ARULI (ko Arudi) wani ilimi ne wanda ake auna waƙar Larabci a kan sa, kuma ta shi ne ake gane shin waƙar ta na da illa ko kuɓutacciya ce daga illar. Sannan ya na daga amfanin sanin wannan ilimi:
– bambance tsakanin waƙa da rubutun zuɓe;
– bambance ma’aunan waƙar masu lafiya da masu illa;
– ƙwanƙwance waƙar da sanin abin da ke faɗa mata na aibu da yadda za a magance shi;
– sanin abin da ya harasta da wanda bai halasta ba a waƙar;
– da sauran su.
Ɗaya daga cikin jagororin harshen Larabci ne ya ƙirƙiri wannan ilimin, wato Khalil bin Ahmad Alfarahidi Albasari, mai littafin ƙamus na farko.

Tun sama da shekaru ɗaruruwa, Allah ya azurta ƙasar Hausa da manyan malamai masu rubuce-rubuce a fannoni mabambanta. Ya ishe ka misali don gane wannan fannin na ilimin Arudy shi Malam Khalil bin Ahmad Alfarahidi ya sanya masa baharai guda 15, almajirin sa Ahfash ya ƙara ƙwara ɗaya, su ka zamo 16. Amma cikin liɗifin Ubangiji (s.w.t.) kakar Shehu Mujaddadi Usmanu Ɗanfodiyo, Sayyada Ruƙayyatu ‘yar Muhammad ɗan Sa’idu (Allah s.w.t. ya yi mata rahama), ita ma ta ƙirƙiri baharin ta mai taf’ila kamar haka:
فاعلن فعولن فاعلن فعولن // فاعلن فعولن فاعلن فعولن
inda ta kira shi da Bahrul Karim:
” بحر الكريم “.
A ɓangaren tadwini kuwa na wannan babban ilimi mai albarka, an samu manyan malamai da su ka yi rubuce-rubuce a kan sa kamar haka:
1- Malam Abdullahi bin Fodiyo (R) ya rubuta:
فتح اللطيف الوافي في علمي العروض والقوافي
a waƙe cikin baiti 215, wanda ɗaya daga cikin malaman Ƙauran Namoda, Malam Sulaiman Aliyu, ya yi masa ta’aliƙi mai kyau inda ya ke faɗa a shimfiɗar littafin:
إن شعت فهم عروض والضرب / فعليك بالفتح اللطيف الوافي
In ka so fuskantar ilimin Aruli, to ka nemi wannan littafi na Malam Balaraben Hausa:
حاوى فرائد شعر عربي مع / الاتقان في أوزانه وقوافى
Ya tattaro manyan mas’alolin sanin wazanan waƙa da ƙafiya:
إن يسئلونك عن مؤلفه فقل / من غير ترديد بقلب ما فى
In an tambaye ka na waye littafi, faɗa kan ka tsaye kar ka ji tsoro, ka ce:
للعالم النحرير عبدالله كا / شف علة الأوزان معا وزحافى
Na Malam Abdullahi ne wanda shi mutum ne wanda ya kai maƙura a kaifin basira wanda ya warware wazanai da zihafi.
Alhamdu lillah, Allah ya azurta ni da samun rubutun hannun Malam Sulaiman ɗin da kuma wanda Mash-Hudul Kunti ya buga.
2 – Littafin da Sheikh ibni Ishaq ya rubuta mai suna:
فن علم العروض.
3 – Waɗanda Dakta Waziri Junaidu ya rubuta:
– المبادئ الضرورية في الدروس العروضية. – اصطلاح فن العروض.
4 – Wanda Farfesa Sarki Ibrahim na BUK ya rubuta cikin juzu’i biyu:
أثمار اليانعة في العروض والقافية.
5 – Wanda Sheikh Musal Ƙasiyuni Kabara ya rubuta:
الصافي في علم القوافي.
6 – Wanda Sheikh Umar Ɓagarawa ya rubuta:
المورد الصافي في علم العروض والقوافي
7 – Waɗanda matashin malami Abdurrahman Umar Ɓagarawa ya wallafa:
– كشف السر الخافي في فتح اللطيف الوافي. – اتحاف الخليل الوافي بعلمي العروض والقوافي
Cikin baiti 99:
– المنهل العذب الصافي، شارحا لاتخاف.
Allah ya kare mana wannan turasi na wannan yanki, ya ƙara wa maluman mu lafiya, ya hore masu irin waɗannan aikace-aikace, ya jiƙan magabatan da su ka gina ayyukan, ya ƙarfafi masu yi da masu niyya.
Alhamdu lillah.
Ibrahim Albrahiɓ Algetsawy malamin addini ne a Getso, Jihar Kano
Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com