• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta fara horas da ma’aikatan wucin-gadi miliyan 1.2 domin aikin zaɓen 2023

by DAGA WAKILIN MU
February 8, 2023
in Nijeriya
0
Mista Festus Okoye ya na gabatar da jawabin sa a wajen horon

Mista Festus Okoye ya na gabatar da jawabin sa a wajen horon

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fara aikin horas da ma’aikatan da za su yi aikin zaɓen 2023 a cikin Fabrairu da Maris.

Ma’aikatan na wucin-gadi su miliyan 1 ne da 265,227, kamar yadda Babban Jami’in Wayar da Kai kuma Kwamishina na INEC, Mista Festus Okoye, ya bayyana a ranar Litinin, a wurin bayar da wani horon a ranar Litinin.

Ya ce hukumar ta ɗauki wannan horaswa da muhimmanci, ganin cewa Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sha alwashin tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe, karɓaɓɓe, kuma wanda jama’a za su yi tururuwar fita su jefa ƙuri’a.

Okoye ya ƙara cewa haka kuma wannan zaɓe mai zuwa, zaɓe ne wanda za a yi amfani da na’urar fasaha a wurin zaɓe.

Ya yi tsinkayen cewa aikin ofishin sa ne wanda aka ɗora wa haƙƙin shawartar Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (REC) da jami’an zaɓe hanyoyin da su ka fi dacewa su fahimtar da jama’a batutuwan da su ka danganci amfani da na’urorin fasaha a lokacin zaɓe.

Wani sashe na mahalarta taron (Hotuna daga: INEC)

Ya ƙara da cewa a ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris ‘yan Nijeriya za su zaɓi shugaban ƙasa, sanatoci 109, mambobin majalisar wakilai su 360, gwamnoni 28, sai mambobin majalisar dokoki 993.

Ya ce mutum miliyan 93 da 469,008 ne su ka yi rajistar katin zaɓe, kuma ake sa ran za su fita su jefa ƙuri’a a ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris.

Ya ce: “Zaɓen 2023 zai tafi ne a bisa tsarin amfani da na’urar fasahar zamani. INEC za ta yi amfani da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe, wato BVAS a dukkan rumfunan zaɓe 176,846 a ƙasar nan.

“Kuma INEC ta yi gwajin waɗannan na’urorin, wato BVAS ta tabbatar da ingancin su. Yanzu haka ana ci gaba da ba su lambobin tantance mai katin shaidar rajistar zaɓe, ta yadda za su kasance lambobin sun zama mabiyi da mabiyi, ko ɗaya bayan ɗaya a lokacin zaɓe.”

A cewar Okoye, Sashen Dokar Zaɓe na 47(2) ya tilasta cewa babu wanda zai yi zaɓe ba tare da an tantance shi na BVAS ba.

Ya ƙara da cewa: “Za a yi amfani da baturen zaɓe  707, 384 da su ka haɗa da mataimakan su. Sai kuma wasu ma’aikata 17,685 a matsayin turawan zaɓe masu sa-ido, jami’an tattarawa da bayyana sakamakon zaɓe su 9,620, sai kuma jami’an tsaron rumfunan zaɓe su 530,538. Ya ce gaba ɗaya idan an haɗa, sun cika 1,265,227 kenan.

Dukkan waɗannan su na ci gaba da samun horon sanin makamar aiki, yayin da nan da ‘yan kwanaki za a ci gaba da bayar da horon ga saura, inji shi.

Loading

Tags: BVASDokar ZaɓeFestus OkoyehoroHukumar ZaɓeINECma'aikatan wucin-gadimahmood yakubuZaɓen 2023
Previous Post

Za mu mayar da littafin ‘Daƙiƙa Talatin’ zuwa fim mai dogon zango, inji Gidan Dabino

Next Post

2023: Yadda ziyarar shugaban INEC hedikwatar CBN ta cire shakkun samun tangarɗar kuɗaɗen sallamar ma’aikatan zaɓe

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Daga hagu: Farfesa Mahmood Yakubu ya na gaisawa da Mista Emefiele a lokacin ziyarar

2023: Yadda ziyarar shugaban INEC hedikwatar CBN ta cire shakkun samun tangarɗar kuɗaɗen sallamar ma'aikatan zaɓe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!