HUKUMAR Hisba ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta na shirin hana yin bukukuwa da dare a faɗin jihar, musamman ma fati.
Ta ce za ta yi haka ne saboda lokacin galibin bukukuwan da ake yi ya na karo da lokutan sallolin magariba da isha.
Mujallar Fim ta ruwaito Babban Kwamandan Hisba na jihar, Alhaji Muhammad Harun Sani (Ibn Sina), ya na bayyana hakan a yayin ganawar sa da manema labarai a Kano.
Ibn Sina ya ce yawancin ‘yanmatan da ke yin biki, musamman ma masu yi fatin dare, su na mancewa da yin waɗannan sallolin, ciku kuwa har da amarya.
Ya ce hukumar na shirin fito da wasu tsare-tsare ta yadda duk wani taron biki zai fara daga safe zuwa ƙarfe 4 na yamma.
Ya ce babban abin takaicin ma shi ne galibin wuraren da ake bukukuwan wurare ne da ake shan shisha da aikata al’amura marasa daɗi, da masu bikin ke fakewa da shi su na ɓarna.

“Wan an ya na tayar min da hankali, saboda yadda yaran mu da ƙannen mu ke rayuwar abin takaici,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Wannan abin ya kai a ce inna lillahi wa inna ilaihir raji’una kurum.
“Mu abin da mu ke so, a fito da tsarin da duk wani irin bukukuwa da za a yi, a yi ƙoƙari a yi shi tun daga safe har zuwa ƙarfe 4 na yamma. Duk inda 5 ta yi an rufe duk inda za a yi irin wannan bikin. Wannan shi ne tsarin da mu ke so mu yi.”