A RANAR Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022, aka yi bikin shekara-shekara na ‘Henna Ball’ wanda mujallar Tozali ke shiryawa.
Wannan shi ne karo na bakwai na bikin wanda aka gudanar a katafaren gidan tarurruka ɗin nan na International Conference Centre da ke Abuja.
A taron, an karrama ‘yan Kannywood uku – Rahama Sadau, Umar M. Sheriff, Khairat Abdullahi da Maryam Bukar Hassan (Alhanislam) – da sauran masu sana’o’in fasaha da kuma manyan mutane daban-daban.

An kuma ƙaddamar da hawan tashar talbijin ta Tozali TV a kan satalayit ɗin DStv wanda shugaban hukumar tashar, Alhaji Sirjo, ya yi.
Haka kuma an nishaɗantu da waƙoƙin Musa Morell da nunin tufafin zamani.
Manyan baƙi sun haɗa da Hajiya Maryam Abacha, Hon. Yakubu Dogara, Dakta Aliyu Modibbo Umar, Hajiya Ummi El-Rufai, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, Dakta Yusuf Datti Baba-Ahmed, da sauran su.

Shugabar kamfanin mujallar Tozali da gidan talbijin na Tozali TV, Hajiya Maimuna Yaya Abubakar, ita ce ta jagoranci shirya bikin.
Taron ya burge mahalarta ƙwarai da gaske, kuma ya tafi bisa tsari gwanin ban-sha’awa.
Ga wasu hotunan bikin da mu ka samo daga shafin Tozali da ke Facebook.







