NA riski mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) da ya shahara a waƙoƙin siyasa a ofishin sa da ke Zoo Road, Kano. Mai bayar da umarni Iliyasu Abdulmuminu (Tantiri) ne ya jagoranci zaman.
Rarara ya ce mani: “Fim mai dogon zango na ke son farawa, mai suna ‘Gidan Dambe’. Kuma zan yi wannan fim ne domin taimaka wa tsoffin ‘yan fim ɗin Ibro, waɗanda a yanzu an jingine su saboda kowa ya koma ‘series’. Ina so a riƙa ganin su ko wasu za su ɗaga a riƙa kiran su aiki. Kuma mutane da dama, irin su Adam Zango da Tantiri da Maishadda, sun ce za ka iya, shi ya sa na ce a kira ka, mu zauna mu tattauna. Ga tsohon ɗan wasan Ibro nan Bawa Maikanwa, ya na da masaniya a kan harkokin dambe, sai a yi ‘sharing ideas’.”
Bayan kammala tattaunawar, na koma ina tunanin ta yaya zan fara. Tashin farko sai na haɗa marubutan da na ke tunanin za su taimaka min a wannan aiki. A karon farko na tarihin rayuwa ta, na kai ziyara babban gidan dambe na jihar Kano domin samun ƙarin haske. Na samu bayanai da yawa, na rubuta labari kamar yadda na samu bayanai da yawa na ƙarin ilimin rayuwa.
Harkar dambe a ƙasar Hausa na buƙatar kwaskwarima da kuma kulawa, kamar yadda su kan su ‘yan damben ke matuƙar buƙatar kulawa da kuma saiti. Siffofin su sun koma siffar ban-tsoro saboda tsabar shan bugu, yayin da wasu da dama su ka zama raunana, waɗanda a baya ƙarfafa ne.
‘Yan dambe na rayuwa ne da shan kayan maye domin gusar da tsoro da samun kuzari, wanda hakan ya na taka muhimmiyar rawa wajen raunata musu ƙarfin su a nan gaba. Kazalika, yawancin su na amfani da tsibbace-tsibbace da surkulle domin neman sa’a, maimakon mayar da hankali wajen motsa jiki. Baya ga haka, babu wani ƙwaƙƙwaran tanadi da ake yi dangane da lafiyar su ko kuma goben su.
Kamar yadda na fahimci ba mamaki da yawan su sun ta’allaƙa ne da wannan dambe ba tare da samun wata sana’a da za su dogara da ita ba. Yawancinsu na ɗauke da askin banza a kan su wanda a al’adar Hausawa ana kallon masu wannan askin a matsayin masu ƙarancin tarbiyya. Da yawan su su na da ƙarancin ilimin addini da na zamani, kuma yawancin su ba sa aure ballantana tunanin nan gaba idan ƙarfin su ya ƙare su na da masu tallafar rayuwar su.
Na fahimci hakan ne a gidan damben da aka gabatar da ajon wani ɗan dambe da ya yi aure, inda mai gabatarwa ya ke kiran sunayen manyan ‘yan damben ya na shawartar su da su daure su riƙa aure a matsayin hanyar samar da zuri’a.
Wasu da yawa sun zama abin tausayi; an ragargaza musu fuskoki da duka, ga ƙarfi ya ƙare, ga babu wata tabbatacciyar madogara, sannan ga shaye-shaye ya auri rayuwar su. Haka zaka gan su su na yawo cikin wani yanayi na abin tausayi, wasu na roƙo ana ɗan taimaka musu da ɗan wani abu.

Wasan dambe na da daɗin kallo ga masu ra’ayi, domin ana karɓar N500 a bakin ƙofar shiga kamar yadda a ciki ake karɓar kuɗin kujerun zama a kalli wasa. Kamar yadda akwai masu bayar da kuɗi ga gwarzon su lokacin da ya yi nasara, ko kuma ya yi aure.
Wani abu da na kasa ganewa shi ne cika da gidan ya ke yi da mata, musamman bisa la’akari da sanin cewa mata ba su faye son abubuwan tashin hankali da firgici ba. Kuma a wajen ana iya fasa wa wani baki ko hanci ko gefen ido. Duk da dai daga baya bincike ya tabbatar min da cewa manyan abokan ‘yan dambe su ne karuwai, bokaye da kuma mahauta.
Wasan dambe hanya ce ta zama shahararre a duniya saboda yadda a yanzu kafofin yaɗa labarai su ka ba shi muhimmanci, sannan kuma kafar sadarwa ta zamani na ɗauka su sanya shi ga masu sha’awar kallo a duniya. Gwamnati da ‘yan kasuwa su na sa gasar kuɗi da ababen hawa a matsayin gasa, wanda manyan ‘yan dambe daga ko’ina su na zuwa ana kuma samun kuɗin shiga a wajen ‘yan kallo.
A wannan rubutu da mu ke yi, mu na ƙoƙarin nuna yadda gwamnati da ‘yan kasuwa za su iya shiga harkar su kyautata wasan dambe a matsayin wasan gargajiya. Sannan mu shigar da illolin shaye-shaye da neman mata gami da zuwa wajen bokaye da rashin samun madogara a rayuwa. Sannan za mu yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin mawaƙi Rarara ya sa musu babbar gasa da za su amfana a rayuwa, mu kuma jawo hankalin kamfanoni su gyara musu wajen damben wanda ya na buƙatar kwaskwarima.
* Maje Elhajeej fitaccen marubuci ne kuma ɗan jarida da ke zaune a Kano. Shi ne ya rubuta labarin ‘Gidan Dambe’, dirama mai dogon zango wadda mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya ɗauki nauyin shiryawa.ko








