MASANA’ANTAR shirya finafinan Hausa ta ƙara girgiza a yau sakamakon rasuwar fitaccen mawaƙi, edita kuma mai riƙe kyamara Alhaji Ibrahim Achimota.
Allah ya yi masa rasuwa ne a Jos a yau, sakamakon rashin lafiya daga cutar suga.
Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa ya yi fama da wannan ciwo tsawon sama da shekara 20.
Ya rasu ya na da shekara 50, domin kuwa an haife shi a ranar 10 ga Oktoba, 1971.
Ya rasu ya bar matar sa ɗaya da ‘ya’yan sa shida (mata uku, maza uku).
Babban ɗan sa ya yi aure, ya na zaune a Jihar Adamawa, yayin da kuma ya na da wata ‘ya da ke aure a Legas.
An yi jana’izar sa ɗazu a Jos.
‘Yan fim da dama sun kaɗu da su ka ji labarin wannan rasuwa ta Achimota.
Jarumi Alhaji Sani Mu’azu, wanda shi ne tsohon haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan Kannywood, wato MOPPAN, ya ce, “Achimota ya na ɗaya daga cikin ƙwararrun masu kyamara daga Jos kuma ya ɗauki finafinai da dama tun a shekarun farko na masana’antar.”
Ya ƙara da cewa, “Ciwon suga (diabetes) ya rage masa karsashi, wanda hakan ta tilasta masa ja da baya a tsawon shekaru. Ya yi ta fatan zai dawo don ci gaba da harkokin sa har dai rai ya yi halin sa a yau.”

Sani Mu’azu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga dukkan ‘yan’uwan marigayin masu shirya finafinai da ke Jos, da kuma iyalan sa. Ya ce, “Allahu (SWT) ya ba mu haƙurin jure wannan rashi, amin.”
Jarumi mazaunin Jos, Malam Tijjani Paraga, shi ma ya ce, “Allah gafarta masa, ya yafe masa kurakuren sa, ya sa Aljanna makomar sa, amin.”
Babban furodusa Sani Muhammad Sani, wanda ya yi aiki da Achimota a Jos, ya faɗa wa mujallar Fim cewa Achimota ƙwararren edita ne kuma mawaƙi wanda ya koya wa mutane da yawa aikin editin da na kyamara.
Ya tuno da cewa shi kan sa matar sa, Hussaina Sani Muhammad Sani, wadda mawaƙiya ce a wancan lokaci a farkon Kannywood, ta taɓa aikin rera waƙa tare da Achimota a wani fim na Sanin mai suna ‘Rana Zafi Inuwa Ƙuna’.
Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya yafe masa kurakuran sa.
Shi dai Achimota, ya taɓa yin aiki a kamfanin Lenscope Media na Sani Mu’azu, inda su ka yi aiki tare da su Ibrahim Danko. A nan ne ma ya yi wa fim ɗin ‘Daɗin Duniya’ na Sani Mu’azu waƙoƙin da ke cikin sa.
Daga baya, ya buɗe nasa situdiyon a kusa da gidan sinima na Kwararafa, a Jos, inda ya riƙa editin na finafinai da kuma buga waƙa.
Mu ma a mujallar Fim mu na addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya yafe masa kurakuran sa, kuma ya ba iyalin sa haƙurin jure wannan babban rashi, amin.


![]()







