GWAMNATIN Tarayya ta bayyana alhini bisa ambaliyar da ta auka wa garin Mokwa a Jihar Neja, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba ɗaruruwan jama’a da muhallan su.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu cikakken bayani kan halin da ake ciki kan wannan ibtila’in, kuma ya umurci dukkan hukumomin agaji da na tsaro da su ƙara zage dantse wajen gudanar da ayyukan ceto da agaji.
Ya ce: “Tunani da addu’o’in mu suna tare da iyalan da suka rasa ‘yan’uwan su da kuma duk waɗanda ambaliyar ta shafa.”
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da haɗin gwiwar Sojojin Nijeriya da Gwamnatin Jihar Neja suna aiki ba dare ba rana wajen kai ɗauki ga waɗanda abin ya shafa.
Gwamnatin Tarayya ta yaba da jarunta da sadaukarwar jami’an farko da masu aikin sa kai da ke ci gaba da sanya rayuwar su cikin haɗari don ceton wasu.
Hukumomi na roƙon mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haɗari tare da haɗa kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa.
A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da jaddada cewa al’ummar ƙasar nan suna tare da su a wannan lokaci na jimami, kuma ba za a yi ƙasa a gwiwa wajen tallafa masu ba.