• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnati ta fara binciken yadda fuskokin fatara su ke a Nijeriya

by DAGA IRO MAMMAN
August 10, 2021
in Nijeriya
0
Gwamnati ta fara binciken yadda fuskokin fatara su ke a Nijeriya
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MA’AIKATAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana wani safiyo da ta ke yi kan yadda fatara ta ke ta fuskoki daban-daban a ƙasar nan (Multidimensional Poverty Index (MPI) Survey).

Minista Sadiya Umar Farouq ce ta ƙaddamar da  safiyon na MPI ta hanyar yanar gizo a ranar Talata.

A lokacin ƙaddamarwar, ministar ta ce Nijeriya ta bi sahun ƙasashe da su ka fara inganta hanyoyin su na yanke shawarar gudanar da shirye-shirye ta hanyar amfani da bayanan da aka samu daga binciken na MPI.

Ta ce, “Kowa ya amince a yi aiki da tsarin MPI ne saboda hanyoyi daban-daban da kuma yarjejeniyoyin ƙasashen duniya da aka yi, ciki har da Muradan Cigaban Ƙarni na Duniya, wato ‘Millennium Development Goals’ (MDGs), waɗanda an maye gurbin su da Muradan Cigaba Masu Ɗorewa, wato ‘Sustainable Development Goals’ (SDGs) domin su shafo sassa daban-daban na rashi wanda shi ne ruhin fatara da abubuwa masu alaƙa da ita.
 “Saboda haka abin farin ciki ne mu tafi tare da sauran muryoyi masu ƙarfi wajen hasko muhimmancin aiki da masu ruwa da tsaki daban-daban a kan yaƙi da fatara, kawar da yunwa, bada nagartaccen ilimi, matakan yanayin ƙasa da kuma rungumar kowa, waɗanda dukkan su muhimman abubuwa ne wajen shaidar da MPI ke samarwa.”
 Sadiya Umar Farouq ta lura da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu nasarar inganta rayuwar sama da mutum miliyan 10 ta hanyar fidda su daga matsananciyar fatara ta hanyar ɗimbin shirye-shiryen gwamnatin, waɗanda su ka haɗa da shirin inganta rayuwa na ƙasa, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP), da GEEP, Npower, NHGSFP da wasu da dama. 

Ta ce, “Wannan muradin ya na yin la’akari da yawan jama’ar da ƙasar nan ta ke da shi yanzu wanda ya kai kimanin mutum miliyan 200, da kuma buƙatar samar da ingantacciyar shaida don tsara shiri. 
“Don haka Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya  ta tsaya tsayin daka wajen yin haɗin gwiwa da hukumomin gwamnati daban-daban, da ƙungiyoyin bada agaji da kuma masu zuba jari masu zaman kan su domin sa hannu a shirye-shirye tare da tabbatar da tasiri ga aiki ta hanyar bayanan da aka tattaro daga MPI don tabbatar da gaskiyar gwamnati ga al’ummar ƙasa ta hanyar ingantaccen sa-hannu ga shirye-shiryen gwamnati ta fuskoki da dama waɗanda za su tumɓuko tushen fatara.

“Bugu da ƙari, ma’aikatar za ta haɗa gwiwa sosai da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, wato ‘National Bureau of Statistics’ (NBS), domin gudanar da bincike a kai a kai a kan fatara ta hanyoyi daban-daban tare da yadda ake kashe kuɗi a matakan ƙasa baki ɗaya da na jihohi don tabbatar da matsayin da fatara ta ke a Nijeriya kuma a yi amfani da abin da aka binciko wajen gudanar da wani shiri ko tsari na gwambati.”

Ma’aikatar za ta haɗa gwiwa da mutane ‘yan kasuwa ko kamfanoni ta hanyar yin amfani da hanyar musamman ta shirye-shiryen haɓaka rayuwa don a ƙirƙiro wata taswira ko na’urar bin diddigi ta fatara a matakin ƙasa da na jiha wanda hakan zai taimaka wajen samar da cigaba a ƙudirorin rage fatara.

Haka kuma za ta haɗa gwiwa da Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare na Ƙasa ta hanyar amfani da bayanan  MPI don inganta rarraba kasafi ga sashe da jiha don kai wa ga mutane da ƙauyuka da gundumomi masu tsananin buƙatar kulawa.

Ministar ta gode wa Bankin Duniya, UNDP, OPHI, UNICEF, Ofishin Jakadancin Kanada, da sauran hukumomin ƙasa da ƙasa saboda tallafin da su ke bayarwa wajen kawar da matsananciyar fatara ya zuwa shekarar 2030.

Manyan baƙi da su ka bada saƙwannin goyon baya a taron sun haɗa da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt Hon. Femi Gbajabiamila, wanda Hon. Sanusi Garba Rikiji ya wakilta, da kuma Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, da Ƙaramin Ministan Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Prince Clem Agba, da Babban Jakaden Kanada a Nijeriya, da Wakilin Ƙasa na UNDP, Mista Mohammed Yahaya, UNICEF, da Daraktan OPHI, Shugaban Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), Dakta Yemi Kale, da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Al’amuran Tattalin Arziki, Ambasada Yemi Dipeolu, da Sabine Alkire daga Jami’ar Oxford, da Kodineta na Ƙasa na ofishin tallafa wa al’ummar ƙasa, wato ‘National Social Safety Nets Coordinating Office’ (NASSCO), Mista Iorwa Apera.

Loading

Tags: Disaster Management and Social DevelopmentMinistry of Humanitarian AffairsPoverty reductionSadiya Umar Farouq
Previous Post

Jarumar Kannywood Zahra Diamond ta yi aure a asirce

Next Post

Rasuwar mawaƙi Ibrahim Achimota ta girgiza Kannywood

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Rasuwar mawaƙi Ibrahim Achimota ta girgiza Kannywood

Rasuwar mawaƙi Ibrahim Achimota ta girgiza Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!