ƘARSHEN tika-tika tik! Jiran da ake ta yi na ganin auren Shugaban Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano, Malam Isma’il Na-Abba (Afakallahu), da jarumar Kannywood Ruƙayya Umar Santa (Dawayya), ya zo ƙarshe, domin kuwa yau saura kwana huɗu a ɗaura auren su.
Za a ɗaura auren nasu da ƙarfe 2:00 na rana a ranar Juma’a, 4 ga Nuwamba, 2022 a Masallacin Juma’a na Tishama, a Kano.
Idan kun tuna, mujallar Fim ce ta fara ba da labarin cewa Afakallah zai auri Dawayya kwanan nan. A ranar 5 ga Oktoba, 2022 mun buga labari mai taken “Auren jarumar Kannywood Ruƙayya Dawayya da shugaban Hukumar Tace Finafinai, Afakallah ya matso
* Samun Afakallah a matsayin miji, Allah ne ya amsa addu’a ta – Dawayya”, labarin da kafafen yaɗa labarai da dama su ka kwafa su ka sake bayarwa.
A labarin, mujallar Fim ta ce: “Mujallar Fim ta ji daga wata majiya mai ƙarfi kan lamarin cewa shirye-shiryen bikin sun kankama.

A kan gaskiyar batun auren, majiyar ta ce: “To ai ba tun yanzu aka fara yin batun auren ba. Ko makaho a Kannuwood ya san akwai soyayya tsakanin Dawayya da Afakallah.
“Soyayya ce da aka daɗe ana yin ta a ƙarƙashin ƙasa, ba tare da sun bayyana wa duniya ta sani ba, sai a yanzu da aski ya zo gaban goshi ne ya sa ita Ruƙayya Dawayya ta fara ɗora hoton Afakallah a ‘status’ ɗin ta na WhatsApp da TikTok da kuma Instagram tare da yin wasu bayanai masu nuna alamar akwai soyayya mai ƙarfin gaske a tsakanin su.”
Majiyar ta ƙara da cewa: “Akwai maganar auren, kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci za a iya yin sa.
“Ana cewa ba wani taro za a yi ba, za dai a ɗaura aure ne kawai amarya ta tare, amma dai mu mun dage a kan lallai sai an yi dina. Dawayya ba ƙaramar jaruma ba ce, kuma shi oga kowa dai ya san matsayin sa da muƙamin sa a gwamnati da ma siyasa. Don haka, za mu yi biki sosai.
“Da zarar sun kammala shirin da su ke yi, za a ji sanarwar ɗaurin auren. Ba wani abu ba ne da za mu ɓoye.”
Allah ya kai mu ranar da rai da lafiya.
![]()







