A YAU ne fitacciyar jarumar Kannywood, Jamila Umar Nagudu, ta ke murnar zagayowar ranar haihuwar ta.
Jamila, wadda uwa ce ga ɗan ta ɗaya, wato Mus’ab, ba ta shirya wani biki a bayyane ba, amma ta ɗora hotunan musamman da ta ɗauka domin wannan rana a Instagram.

‘Yan fim da dama sun taya ta murna tare da yi mata fatan alheri a wannan rana ta ‘birthday’ ɗin ta.
Ga hotunan nan mujallar Fim ta kawo maku. A sha kallo lafiya.



