SHAHARARREN mawaƙin nan na Kannywood, Mudassir Ƙasim, ya bayyana cewa akwai wasu waƙoƙi da ya rera waɗanda ya ke nadamar yin su.
A ranar Lahadi da ta gabata Mudassir ya yi rubutu a Instagram inda ya ce, “Duk masoyin waƙoƙi na ya shirya. Ina nan ina tattara jimlar wasu da na yi nadamar yin su. Kuma da sannu zan lissafo muku su da dalilin hakan.”
Wannan ƙudirin nasa ya ja hankalin jama’a, aka shiga sauraron ganin sunayen waƙoƙin da ya ke nufi.
Da mujallar Fim ta nemi jin ta bakin sa kan iƙirarin nasa, sai mawaƙin ya ce, “To gaskiya ban yi niyyar bayyana su ba ga ɗan jarida, kuma a yanzu haka ma ina kan binciken su ma, ban kammala haɗa su ba.
“Don haka a yanzu babu maganar da zan faɗa a game da waƙoƙin, sai dai idan na kammala haɗa su na ɗora a Facebook don wani ƙarin bayani sai in yi. Amma dai a yanzu ina kan binciken su ne.
“Don a yanzu wasu ma na manta da su, shi ya sa a yanzu na mayar da hankali don binciken su.”
![]()







