GWAMNATIN Tarayya ta ƙaddamar da wani shiri na horas da matasan Nijeriya guda 50 kan yadda za su iya samar da ayyukan ƙirƙira da yadda za su yi kasuwancin su har su samu kuɗi da su.
Masu ƙirƙirar sun haɗa da masu yin guntayen bidiyo da ‘yan TikTok, masu wasannin barkwanci, masu yin katun, furodusoshi, masu tsara fim, jarumai da marubuta fim.
An buɗe horaswar ne a otal ɗin Suru-Express da ke Ikeja, Legas, a yau Talata.
A jawabin sa na buɗe taron, Babban Daraktan Hukumar Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa, Alhaji Adedayo Thomas, ya yaba wa matasan saboda kuzarin su da yadda su ke neman na kan su duk da matsin tattalin arziki da ake ciki.
Ya ce wasu daga cikin su sun samu madafa a fagen ƙirƙirar abubuwan sakawa a kafafen yaɗa labarai na zamani, su na ƙara ƙaimi ta hanyar ƙirƙira da kuma amfani da kayan fasaha.
Ya ƙara da cewa ganin hakan ne ya sa aka ware waɗannan kwanaki domin a horas da matasa 50 masu basira kuma ‘yan kasuwa da aka zaɓo a ƙarƙashin jigon “Fahimtar Hanyoyin Tura Wasannin Bidiyo Bisa Buƙatar Mai Kallo Da Rabe-raben Su.”

Shugaban ya bayyana cewa an fito da shirin ne saboda buƙatar da ke akwai ta jawo hankalin matasa da su shigo harkar domin su taimaka wajen samar da aikin yi mai yawa, su agaza wa tsarin tattalin arziki kuma su samar da hanya.
Thomas ya yi la’akari da cewa za su yi gogayya da manya kuma sanannun gwanayen harkokin nishaɗantarwa da manyan masu harkar a duniya.
Ya ce: “Kun samu babbar dama wadda za ku inganta ƙwarewar ku, kuma ku samu malaman da za su karantar da ku, kuma su samu damar yin haɗin gwiwa.”
Thomas ya yi kira ga matasan da su yi aiki tare da bin doka, ya ƙara da cewa hukumar ta na sane da cewa ba ta takura wa kowa ba wajen aikin ƙirƙira.
Ya ce: “Kuma dole ne mu kasance a kan gaba wajen kare kyawawan al’adun mu.”
Jagorar shirya taron ita ce jaruma kuma furodusa a Nollywood, Kemi Adekomi. Sauran masu gudanar da taron sun haɗa da furodusa Zik Zulu Okafor, darakta Yemi Amodu, marubuci kuma babban malami a Jami’ar Legas, Farfesa Tunji Azeez, Dakta Rasheedah Liman ta Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya; jarumi kuma furodusa Keppy Ekpenyong, jaruma kuma tsohuwar shugabar Ƙungiyar Jarumai ta Nijeriya (AGN), reshen Jihar Legas, Moji Oyetayo, da sauran su.