littafi na na farko, ‘So Sarki Ne’.
Daga nan kuma sai na zo na ga an fara rubutun onlayin ɗin nan. Ina bi ina ɗan karanta wasu littattafan, sai na fara a guruf ɗin Facebook, ina gabatar da wani wasan kwaikwayo. To, akwai wata ƙawa ta ita kuma da ta ke rubutu, sai ta ce min ai rubutu ma haka ne kamar yadda na ke rubuta wasan kwaikwayon nan. Sai na ce mata a’a ba zan iya ba. Duk da cewa na taɓa rubuta wancan (a sakandare), amma ban ɗauke shi a matsayin wani abu ba. Ta ce min in gwada. Tun da dai na fara gwadawa shi ne har yanzu.
FIM: Kin faɗi littafin ki na farko. Ya ki ka yi da littafin – an buga shi ne a matsayin littafi ko kuma a onlayin ki ka wallafa shi?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Gaskiya littafin shi ko onlayin bai je ba. Ba na ma sa shi a jerin littafai na na onlayin, saboda shi ban rubuta shi ba, a ‘school’ ɗin an karɓa, malamin mu ya ce za a buga. To ban san me ya faru ba, amma dai ba a buga shi ba, kuma littafin ya na wurin shi.
FIM: Ba ki da kwafe?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Ban da shi, gaskiya.
FIM: Littafi ne kamar na haɗin gwiwa?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: A’a, kowa shi ya yi nashi. Lokacin ’20-leaves’ kowa ya saya, za ka rubuta labari ‘complete’ a kai.
FIM: To, wannan mu ɗauka kawai ya tafi. Wanne ne kuma ya zama littafin ki wanda ki ka wallafa shi ko da onlayin ɗin ne?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Littattafai na kusan goma sha bakwai.
FIM: Na farkon na ke magana.
A’ISHA SANI ABDULLAHI Na farko ‘Babu Ruwan So’.
FIM: Shi an buga shi a onlayin?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: E, akwai shi a onlayin.
FIM: Waɗannan littatafan kusan goma sha bakwai duk an buga su?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Su na nan onlayin. Guda ɗaya ma an yi ‘publishing’ ɗin sa.
FIM: A matsayin littafi?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: E. ‘Sai Na Auri Marubuci’, akwai shi a kasuwa a Kano.
FIM: A’isha Adam Hussaini, ke wanne ne littafin ki na farko da ki ka rubuta kuma aka buga shi? Sannan ki na da wani littafi wanda ba a onlayin aka buga shi ba, an buga shi ne a kan takarda?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: E to, ban buga littafi ba har kawo yanzu, sai dai na sake su a onlayin ne kawai. Babu bugaggen littafi. Kuma littafin da na fara rubutawa onlayin shi ne ‘Yawon Sallar Hajiya Iya’. Labari ne a kan wata dattijuwa haka mai ɗan rikici, to kuma ya na nuna yadda ‘ya’ya ya kamata su yi haƙuri da iyayen su, don sun girma sun kai wasu shekaru na girma, sakamakon in iyaye su ka yi irin wannan girman dole sai an yi haƙuri da su. To a kan haka na yi rubutun, amma gaskiya ban taɓa bugawa ba.

FIM: Littattafan ki da ki ka rubuta yanzu sun kai guda nawa?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: E to, za su kai goma sha biyu haka.
FIM: Waɗanda aka wallafa su a onlayin sun kai guda nawa?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Za su yi goma sha biyu su ɗin ma.
FIM: A’isha Abdullahi Yabo, ki faɗa mana littafin da ki ka fara rubutawa ke ma da kuma yawan littattafan da ki ka rubuta zuwa yanzu.
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Na fara rubuta littafi na mai suna ‘Amal’. Sannan na rubuta littattafai goma.
FIM: Dukkan su su na nan onlayin ko kuma waɗansu ba ki ɗora su ba?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Dukkan su su na nan onlayin. Sai kuma na rasa wasu, amma ina da wasu.

FIM: Daga bayanin da mu ka yi, dukkan ku dai marubutan onlayin ne, amma A’isha Sani Abdullahi ta buga littafi ƙwaya ɗaya, ya na kasuwa. Shin ku na da burin ku rubuta littattafai na takarda, ko kuwa dai kun gamsu ku zama marubutan onlayin ya ishe ku?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Ina da burin in buga nawa littafin, amma ba wai don ban gamsu cewa wai ni marubuciyar onlayin ba ce. Har ko yaushe ina alfahari da kasancewa ta marubuciyar onlayin saboda cigaba ne shi ma na rayuwar zamani da mu ke ciki. Sai dai kuma zan yi fatan a ce na kafa tarihin da na buga nawa littafin a takarda.
FIM: Zuwa yaushe?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Kowane lokaci na samu damar yin haka.
FIM: Hajiya A’isha Adam Hussaini, ki na da burin ke ma ki buga littafi, wata rana a ce ga littafin ya fito da aka buga ko kuwa kin gamsu ki tsaya a onlayin kawai shi kenan?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Sosai, ina da buri gaskiya, don littafin da na kammala nan ba da jimawa ba na kammala shi, ‘Shu’umin Masarauta’, saboda yanayin rubutun onlayin, mu na yin shi ne ‘page by page’, ka ga in bugawa ne dole sai ka haɗe shi a ‘document’ wuri ɗaya. Na zauna na haɗe duk waɗannan abubuwan, don ina da burin buga shi in-sha Allahu. Na yi magana da wanda zai buga min.
FIM: Kin magana da kamfanin da za su buga maki?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: A’a, akwai wanda ‘yan onlayin ke ba aikin, in ka na da sha’awa za ka yi masa magana, sai ka ba shi aikin da duk abin da dai ya kamata. To, in-sha Allahu ina da burin buga ‘Shu’umin Masarauta’, gaskiya.
FIM: A’isha Sani Abdullahi, ke yanzu har kin buga littafi guda ɗaya. Shin ki na da burin ci gaba da buga littattafai? Sannan wanda aka buga ɗin kin ci wata riba daga buga shi fa aka yi, misali, kin samu kuɗi?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: E to, gaskiya ina da burin buga dukkan littattafai na ko wanne. Duk da cewa ina da su onlayin, zan so a ce na gan su a buge. Duk da dai onlayin ɗin ne mafari, amma kasancewar su a buge wani tarihi ne da zan iya adanawa a kowane lokaci da na ke buƙatar shi zan yi amfani da shi.
Sannan kuma littafi na da ya ke kasuwa, gaskiya an samu (kuɗi), alhamdu lillah. Tunda ko ba komai ma akwai waɗanda in su ka je za su tambaye ni wane littafi ne nawa na ke da shi a kasuwa? Akwai irin manyan marubutan da ba su cika son karatu a waya ba, in ku ka yi magana, su kan ce ka na da wani littafi bugagge? In ka faɗa, za su nema su karanta.
FIM: Wace riba ake samu a rubutun onlayin? Ana samu wani kuɗi ne?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Ana samu gaskiya. Saboda yanzu an fitar da hanyar da za ka sa kuɗi a littafin in ka na so ka yi shi na saidawa. Kuma akwai ‘application’ da aka yi na marubuta ma yanzu, wanda za su iya sawa na littafan Hausa. Na littattafan Hausa ne gaba ɗaya, za ka iya sawa ka saida littafin ka, in kuma ‘direct’ a WhatsApp ka ke so ka saida, za ka iya fara ‘free pages’ na littafi ka, ka saka kuɗi, in ‘free pages’ ɗin ya ƙare duk mai so zai biyo ka ya biya ka kuɗi, ka sa shi a guruf, in kuma ka kammala zai ɗauki ‘document’ ɗin ya karanta.

FIM: Malama A’isha Abdullahi Yabo, ina so in tambaye ki, ku marubutan onlayin akwai waɗanda ke sukar ku, suka kala-kala. Akwai masu cewa ba ku bi ƙa’idar rubutu, mutum zai yi rubutu yadda ya ga dama, Hausar ba nahawu, ba kaza ba kaza, sannan akwai masu rubutun batsa kawai, su na aikawa ko da da sunan ƙarya, da sauran su, har wasu na cewa a hana ma rubutun onlayin. Me za ki ce a kan wannan?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: To, abin da zan iya cewa, saboda baragurbin cikin mu bai kamata a soki gaba ɗaya marubutan onlayin a ce a ɗauke mu ba marubuta ba ko kuma a riƙa sukar mu. Saboda kowane irin al’amari na rayuwa akwai abu mai kyau, akwai mara kyau cikin shi. Tabbas, akwai marubutan batsa, amma ba su kai yawan marubutan da su ke ƙoƙarin ganin alƙalamin su ya saitu a kan hanya tagari, ta kirki ba.
Sannan batun marubutan onlayin ba su bin nahawu, sai in ga ba na wannan lokacin ba. Don yanzu gaskiya abubuwan an samu cigaba sosai. Da yawa marubutan onlayin su na ƙoƙari su ga cewa sun tsaya sun karantu, saboda akwai marubuta da yawa da yanzu su ka buɗe ajujuwa na onlayin da su ke koyar da mu darussa a kan ƙa’idojin rubutu, wanda ina da tabbaci a yanzu idan za a haɗa marubutan da ke buga littattafan su na baya da mu marubutan da mu ke na onlayin yanzu, mafi yawa idan za a haɗa, a ce kowa ya kawo abin rubutun shi na ƙa’idojin rubutu, su ma su kawo, to in-sha Allahu marubutan onlayin za su cinye. Saboda yanzu marubutan onlayin su na ƙoƙarin ganin sun kare ƙa’idojin rubutu da nahawun Hausa.
FIM: A’isha Adam Hussaini, ku marubutan onlayin, ku na da wata ƙungiya ne da ku ke tafiyar da ita, misali da shugabanni da komai, kun san junan ku?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: E to, ba mu da wata ƙungiya dai guda ɗaya da za mu ce baki ɗayan marubuta onlayin mu na ƙarƙashin ta. Sai dai a marubuta onlayin ɗin ma, akwai ƙungiyoyi da a kan buɗe, don ko Malama A’isha shugabar wata ƙungiya ce ta ‘yan onlayin ɗin.
FIM: Ita A’isha Sani Abdullahi ko?
A’ISHA ADAMU: E, ita A’isha Sani Abdullahi. Akwai ƙungiyoyi da dama da za a buɗe, akwai shugabanni a ciki, sai kuma membobi, akwai dokoki da ake kafawa: ba mu son rubutun batsa, ba mu son cin zarafi, ba mu son wani abu; akwai dai dokoki da dama da aka rubuta, in ka amince da waɗannan dokoki to za ka zauna a wannan ƙungiyar, in ba ka amince ba, ba za ka zauna ba. Don kamar yadda ka yi maganar rubutun batsa ma, yawanci idan aka duba masu rubutun batsar nan, cin gashin kan su su ke yi, gaskiya, ba su rubutu a ƙarƙashin ƙungiya.
FIM: Kuma an san su?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: An san su. Kuma bai kamata ɗoyin su ma ya shafe mu ba saboda, misali, mu mu na zaune a ƙarƙashin ƙungiya, bai kamata su da su ke cin gashin kan su a ce za a yi mana kuɗin goro ba.
To akwai ƙungiyoyi daban-daban haka na marubuta, rukuni-rukuni, za ka samu kowane da ‘members’ da kuma shugabannin su, kuma in laifi ma ka yi a cikin ƙungiya, a kan hukunta haka da horo ko a kore ka, ko a ba ka hutu ko kuma dai a ce ka biya tara, gaskiya.
FIM: A’isha Sani Abdullahi, an ce ki na shugabantar wata ƙungiyar marubuta. Yaya sunan wannan ƙungiyar, kuma waɗanne irin membobi ne a cikin ta? Kuma duka a Filato su ke ko kuma akwai su a garuruwa daban-daban?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Sunan ƙungiyar ‘Noble Writers Association’.
FIM: Sunan da Turanci ne kuma ba da Hausa ba?
A’ISHA SANI ABDULLAHI (dariya): E. Dalilin da ya sa aka saka da Turanci, yanzu in zan fassara, ‘Noble’ ɗin ya ƙunshi kalmomi da yawa da Hausa. Kuma ba na son in gajarta in ɗauki kalma ɗaya, kamar in na ɗauki ‘karamci’, kalma ɗaya ce, in kuma na sa ‘Noble’ ɗin ya ƙunshi abubuwa da yawa da mu ke so ƙungiyar ta kasance da shi.
FIM: Su wanene ‘ya’yan ƙungiyar? Kuma a ina su ke?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Gaskiya ba ‘yan Jos ba ne. Ina tunanin ma ni kaɗai ce ‘yar Jos ɗin a ciki.
FIM: Ku na ganin juna ko kuma ƙungiyar onlayin ta ke, ita iyakar ta kenan?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Ba mu ganin juna, amma mu na da shirin yi mata rajista. Har ‘yan Nijar akwai, ba ma iyaka ‘yan Nijeriya ba ne kaɗai.
FIM: A’isha Abdullahi Yabo, su marubutan onlayin me ya sa mata su ka yi yawa a ciki? Me ya sa babu maza a onlayin? Ko kuma akwai, ni ne dai ban sani ba?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Gaskiya ba zan ce ba maza ba. Akwai mazan, sai dai matan sun fi yawa. Kuma ba mamaki saboda damar da wasu matan ba su samu ba ne ƙila. Da yawa akwai matan da su na da baiwar da za su yi rubutu, amma a lokacin da ake buga littattafan ba su samu wannan damar ba. Sai wannan lokacin da zamani ya zo mana da rubutun onlayin, harkar (soshiyal) midiyar nan ta shigo, sai ya zamana matan su ka samu damar da za su baje kolin baiwar da Allah ya yi masu.
Wannan dalilin ya sa na ke ganin mata marubuta onlayin sun fi maza yawa, duk da su ma mazan akwai su.
FIM: A’isha Adam Hussaini, ku marubutan onlayin yawanci ku na rubutu ne a kan soyayya da zaman aure. Sai ana cewa shin ba ku san matsalolin da su ke damun ƙasar nan ba ne, misali na tattalin arziki ma, kawai sai kullum maganar aure da soyayya? Ko kuma ke a matsayin kan ki ki na rubutu a kan wasu matsaloli waɗanda ba su shafi zamantakewar namiji da mace ba?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: E to, akwai masu rubutu a kan abin da ya shafi waɗannan ɓangarorin, sai dai kuma, kamar yadda ka faɗa, an fi karkata ta wancan ɓangaren. Ni a karan kai na ban yi wasu rubuce-rubuce da ya shafi matsalolin ƙasa ba, sai inda na fi karkata.
Na fi karkata ɓangaren abin da ya shafi aljanu haka, ban cika ma rubutun soyayya ba, gaskiya. Don ni labarin soyayya bai cika burge ni ba. Na dai fi yin rubutu ne a kan abin da ya shafi aljanu haka, da sakacin da mata kan yi har aljanu su samu damar shiga cikin jikin su, ko kuma fannin aljani da zai razana ko kuma wata kariya da addu’a da ya kamata ka riƙe. Gaskiya ni na fi rubutu a wannan fannin.
FIM: A’ishar Jos, a kan me ki ka fi yin rubutu ke?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Gaskiya na fi yin rubutu a kan abubuwan da ba a cika bayyanar da su ba ne.
FIM: Kamar me?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Kamar abubuwan da ke faruwa da rayuwar mata, har ma da mazan. Abubuwan da an fi so a danne su, amma an san cewa su na faruwa, kuma su na cutar da waɗanda ya ke faduwa a kan su, amma an fi so a danne su a da; wasu abubuwan da babu buƙatar bayyanar da su ga duniya.
FIM: Kamar me kenan?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Kamar yadda za a ce namiji ne ke tauye wa mace haƙƙin ta, ba a iya tunanin cewa akwai mace da ta ke iya danne haƙƙin mijin ta. Sannan ba a son bayyanar da cewa e, su ma mata su na shiga ƙalubale yayin da maza ke nuna rashin kulawa a gare su. Su na iya fuskantar ƙalubalen rayuwa da kuma halin da ƙasa ke ciki, abubuwan da aka sa na cin hanci da irin wani abu irin in mace ta je ta na neman wani abu ake nuna mata cewa sai ta bada wani abu kafin a ba ta, ba za ta taɓa samun abu ta daɗi ba, musamman (saboda) kasancewar ta mace, sai ya sa wannan abin ya zame mata abu mai wahala, wani lokacin har ya kai ga ta iya saɓa wa Ubangijin ta kafin ta samu biyan buƙata.
FIM: Ya aka yi ki ka san da maganar gasar Hikayata? Kuma kin taɓa shiga gasar a baya, ko kuma wannan ne na farko?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Gaskiya na san ta a Facebook, saboda marubuta ana sakewa, irin ana ‘sharing’ a cikin guruf ɗin. Sannan wannan ne shiga ta ta uku.
FIM: Da wace shekara da wace shekara ki ka shiga?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Na shiga 2021, 2022, sai wannan 2023.
FIM: Sai ga shi an zaɓe ki ki na cikin waɗanda su ka zo ƙarshe.
A’ISHA SANI ABDULLAHI: E.
FIM: Me za ki ce a kan wannan mataki da Allah ya kawo ki na zama cikin mutum uku na ƙarshe?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Gaskiya na yi farin ciki, kuma na gode wa Allah, domin nasarar ba tawa ba ce, daga Shi ne.
FIM: Ki na da wani buri a kan gasar?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Tunda na zo wannan matakin, ni a tunani na, na gama yin nasara! Ko na ɗaya, ko na biyu, na gode wa Allah kawai. Zuwa wannan gasar in ka samu zuwa wannan mataki sai dai ka gode wa Allah kawai.
FIM: A’isha Adam Hussaini, ya aka yi ki ka san da gasar Hikayata?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: E to, in aka zo nan ɓangaren ma, ka ga cigaban onlayin kenan, tunda a onlayin aka saki wannan gasar, a onlayin ne za ka yi rubutun kuma ka tura, su ma kuma har su duba su dawo da amsar cewa ka yi nasara, tunda ba wai cewa ake ku je wani wuri an kafe ku duba sunayen ku ba. A onlayin su ka saki, mu ka bibiya, mu ka shiga guruf na marubuta haka, da Facebook da kuma na WhatsApp, a nan mu ka ga ƙa’idojin mu ka karanta, sannan kuma mu ka lalubi jigogin da ya kamata mu yi rubutu a kai don ya kawo cigaba da wani gyara a cikin al’ummar mu.
FIM: Sau nawa ki ka shiga gasar kafin Allah ya kawo lokacin da aka zaɓe ki ki ka kawo wannan matakin?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Na shiga sau uku, gaskiya. Na fara daga 2021, aka zo 2022, sai kuma 2023 ɗin nan Allah ya kawo mu na yi nasara.
FIM: Mecece fatar ki game da wannan gasa da ki ka shiga?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Alhamdu lillah. Fata kam na kasance cikin ukun da za su yi nasara, to kuma ga shi ka zo matakin, sai dai ka ce ka na godiya ga Ubangiji da ya yi maka wannan baiwar, tunda ba wayon ka ko dabarar ka ba ne ya ba ka; a ce labarai daga cikin mutane ɗari biyar an zaɓe ku ku uku, ka san wannan ba yin ka ba ne, ba kuma wayon ka ba ne, Allah ne ya ba ka, sai kuma ƙoƙarin da ka yi kai ma na rubutun da ya kamata.
FIM: Ba ki da wata fata ta zama ta ɗaya ko ta biyu ko ta uku?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Duk wanda ka samu nasara ce, saboda ɗaruruwan ka su na nema ba su samu ba, kai kuma ka samu. Ko a wane mataki ka zo, ko na ɗayan ko na biyun, alhamdu lillah.
FIM: Ke ma babu damuwa duk inda aka jefa ki gobe?
A’ISHA ADAM HUSSAINI (dariya): In-sha Allahu!

FIM: A’isha Abdullahi Yabo, ya aka yi ki ka san da gasar Hikayata ke ma?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Gaskiya da ma mafi akasarin gasa, ko ma wace iri ce, a kan cillo ta cikin guruf-guruf da marubuta su ke ciki. Wannan ɗin ma na san ta ne ta hanyar guruf na marubuta. Lokacin da na fara shiga 2019 ne, kuma duk shekara na kan shiga, kuma ban taɓa karya mataki ba, in shekara ta zo sai in ji kai ba zan shiga ba saboda na shiga waccan ban ci ba, sai marubuta ‘yan’uwa su ke ƙara ƙarfafa min gwiwa, su ce in yi haƙuri.
FIM: Ki na canza labari duk shekara idan za ki shiga?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Duk shekara ina canza labari.
FIM: Ya ki ka ji a bana kawai da ki ka ji sunan ki a cikin waɗanda aka zaɓe su su ka kai wannan mataki?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Gaskiya farin ciki na ba zai misaltu ba. Sannan kuma na san wannan abu ba wai iyawa ta ba ne, kawai nufi ne na Ubangiji. Allah shi ne ya ba ni nasara. Ban taɓa zato ko tsammani ba, a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba. Lokacin kawai sai na gode wa Allah, na san cewa babu wanda ya yi min, Shi ne ya yi min.
FIM: Ya sunan labarin da ki ka shiga da shi a wannan shekarar?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: ‘Baƙin Kishi’.
FIM: A kan menene?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Labari ne a kan kishi, yadda mata su ke ɗaukar zafin kishi. Sannan kamar yanzu abubuwan da su ke yawan faruwa, za ka in ka hau midiya ko a labarai za ka ji an ce wacce ta kashe mijin ta, wacce ta caka wa mijin ta wuƙa. In ka bibiyi labarin za ka ga cewa ba fa auren dole aka yi ba, aure ne da aka gina shi da soyayya, in ka bibiyi ƙarshen labarin za ka ga ba komai ba ne ya janyo haka, zafin kishi ne ya janyo mace ta kashe mijin ta. A kan wannan ne na gina labari na.
FIM: Mecece fatar ki a kan wannan gasa?
A’ISHA ABDULLAHI YABO (dariya): Ai fata ya riƙa ya ƙare. Allah ya riga ya gama nashi hukuncin Tunda Allah ya fito da ni cikin ukun, alhamdu lillahi, na riga na gama nasara, sai dai godiyar Ubangiji.
FIM: A’isha Adam Hussaini, ya sunan labarin da ki ka shiga wannan gasar da shi? Kuma a taƙaice a kan me ki ka yi labarin?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Sunan labari na ‘Rina A Kaba’. Labari ne da ya ke bayyana illolin shaye-shaye da cushe-cushen magungunan mata, musamman a wannan lokacin da mata ke cin karen su babu babbaka. In ka buɗe WhatsApp, Facebook, ina ne, duk dai soshiyal midiya in ka buɗe za ka ga talla ta magungunan mata; (haka a) gidan biki ko suna, wani zubin har gidan mutuwa mata kan tafi da ‘yan kayan su su riƙa tallar waɗannan abubuwan. Kuma mata idon su na rufewa, su yi ta sayen waɗannan abubuwan babu tunanin abin na zai cutar da lafiyar su. A kan haka na gina labarin ‘Rina A Kaba’. Kamar yadda ya faru da jarumar, ita ta kasance mai wannan ɗabi’ar, ba ruwan ta, kawai ita burin ta ta yi amfani da wannan, zai zame mata maslaha ko ba zai zame mata ba, ba ruwan ta, idon ta ya rufe. Burin ta ta yi amfani da wannan abin. Daga ƙarshe har ya cutar da ita da mijin, cutar ya fi cutar da ita daga ƙarshe.

FIM: A’isha Sani Abdullahi, ya sunan labarin ki da ki ka shiga wannan gasar da shi? Kuma menene jigon labarin?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Labari na sunan shi ‘Tuwon Ƙasa’. Kuma jigon sa yi shi ne a kan uƙubar da wasu matan ke fuskanta sanadiyyar rashin kulawar miji.
FIM: Kamar yaya?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Rashin samun kulawar miji, miji ba zai ɗauki nauyin su ba, ba zai damu da rayuwar su ba, ba za su inganta rayuwar su da ta ‘ya’yan su ba. Ita jarumar, mijin ta ya zuba maƙudan kuɗaɗen shi ne a manhajar yanar gizo, irin mazan nan marasa ɗaukar shawara. A tunanin shi zai samu ninkin su, a ƙarshe masu manhajar su ka gudu, ita kuma ya yi watsi da rayuwar ta da ta ‘ya’yan ta, bai damu da sun ci, sun sha ba, ita kuma yaran ta sun fara tasowar da ya kamata a ce sun yi karatu, hakan ya sa ta fara faɗi-tashin nema masu mafita, inda ta ke shiga halin gaba kura, baya siyaki. Duk da kasancewar ta matar aure, ta bada kan ta. Ita tunanin ta cewa wahalar ta ya zo ƙarshe, daga baya kuma ta zo ta yi biyu babu. Ba ta san cewa tuwon da ta tuƙa na ƙasa ba ne, kuma tuwon ƙasa ba ya maganin yunwa, tunda ta zo ta rasa aiki, kuma ta saɓa wa Ubangijin ta.
FIM: Menene burin ki a rayuwa?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: In zama mai bada shawarwari musamman ga mata.
FIM: A kan me?
A’ISHA SANI ABDULLAHI: Fannin rayuwar su, musamman a aure. Tunda yanzu mata abin da ya fi damun su a rayuwa, ya ke je fa su a halaka, shi ne rayuwar aure, abin da za su fuskanta a gidan su da mazajen su.
FIM: Kuma kin faɗi ki na so ki shiga makaranta.
A’ISHA SANI ABDULLAHI: E. Kuma ina so in karanci ɓangaren bada shawarwari.

FIM: A’isha Adam Hussain, menene burin ki a rayuwa a matsayin ki na marubuciya?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Buri na a rayuwa in zama marubuciyar da zan yi rubutun da zai faɗakar da al’umma, kuma ya ci gaba da faɗakar da su, in yi rubutun da zai amfani al’umma, ya kawo gyara ko sauyi a rayuwar mu gaba ɗaya.
FIM: Ki na da burin ki ƙara karatu ko kuwa kin gamsu da matakin karatun da ki ke?
A’ISHA ADAM HUSSAINI: Yanzun ma dai karatun na ke yi. Ina da burin in kammala shi cikin kwanciyar hankali lafiya ƙalau.
FIM: A’isha Abdullahi Yabo, menene burin ki yanzu a rayuwa?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Buri na game da rubutu, ina fatan ya kai inda ban ma yi tunanin zai kai ba, kuma saƙo ya riƙa isa ga al’umma, ya yi amfani ga al’umma.
FIM: Karatu fa? Wanda ki ka yi ya isa?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: In zan samu dama ina so, ai shi ilmi ya na da daɗi.
FIM: Ɗazu a bayanin ki, kin faɗa mani cewa kin yi makarantar addini ne. Ko ki na da burin ki yi ɓangaren boko? Ko kuma ɓangaren addinin ki ke so ki ƙara a kai?
A’ISHA ABDULLAHI YABO: Dukkan su ina da buri a kai. Ina da burin ilmi na ya ƙaru a fannin addini, kuma idan zan samu dama fannin boko ina so, saboda ilimi ko da yaushe abin so ne.
FIM: To, ina yi maku fatan alheri baki ɗayan ku. Allah ya ba ku nasara. Na gode ƙwarai.
A’ISHOSHI: Mu ma mun gode.
