• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta fito da matakai 4 na hana maguɗi a zaɓen 2023

by DAGA WAKILIN MU
November 2, 2022
in Nijeriya
0
INEC ta fito da matakai 4 na hana maguɗi a zaɓen  2023
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta samo wasu ƙwararan matakai huɗu da ta tabbatar da cewa babu wata hanya da za a iya bi a yi maguɗi a zaɓen 2023.

Mataimakin Sakataren INEC, Injiniya Chidi Nwafor, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron zaburar da matasa muhimmancin zaɓe, wanda ƙungiyar Yiaga Africa ta shirya a Inugu.

A cewar sa, mataki na farko shi ne dabarar tantance wanda ya yi rajistar mallakar katin zaɓe sau biyu ko fiye da haka, wato ‘Biomodal Voter Accreditation System’ (BVAS).

Na biyu shi ne amfani da na’urar tantance adadin masu zaɓe a rumfunan zaɓe, wato ‘INEC Voter Enrollment Device’ (IVED). Shi wannan tsari ya na maganin masu satar ƙuri’a ko ɓarayin akwatin zaɓe.

Na uku shi ne manhajar tattara sakamakon zaɓen da kowa zai iya gani ido-da-ido, wato ‘INEC Result Viewing Portal’ (IRVP).

Mataimakin sakataren ya ce Dokar Zaɓe ta 2022 ita ce mataki na huɗu na hana maguɗin zaɓen.

Yanzu dai saura kwana 116 a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar wakilai da na majalisar dattawa.

Idan ba a manta ba, a farkon Oktoba shi ma Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar da cewa maguɗi ba zai yiwu a zaɓen 2023 ba.

A labarin, ya ce INEC ta fito da hanyoyin kashe maguɗin zaɓe.

Yayin da hukumar ke ci gaba da tsare-tsaren gudanar da zaɓubbukan 2023, shugaban ya bugi ƙirji da cewa INEC ta samu nasarar toshe duk wata ƙofar da za a iya bi a yi maguɗi.

Da ya ke jawabi a wani taron da aka shirya a Cocin St. James na Ɗariƙar Angalika da ke Asokoro, Abuja, a kwanan baya, Yakubu ya ce INEC ta samu wannan gagarumar nasara ne ta hanyar ƙirƙiro tsarin tantance mai rajistar zaɓe na ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato BVAS.

Yakubu, wanda Mataimakin Kakakin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ba hukumar, Chukwuemeka Ugboaja, ya wakilta, ya tsarin tantance mai karin rajistar hikima ce da basirar injiniyoin INEC ta kai su ga kirƙiro shi.

Ya ce BVAS zai ƙara wa INEC ƙarfin gwiwar tabbatar da cewa ta shirya zaɓe sahihi, wanda babu yadda za a iya yin maguɗi a lokacin zaɓe.

Ya ce: “Abu na biyu da zai ƙara wa zaɓen 2023 inganci shi ne sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022. Sashe na 9 (6) ya bai wa INEC ikon daina yi wa mutane rajista kwanaki 90 kafin zaɓe. Daga nan ne kuma sai hukumar ta tankaɗe tare da tace rajistar ɗungurugum.

“Kuma mutane su fahimci cewa INEC ba ta iya soke rajistar kowa. Amma ta na da ikon soke rajistar wanda ya yi rajista sau biyu.

“Hanya ta uku da za a kawo ƙarshen maguɗin zaɓe ita ce aikawa da sakamakon zaɓe kai-tsaye ta na’urorin kafafen sadarwa na zamani daga rumfar zaɓe.

“Sannan kuma Sashe na 51 na Dokar Zaɓe ta 2021 ya nuna ƙin amincewa da sakamakon zaɓen inda adadin ƙuri’un da aka jefa a akwati su ka haura adadin yawan waɗanda aka tantance ta tsarin BVAS.

“Sannan kuma a zaɓen 2023, Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2023 ta haramta wa INEC karɓar sakamakon da aka tilasta wa jami’in zaɓe bayyana sakamkon zaɓe.”

Ya buga misali da zaɓen sanata na Jihar Imo a 2019, wanda duk da cewa tilasta jami’in INEC aka yi ya karanta sakamakon zaɓen, amma kotu ta amince da sakamakon. Ya ce a yanzu ƙarƙashin sabuwar dokar zaɓe, hakan ba zai yiwu ba.

Daga ƙarshe ya yi kira ga manya da masu ilimi mazauna birane cewa su daure su riƙa fita su na jefa ƙuri’a a ranar zaɓe.

Ya nuna damuwa kan cewa mazauna birane, musamman masu hali da manyan ‘yan boko, ba su zuwa su na jefa ƙuri’a, duk kuwa da cewa sun san muhimmancin yin  zaɓen.

Loading

Tags: BVASChidi NwaforDokar ZaɓeINECmaguɗin zaɓemahmood yakubuYiaga AfricaZaɓen 2023
Previous Post

Rana ba ta ƙarya: Za a ɗaura auren Afakallah da Dawayya Juma’a mai zuwa

Next Post

Shin ƙungiyar 13×13 ta yi tuntuɓe a tafiyar ta ne?

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Aminu Alan Waƙa

Shin ƙungiyar 13x13 ta yi tuntuɓe a tafiyar ta ne?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!