ƊAN takarar zama shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi addu’ar kada Allah ya ƙara maimaita irin mulkin APC bayan 2023.
Atiku ya faɗi haka ne a lokacin da ya ƙaddamar yaƙin neman zaɓen sa na shiyyar Kudu-maso-yamma a Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Da ya ke jawabi a wurin gangamin, wanda ya samu halartar ɗimbin magoya bayan PDP, Atiku ya ce Nijeriya ta yi asarar shekara takwas da APC ta yi ta na mulki, wanda su ka jefa jama’a cikin mawuyacin halin da ba shi misaltuwa.
Ya yi fatan cewa, “Daga 2023, kada Allah ya sake jarabtar ‘yan Nijeriya da irin mulkin APC.”
Wazirin na Adamawa ya yi alƙawarin farfaɗo da harkokin ilimi tare da inganta shi, ya na mai cewa, “Gwamnatin APC ta kashe harkar ilimi a ƙasar nan ta hanyar bijiro da tsare-tsaren da kowa ya san ba za su inganta cigaban ilmi ba.”
Ya ƙara jaddada irin alƙawarin da ya yi a Ilorin, wanda ya ce idan ya yi nasara, gwamnatin sa za ta ware dala biliyan 10 domin bunƙasa ƙanana da matsakaitan masana’antu, ta yadda matasa za su yunƙuro wajen samun aikin yi sosai, kuma su ma mata rayuwar su za ta ƙara bunƙasa.
Kafin ya fara jawabi, sai da uwargidan sa, Hajiya Titi Abubakar, ta fara yi wa dandazon magoya bayan PDP jawabi tukunna.
Titi, wadda haifaffiyar Jihar Ondo ce, ta ce ta yi farin cikin ganin PDP ta fara kamfen ɗin shiyyar Kudu-maso-yamma a jihar ta ta haihuwa.
Ta ce: “Ina gabatar da kai na a gare ku, a matsayi na na ‘yar ku. Idan ku ka zaɓi miji na, zai daƙile Boko Haram kuma zai inganta ilimi.

“Kada ku manta, miji na ne ya yi nasara a zaɓen 2019, amma aka yi masa maguɗi, aka murɗe zaɓen. To kada ku bari a sake yaudarar ku. Wannan lokacin ma ku fito ku sake zaɓen PDP.
“Idan Atiku ya yi nasara, wata dama ce da Jihar Ondo za ta samu cewa ‘yar su za ta zama uwargidan shugaban ƙasa. Da ma kuma Bayarabiya ba ta taɓa zama uwargidan shugaban ƙasa a Nijeriya ba.”
Da ta ke yabon mijin ta, Titi ta ce ko lokacin da ya na mataimakin shugaban ƙasa ya yi rawar gani, domin shi ne ya janyo irin su Nasir El-Rufai da Ngozi Okonjo-Iweala cikin gwamnati, “har da ma wasu fitattun haziƙan da su ka kawo cigaba a ƙasar nan.”
Mataimakin takarar Atiku, Gwamna Ifeanyi Okowa, shi ma ya ce PDP za ta farfaɗo da fannin ilimi. Sannan ya nuna damuwar sa dangane da yadda ɗaliban jami’a su ka shafe watan takwas a gida, ya na mai cewa ba za a samu irin haka a gwamnatin su ba.
Shi ma Gwamna Udom Emmanuel ya roƙi al’ummar Jihar Ondo da su zaɓi Atiku, wanda ya ce shi kaɗai a cikin sauran ‘yan takarar zai iya haɗa kan Nijeriya.
Shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu, da Babban Daraktan Kamfen, wato Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto, duk sun yi wa taron jawabai masu nuna fifikon Atiku kan sauran ‘yan takara.