• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Batun A’isha Buhari: Ni ma ba zan iya ɗaukar wulaƙancin yaran soshiyal midiya marasa tarbiyya ba – Mansurah Isah

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 1, 2022
in Labarai
0
Mansurah Isah

Mansurah Isah

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHUWAR jaruma a Kannywood kuma furodusa, Mansurah Isah, ta ja kunnen mutane da kada wanda ya ce ta yi magana a kan matar shugaban ƙasa, A’isha Buhari.

A wannan makon dai muhawara ta ɓarke kan shari’ar da ake yi tsakanin matar shugaban ƙasar da wani ɗalibin jami’a da ya faɗi baƙar magana a kan ta a Twitter.

Aisha Buhari ta maka shi a kotu bayan jami’an tsaro sun kamo shi sun kawo shi Abuja.

Mansurah ta yi maganar ne a Instagram, inda ta ɗora hoton rubutun da ta yi da Turanci. Mujallar Fim ta fassara rubutun kamar haka: “Kada wanda ya tambaye ni in ce wani abu a kan A’isha Buhari. Ni ma na taɓa shiga wannan halin. Haka ‘ya ta ma ta taɓa shiga irin wannan halin. Na ce a’a da cin mutuncin soshiyal midiya da kalaman ƙiyayya.

“Ni ba matar shugaban ƙasa ba ce ko iyalin sa. A matsayi na na ‘yar wasa, na san yadda mu ke ji, inda wasu wawaye, marasa kunya, mahaukatan mutane, su kan zo soshiyal midiya, su na faɗin abubuwa a kan mu, su zage mu, su kira mu da sunaye kala-kala. 

“Wasu lokuta mu yi kuka a ɓoye. Manyan jaruman duniya da ba za su iya ɗauka ba, kan kashe kan su. 

“Ba zan kashe kai na ba, amma ba zan taɓa barin wanda ba shi da tarbiyyar gida ya yi wasa da rayuwa ta ko lafiya ta ba. Za su yi basaja da sunan ka, su ɗora bidiyon marasa lafiya a matsayin kai ne.

“Wallahi, wallahi, abin da ciwo, har ta kai  ƙarshe, na kai wasu marasa kunya gidan yari. Ba zan ɗaukar wa kai na ko iyali na ba. Kada ku taɓa ni, shi kenan.”

A ƙasan hoton da ta ɗora ɗin kuma, sai ta rubuta cewa, “Ƙananan  yara za su zo soshiyal midiya su zage ka, su ci mutuncin ka, su ci zarafin ka da sauran su.

“Haka kawai, ba abin da ka yi musu don su na ganin sun isa, ba a isa a yi musu komai ba.

Maganar da Mansurah ta rubuta

“Za su buɗe yanar gizo da sunan ka, su rinƙa ‘posting’ ɗin batsa , satar kuɗin mutane da ɓatanci da sunan ka. Sannan a ce kar ka ɗauki mataki, haba jama’a, mu rinƙa yi wa junan mu adalci!”

“Ɓatanci a ‘social media’ addini ne?

“Munafukin mutum ɗan ‘social media’ (like influencer na social media) shi ne zai ce ba a yi daidai ba.”

“Akwai wata kwanaki da su ka biyo ta har cikin ‘dm’ (diract message) ɗin ta su na cin zarafin ta, wallahi sai da ta kwanta a asibiti. 

“Ni ce nan na yi mata wa’azi cewa sai haƙuri kawai da yi musu Allah ya isa.”

Loading

Tags: Aisha BuhariɓatanciMansurah Isahsoshiyal midiya
Previous Post

Shekara takwas na mulkin APC asara ce ga Nijeriya – Atiku

Next Post

Taro: An tashi ba shiri tsakanin hukumar tace finafinai da masu sana’ar fassara finafinan Indiya

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Mahalarta taron

Taro: An tashi ba shiri tsakanin hukumar tace finafinai da masu sana'ar fassara finafinan Indiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!