ZA a iya cewa duniyar rubutun Hausa ta koma soshiyal midiya, wanda hakan ya samar da wasu marubuta da su ka yi fice a fagen rubutu waɗanda ake kira ‘yan onlayin. Tashen su ya kwatankwacin na marubutan littattafai kan takarda su ka yi sharafin su a baya. Akwai matasa da dama da ba su taɓa karanta littafin hikaya ba sai na waɗannan ‘yan onlayin ɗin.
Halima Salahu Adamu ko Sadiya S. Adam, wadda aka fi sani da SaNaaz Deeyah, ta na ɗaya daga cikin fitattun marubutan onlayin. Ta yi littattafai da dama waɗanda su ka cafki zuciyar masu karatu a yanar gizo. Sun haɗa da ‘Direban Gidan Mu’, ‘Rashin Halacci’, ‘Sanadin Mahaifi Na’, ‘Mubina’, ‘Zafin Hawaye Na’, ‘Son Zuciya’, ‘Jarrabar Rayuwa’, ‘A Cikin Ido…’, ‘Kin Min Illa’, ‘A Dalilin So’, ‘Menene Aibu Na?’ da kuma ‘So Da So’.
Ganin yadda harkar rubutun onlayin ta ke ƙara samun karɓuwa a wajen masu karatu ya sa mujallar Fim ta tattauna da Halima SaNaz-deeyah don jin yadda ta samu kan ta a ciki da irin ribar da su ke samu, kamar haka:
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatu.
HALIMA SALAHU ADAMU: To ni dai Halima Salahu Adamu shi ne suna na, amma an fi sani na da SaNaz-deeyah musamman a kafar sadarwa. Kuma ni haifaffiyar Jihar Jigawa ce, a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Kazaure. Na yi ‘primary school’ a Al-Iman, na kuma yi ‘secondary school’ a FGGC Kazaure. Daga nan kuma na wuce State Polytechnic, Dutse, na yi National Diploma a fannin kasuwanci, wato Business Administration. Ban tsaya a nan ba, na kuma wuce na yi Higher Nation Diploma (HND) a Hassan Usman Polytechnic da ke garin Katsina. A yanzu haka na kammala ina shirin fara bautar ƙasa (NYSC).
FIM: Me sunan SaNaz-deeyah ya ke nufi, kuma me ya sa ku marubutan onlayin ku ke ɓoye sunan ku?
HALIMA: To shi wannan suna ‘nickname’ ɗi na ne tun kafin na fara rubutu. Kuma al’adar marubutan onlayin ce haka, ɓoye sunan su, amma a yanzu za ka ga wasu su na bayyana sunan su. Ni kai na don na fara da ‘nickname’ ne kuma ta haka ne kawai in na yi rubutu za a gane ni ce, amma ina so na canza na mayar da asalin suna na, sai dai sunan zai zama baƙo a wajen makaranta.

FIM: Tun a wanne lokaci ki ka fara rubutu kuma ya aka yi ki ka samu kan ki a matsayin marubuciyar onlayin?
HALIMA: Ba ni ke da burin rubutu ba a farko, ‘yar’uwa ta na ga ta na yi a littafan ta; ta kan ƙirƙiri labari ta kuma rubuta. Abin ya na bani sha’awa har na fara kwaikwayon ta. To kuma cikin ikon Allah ina gama ‘secondary school’ sai rubutu ya ɓullo a kafar sadarwa ta Facebook, ina ɗan bi in karanta. Lokacin kuma da ya fara yaɗuwa a WhatsApp sai na yi sha’awar farawa kasancewar ni na fi ƙarfi a WhatsApp. Daga nan kawai sai na fara. Sai dai a farko na sha wahala kafin na samu labari na ya kai gaci, domin rubutun kawai na iya, ban iya ƙa’idojin rubutu ba, sai daga baya da na zama mai naci har Allah ya sa na iya. Kuma ta ƙarƙashi na marubuta da dama su ma su ka iya. Sai dai na ce alhamdu lillah.
FIM: Ko kin taɓa buga littafin ki kin fitar da shi a kasuwa?
HALIMA: E to, gaskiya ban taɓa buga littafi ba, sai dai niyya, domin ko a cikin shekarar nan na so na buga ɗaya daga cikin littattafai na ya zama ‘published’, don har na yi magana da mai bugawar, to kasancewar mu rubutu ne a onlayin akwai wasu abubuwa da dole sai mun cire, misali sunan mu da ke kowane shafi, sunan ƙungiya da kuma lambar shafi da kuma irin ɗan bayanai da ake yi. Waɗannan abubuwan da ya ce na cire su ne su ka jawo tsaiko, kasancewa ta mace da ta ke da ƙarancin lokaci a waɗannan watanni da su ka shuɗe. Amma in-sha Allah da komai ya daidaita a wannan shekarar za a iya ganin littafi na a kasuwa.
FIM: Ta ina ake samun kuɗi a rubutun onlayin?
HALIMA: Ina samun kuɗi a Youtube; Youtubers su na sayen littattafai na sosai. Ni ma ina da Youtube channel tawa ta kai na, sannan kuma ina sayar da ‘novels’ ɗi na a WhatsApp. Sai dai na ce alhamdu lillah, gaskiya ina samun kuɗi a onlayin, ba laifi.
FIM: To yaushe ki ka fara rubutun da ki ka zama marubuciya onlayin?
HALIMA: Kamar dai yadda na faɗa, gaskiya na fara ne a ban san kowa ba, sai dai a wancan lokacin, wato farkon fara rubutu a onlayin, marubuta su na saka lambar wayar su a cikin littattafan su, to sai na ɗauki lambar wata Beebah luv – Allah ya jiƙan ta da rahama – na yi mata magana mu ka fara littafi tare da ita, wanda shi ne littafi na na farko. To daga baya kuma sai Allah ya haɗa ni da wata Munyshat, ita ta fara tura mini ƙa’idojin rubutu na duba na kuma zauna na yi nazari a kai, har dai na ƙware. A haka har na shiga ‘groups’ na marubuta, kasancewar a wancan lokacin babu ƙungiya.
FIM: Yaya alakar ku ta ke tsakanin marubutan littafi da na onlayin?
HALIMA: To kyakkyawar alaƙa ce, domin kamar ma mun zama ahali ɗaya ne, kuma dukkan mu mu na amsa sunan marubuta. Kasancewar sun fi mu gogewa a harkar, mu na ba su girman su kuma su kan saurare mu idan mu ka kawo masu kukan mu. A yanzu gaskiya mun samu fahimtar juna tsakanin mu da su.
FIM: A wanne lokacin ki ka fi jin daɗin yin rubutun ki?
HALIMA: Na fi jin daɗin rubutu da daddare idan kowa ya yi bacci, sai kuma da sassafe kafin rana ta fito. A waɗannan lokutan na fi samun natsuwar yin rubutu.

FIM: Waɗanne irin nasarori ki ka samu a cikin harkar rubutun onlayin?
HALIMA: To, na samu nasarori da dama. Na haɗu da mutanen da ban taɓa tunanin zan haɗu da su ba a sanadiyyar rubutu, sannan suna na ya je inda ban taɓa tunanin zai je ba, na riƙe muƙaman da ban yi tunanin zan kai matsayin ba. Sai dai na ce alhamdu lillah domin rubutun onlayin ya yi mini rana, sai dai fatan ƙara samun wasu nasarori a gaba.
FIM: Ana yi maku kallon masu rubutun batsa da ɓata tarbiyya ku marubutan onlayin. Me za ki ce?
HALIMA: To maganar kalaman batsa gaskiya sabbin marubutan da aka samu a yanzu su ne su ke son lalata harkar, domin wasun su za ka ga an yi hira da su kai-tsaye su ke faɗin su na saka batsa ne a littattafan su domin su yi suna. Ka ga waɗannan ai ba za a kira su da marubuta ba, sai dai mu ce musu ɓata-garin marubuta. Kuma su ne za ka samu mafi yawa daga littattafan su babu ƙa’idojin rubutu domin yin sa su ke kara-zube don su gurɓata tarbiyyar wasu su kuma ɓata wa marubuta suna. Sai dai muce Allah ya yi mana maganin su. Akwai kuma marubutan da suna su ka fito nema, shi ya sa ba sa tsayawa su fahimci komai. Amma dai cikakken marubuci wanda ya shirya da gaske rubutun zai yi za ka same su su na ƙoƙarin koya kuma su na shiga ƙungiya ta marubuta.
FIM: Waɗanne irin matsaloli ku ke fuskanta a harkar rubutun ku na onlayin?
HALIMA: To gaskiya a yanzu mu na fuskantar matsala daga gurɓatattun marubuta wanda har yanzu mu na cikin tunanin ta ina za mu magance matsalar, domin shi rubutu baiwa ce, ba wai don kin ga wance ta na rubutu ko ka ga wane ya na rubutu ka ce kai ma dole za ka yi ba. Idan har ba ka da wannan baiwa ɗin, to ka haƙura ka samu wani abu wanda ka ke da baiwa a wannan fanni. To yanzu za ka haɗu da littattafai guda ɗari amma a ciki bai fi guda ashirin za ka samu da jigo da kuma salo mai kyau ba. To mu na son ƙara wayar wa da sabbin marubutan mu kai, da kuma fitar da waɗanda ba su cancanta ba.

FIM: Menene saƙon ki na ƙarshe?
HALIMA: Saƙo na na ƙarshe shi ne idan za ki fara rubutu ki tsaya ki natsu ki kuma yi tunanin littafin da za ki rubuta zai iya kaiwa inda ba ki yi zato ba, don haka mu riƙa rubuta alkhairi a littattafan mu. Mu kuma rage ƙarya, mu rubuta abin da mu ka san zai iya faruwa. Domin ni na ɗauki rubutu ne a matsayin hanyar isar da saƙo ga al’umma; marubuci zai iya gyara ko ya ɓata. Don haka mu riƙa samun jigo mai kyau, mu kuma fid da salo mai kyau, sannan mu daina rubutu kara-zube, ƙa’idojin rubutu su na da matuƙar muhimmanci da kuma tasiri a duniyar rubutu.
FIM: To madalla, mun gode.
HALIMA: Ni ma na gode sosai.