• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jama’a kan ajiye abubuwa masu fashewa don haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba

by WAKILIN MU
January 30, 2025
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jama’a kan ajiye abubuwa masu fashewa don haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba

Minista Mohammed Idris (a tsakiya) tare da Gwamna Mohammed Umaru Bago (a dama) da sauran jama'a a lokacin ziyarar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya gargaɗi mutane kan ajiye abubuwa masu fashewa a gidajen su don haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa irin wannan ɗabi’a tana haifar da babbar barazana ga rayuka da dukiyoyi.

Ministan ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Laraba yayin da ya kai ziyarar jaje ga al’ummar Sabon Pegi a Jihar Neja, inda wata fashewar ɗanyen abu ta auku a ranar Litinin, ta haddasa asarar rayuka da lalata dukiyoyi.

Tawagar ministan ta haɗa da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago; da tsohon gwamna kuma Sanata mai wakiltar Mazaɓar Neja ta Arewa, Alhaji Abubakar Sani Bello; da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Alhaji Abdulmalik Sarkin-Daji, da wasu jami’an gwamnati.

Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba.

“Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan yanki yana da albarkatun ma’adinai da dama.

“Kwanan nan, Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta Tarayya ta fara gyaran tsarin haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar nan, kuma muna fatan za su ɗauki wannan darasi da muhimmanci.”

Ministan ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Raya Ma’adanai ta Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen tsaftace harkar haƙar ma’adanai don kauce wa irin waɗannan haɗurran.

Haka kuma, ministan ya jaddada damuwar Shugaban Ƙasa kan yawaitar irin waɗannan bala’o’i a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa dole ne a ƙara wayar da kan al’umma domin daƙile aukuwar irin su a nan gaba.

Ya ce: “Abu na farko da ya kamata mu gane shi ne irin wannan bala’i yana faruwa sau da yawa a ƙasar mu, kuma Shugaban Ƙasa yana cikin matsanancin baƙin ciki. Ya kuma umarta cewa Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa ta gudanar da wayar da kai da faɗakarwa, musamman a cikin waɗannan ƙauyuka, domin hana aukuwar irin hakan a nan gaba.”

A ƙarshe, Idris ya yaba da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Neja ta yi wajen ɗaukar matakin gaggawa game da lamarin, tare da bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umarci Ma’aikatar Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci tare da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da su taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

Loading

Tags: Jihar Nejama'adinaiMohammed IdrisMohammed Umaru BagoSabon Pegi
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa BPP kan inganta gaskiya wajen sayen kayayyaki

Next Post

Cewar Cashman, sabon shugaban MOPPAN: Muna neman haɗin kan ‘yan Kannywood baki ɗaya

Related Posts

Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano
Nijeriya

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

July 5, 2025
Next Post
Cewar Cashman, sabon shugaban MOPPAN: Muna neman haɗin kan ‘yan Kannywood baki ɗaya

Cewar Cashman, sabon shugaban MOPPAN: Muna neman haɗin kan ‘yan Kannywood baki ɗaya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!