• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 12, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumar Kannywood Zahra Diamond ta yi aure a asirce

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
August 10, 2021
in Ranar Murna
0
Jarumar Kannywood Zahra Diamond ta yi aure a asirce
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMAR Kannywood mai tasowa, Zahra Muhammad (Zahra Diamond), ta yi aure asirce, abin da ya ba mutane da dama mamaki.

Zahra da kan ta ne ta alamta hakan a wani saƙo da ta wallafa a Instagram a ranar Lahadi, 8 ga Agusta, 2021 inda ta ba furodusoshi da daraktoci haƙuri kan rashin ƙarasa masu finafinan su da ba ta yi ba.

Ta ce: “Salam masoya na, ‘producers’ ɗi na, ‘directors’ da abokan aiki na, waɗanda na gama ayyukan su ina musu fatan alkairi, waɗanda kuma ban gama ba ina mai ba su haƙuri, saboda yanayin zaɓin da Allah ke yi wa dukkanin bayin sa, to ya min zaɓi mafi alkairi a gare ni, saboda haka ba ni da baki ko ‘yancin ƙarasa muku ayyukan ku. Fatan za ku fahimce ni? Allah ya ba ku haƙuri ya kuma musanya muku da alkairi.”

Haka kuma ta yi kira ga mamallakan shafukan mabiyan ta da su cire hotunan ta da bidiyoyin ta daga shafukan, domin fa ita ta yi bankwana da harkar fim.

Saƙon da Zahra Diamond ta wallafa game da auren ta a Instagram

Ta ce, “Don Allah masu ‘fans page’ ɗi na, ku yi haƙuri ku dubi girman Allah ku cire hotuna ɗi na da kuma bidiyo-bidiyo ɗi na, kuma ku canza suna na. Na gode.”

Duk da cewa a wannan saƙon jarumar ba ta ambaci ta yi aure ba, mutane da dama na ganin cewar ta yi aure ne.

Sanarwar ta bai wa jarumai da dama mamaki domin a cewar wasu daga cikin su ko kaɗan ba su kawo wa jarumar aure kusa ba musamman idan aka yi la’akari da yadda a hirar ta da BBC Hausa kwanan nan ta bayyana ƙudirin ta na zama shahararriyar jaruma.

Jarumai da dama sun wallafa hotunan Zahra a shafukan su na soshiyal midiya tare da yi mata fatan alheri.

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jarumar kan wannan al’amari, amma haƙar mu ba ta cimma ruwa ba. 

Mu na addu’ar Allah ya ba Zahra da sabon mijin ta zaman lafiya da zuriya ɗayyiba.

Yadda mawaƙi kuma jarumi Ado Gwanja ya taya Zahra Diamond murnar auren da ta yi
Zahra Muhammad (Zahra Diamond) ta faɗa wa BBC Hausa kwanan nan cewa burin ta shi ne ta zama shahararriyar jaruma

Loading

Tags: hausa actresshausa filmsKannywoodZahra Diamond
Previous Post

Hotunan taron gangamin yi wa Umma Ali addu’a

Next Post

Gwamnati ta fara binciken yadda fuskokin fatara su ke a Nijeriya

Related Posts

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Mawaƙi Sa’eed Ja’afar ya samu ƙaruwa da ‘ya mace
Ranar Murna

Mawaƙi Sa’eed Ja’afar ya samu ƙaruwa da ‘ya mace

July 6, 2026
Furodusa Alhaji Sheshe da Khairiyyah sun zama ɗaya
Ranar Murna

Furodusa Alhaji Sheshe da Khairiyyah sun zama ɗaya

July 4, 2026
Abokai sun shirya yin walima don taya jarumin Kannywood AS Bello murnar zama Farfesa
Ranar Murna

Abokai sun shirya yin walima don taya jarumin Kannywood AS Bello murnar zama Farfesa

July 2, 2026
Furodusan Kannywood Alhaji Sheshe zai angwance ranar Asabar
Ranar Murna

Furodusan Kannywood Alhaji Sheshe zai angwance ranar Asabar

June 29, 2026
Next Post
Gwamnati ta fara binciken yadda fuskokin fatara su ke a Nijeriya

Gwamnati ta fara binciken yadda fuskokin fatara su ke a Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!