SANANNEN marubuci, furodusa kuma jarumi a Kannywood, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), zai aurar da ‘yar sa Fatima a ranar Asabar mai zuwa, wato 2 ga Satumba, 2023.
Za a ɗaura auren Fatima Ado Ahmad Gidan Dabino da masoyin ta, Bello Umar Kawaji, da misalin ƙarfe 11:00 na safe a masallacin Juma’a na Alfurƙan da ke Titin Alu Avenue, Nassarawa GRA, Kano.

Gidan Dabino ya raba da kan sa ya raba katin auren a guruf-guruf na soshiyal midiya tare da faɗin, “Wannan kati ana sanar da ku ne don ku yi wa ango da amarya addu’ar samun zaman lafiya.
“Waɗanda su ke wajen Kano an ɗauke musu ba sai sun zo ba, saboda yanayin rayuwar da ake ciki. Allah ya sa mu dace. Mun gode da addu’ar ku.”
Allah ya kai mu da rai da lafiya.
