• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya ta musanta iƙirarin Binance na neman cin hanci

by WAKILIN MU
May 8, 2024
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tarayya ta musanta iƙirarin Binance na neman cin hanci

Alhaji Mohammed Idris

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta mayar da martani kan iƙirarin da Shugaban kamfanin Binance, Richard Teng, ya yi na cewa wai wasu jami’an gwamnatin Nijeriya sun buƙaci a ba su cin hanci da kuɗaɗen kirifto don warware binciken laifuffukan da ake yi wa masa.

Teng ya yi wannan iƙirarin ne a wani shafin yanar gizo wanda kafafen watsa labarai na ƙasashen waje suka buga ranar Talata, inda ya ƙara da cewa lauyan Binance ya ƙi amincewa da tayin.

Da yake mayar da martani kan zargin a ranar Laraba, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Teng ya ƙare da “dabarun karkatar da hankalin jama’a da kuma yunƙurin yin ɓatanci da kamfanin ke yi don kawar da tuhume-tuhume masu tsanani da yake fuskanta a Nijeriya.”

A wata sanarwar da Rabiu Ibrahim, mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai ya sanya wa hannu, ministan ya jaddada cewa wanda ya kafa Binance, Changpeng Zhao, ya aikata irin wannan laifin na halasta kuɗaɗen haram a Amurka, kuma a halin yanzu yana zaman gidan yari, lamarin da ke nuni da cewa ya kamata kamfanin na kirifto ya miƙa kan sa ga hukuma domin bincike.

Ya ce: “Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta na sane da yunƙurin da Binance ke yi na wanke sunan sa a matsayin kamfanin da ba ya bin ƙa’ida da dokokin da ke jagorantar harkokin kasuwanci a ƙasashe masu cin gashin kai.

“A cikin wani saƙon da ya wallafa a shafin yanar gizo wanda yawancin kafafen watsa labarai na ƙasa da ƙasa su ka wallafa a yanzu, Shugaban Binance Richard Teng, ya zargi kan wasu jami’an gwamnatin Nijeriya da ba a san ko su waye ba da cin hanci da rashawa, wanda ya yi iƙirarin cewa sun buƙaci a biya kuɗaɗen kirifto dala miliyan 150 don warware binciken laifuffukan da ake yi wa kamfanin.

“Wannan iƙirarin na Shugaban Binance ba gaskiya ba ne. Ba komai ba ne illa dabarar karkatar da hankalin jama’a da kuma yunƙurin yin ɓatanci da kamfanin ke yi don kawar da tuhume-tuhume masu tsanani da yake fuskanta a Nijeriya.

“Gaskiyar wannan al’amari ita ce ana binciken Binance a Nijeriya ne saboda yadda ya ba da damar yin amfani da dandalin sa wajen halasta kuɗaɗen haram, bayar da tallafi ga ta’addanci, da kuma tafka maguɗin kuɗaɗen ƙasashen waje ta hanyar cinikin haramun.”

Loading

Tags: Binancecrypto currencykiriftoMohammed IdrisRichard Teng
Previous Post

Ni na fara sa Ali Nuhu a fim, amma ana yaɗa ƙarya a tarihin shi – Sani Muhammad Sani

Next Post

Shigar Ali Nuhu harkar fim: Akwai gyara a iƙirarin Sani Muhammad Sani, inji darakta Salisu Mu’azu

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Shigar Ali Nuhu harkar fim: Akwai gyara a iƙirarin Sani Muhammad Sani, inji darakta Salisu Mu’azu

Shigar Ali Nuhu harkar fim: Akwai gyara a iƙirarin Sani Muhammad Sani, inji darakta Salisu Mu'azu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!