• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ba ta nuƙu-nuƙu da kayan zaɓe, za mu bai wa masu shigar da ƙara bayanan da kotu ta ce a ba su – Yakubu

by DAGA WAKILIN MU
March 15, 2023
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu

Farfesa Mahmood Yakubu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a shirye ta ke ta damƙa kwafen bayanai da dukkan kayan da kotu ta bayar da umarni ga jam’iyyu ko ‘yan takarar da ke ƙorafi kan zaɓen ranar 25 ga Fabrairu, domin su yi nazarin da su ke so su yi.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi tawagar lauyoyin jam’iyyar  Labour (LP), bisa jagorancin Babban Lauya Livy Uzoukwu.

Tawagar lauyoyin dai ta ziyarci hedikwatar INEC ne a ranar Litinin a Abuja.

Yakubu ya tabbatar masu da cewa ya karɓi wasiƙar da LP ta aika masa a ranar 6 ga Maris, wadda ta sanar da shi cewa lauyoyin ta za su kai ziyara INEC domin duba kayan zaɓe.

Ya ce wasiƙar na ɗauke da ƙarin bayanin sanar da shi cewa ya sanar da Kwamishinonin Zaɓe na INEC da ke a kowace jiha, cikin jihohi 36 na faɗin ƙasar nan da Abuja.

Wasiƙar dai ta nemi INEC ta umarci Kwamishinonin Zaɓe na jihohin su damƙa wa LP bayanai da kayan da ta ke buƙata domin gabatar da bayanan ƙarar ta a kotu.

Yakubu ya ce INEC ta shirya gudanar da taro da Kwamishinonin Zaɓe, domin su tattauna batutuwa da dama, ciki har da batun bayar da sahihan kwafe-kwafe na bayanan zaɓe ga dukkan waɗanda su ka shigar da ƙara, ba ma ga LP ita kaɗai ba.

“Ina tabbatar maku da cewa INEC ba ta wani nuƙu-nuƙun ɓoye komai. Za mu ba ku dukkan abin da ku ke buƙata.

“Kwafen bayanai biyu ne ke a hannun Hedikwatar INEC nan a Abuja. Kuma za mu iya samar maku waɗannan kwafen ba tare da  ɓata lokaci ba. Akwai kwafen sakamako na EC8Ds da aka tattara daga jihohi da kuma mai lamba EC8DA, wanda sakamakon zaɓe ne da INEC da kan ta ta tattaro daga cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

“Mai lamba EC8DA dai ina jin kwafe 39 ne. Kuma za mu iya samar maku kwafen su ba tare da ɓata lokaci ba,” inji Yakubu.

Ya ce sauran kwafen bayanai kuma duk su na ofisoshin INEC na jihohi daban-daban, kuma hukumar za ta so sanin ranakun da lauyoyin za su je jihohi domin a shirya masu kwafen kafin su isa, yadda su na zuwa sai dai su fara nazari kawai’.

“Sauran bayanai kuma alƙaluma ne lambobi da bayanan tantance mai shaidar katin rajistar zaɓe na rumfunan zaɓe fiye da 176,000.

“Za mu samu lokaci mu buga kwafe-kwafen su a wadace, sannan mu damƙa maku cikin hanzari.”

Daga nan ya shawarci tawagar lauyoyin INEC su gana da lauyoyin INEC domin su bayyana wa juna batutuwa da dama.

Jagoran tawagar lauyoyin LP, Uzoukwu ya shaida wa Yakubu cewa dalilin ziyarar shi ne domin su share hanyar fara nazarin kayan zaɓen shugaban ƙasa. “Saboda ka san dai mu na da kwanaki 21, waɗanda a cikin su ne za mu shigar da ƙara, a madadin waɗanda mu ke karewa. Yanzu kuma daga cikin kwanaki 21 ɗin, kusan kwanaki 10 kaɗai ne su ka rage mana. Ga shi kuma har yau ɗin nan ba mu karɓi kwafen takardun bayanai ko kayan zaɓe ko da guda ɗaya ba.”

Loading

Tags: INECkotuLabour PartyLivy UzoukwuLPmahmood yakubuZaɓen 2023
Previous Post

Dakan-ɗaka-shiƙar-ɗaka: An saka ranar auren darakta Kamal Alƙali da jaruma Hauwa SG

Next Post

Tallar ‘yan takara: Mun gama shan wahala an yi watsi da mu, inji Fati Nijar

Related Posts

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa
Nijeriya

Tinubu ya yaba wa Sule Lamiɗo a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar sa

May 13, 2025
Next Post
Fati Nijar: An ci moriyar ganga ne?

Tallar 'yan takara: Mun gama shan wahala an yi watsi da mu, inji Fati Nijar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!