• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Dattijo ya sha alwashin agaza wa Kadawood idan ya zama sanata

by DAGA ABBA MUHAMAD
October 28, 2022
in Labarai
0
Lokacin da Dattijo ke amsa tambayoyi

Lokacin da Dattijo ke amsa tambayoyi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar zama sanatan Kaduna ta Tsakiya a jam’iyyar APC, Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), ya bayyana irin gudunmawar da zai ba manishaɗanta, musamman na Kaduna da ake kira Kadawood in Allah ya ba shi nasarar cin zaɓe na 2023.

A shekaranjiya Laraba, 26 ga Oktoba, 2022, Dattijo ya yi bikin cikar sa shekara 43 a duniya, wanda aka yi a ɗakin taro na ‘Ahmed Musa Neibourhood Centre’ da ke Sabon Hanya, Kaduna.

A yayin da ya ke amsa tambaya kan abin da zai yi wa masu harkar nishaɗi idan ya samu nasara, ɗan siyasar ya ce ya ji daɗin wannan tambaya, sannan ya ƙara da cewa kamar shekara biyar da ta wuce Gwamnatin Tarayya na ba da tallafin kuɗi ga masu harkar nishaɗantarwa, amma ‘yan Kudu kaɗai ke amfana.

Ya ce: “Idan Allah ya ba mu nasara, za mu yi iyakacin bakin ƙoƙarin mu don ganin an samu damar amfana da irin wannan kuɗaɗe da ake bayarwa, musamman ‘yan Kadawood.”

Da jin haka, nan da nan ɗakin taron ya cika da sowa.

Tun farko dai ƙungiyar Kadawood sun samu gayyata ta musamman ne daga jaruma Asabe Madaki, wadda ta na daga cikin waɗanda su ka shirya bikin.

Nura MC, wanda shi ne shugaban Kadawood, shi ne ya jagoranci tawagar ‘yan fim zuwa wurin taron.

Bayan jawabai da abokan Dattijo su ka yi na taya shi murna, an kira ‘yan Kadawood don su ma su tofa albarkacin bakin su.

A daidai wannan lokacin sai Aƙilu Muhammad (Baban Mulika) ya yi wa Dattijo kirari cikin barkwanci a yadda ya ke shiri a matsayin Bayarabe.

Shugaban Kadawood, Nura MC, da su A.S. Muhammed a wurin taron

Bayan ya gama kuma sai Sani Ɗangwari ya amsa, inda ya zaro N2,000 ‘yan ɗari biyar-biyar ya ce wa Dattijo ga su gudunmawa ne, da ma da su ka je Kano Asiwaju ya ce su riƙa ba da gudunmawa. Bayan Dattijo ya amshi kuɗin sai Ɗangwari ya sauka daga dandamalin da abin magana a hannun sa ya ce wa mahalarta taron duk mai ƙaunar Dattijo ya zo ya biya shi kuɗin shi da ya ba Dattijo. 

Nan da nan kuwa ɗakin ya cika da ihu. Kan ka ce kwabo jama’a su ka yi ta zuba wa Ɗangwari da Moɗa kuɗi.

Wannan abu ya nishaɗantar da jama’a matuƙa. Shi kan shi Dattijo ya nishaɗantu, inda ya yi alƙawarin zai ba da lokacin da zai zauna da su don tattauna abubuwa muhimmai.

Daga nan ‘yan fim ɗin su ka yi masa godiya da sallama su ka watse. 

Waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Sani Idris Kauru (Moɗa), Aƙilu Mohammed (Baban Mulika), Baba Gwanki, A.S. Muhammed, Ibrahim Usman Muhammad (Al-Imash), Ibrahim Yalawa, Nura MC, Jamil Nafseen, Zaharaddin Mando, A.A. Rasheed Kabala, Nas M. Shareef, A’ishatu Umar Mahuta, A’isha NTA, Farida Mansur, Fauziyya Yola, Nafisa Little, da Fati Wuff.

Umar MB tare da Dattijo a wurin taron
Dattijo da ‘yan Kadawood a taron

Loading

Tags: APCKadawoodMuhammad Sani DattijoNura MCsanataUmar MBZaɓen 2023
Previous Post

Mawaƙi El-Mu’az ya maka mawaƙiya Ummi BY a kotu bayan ta kai shi kotu

Next Post

Rana ba ta ƙarya: Za a ɗaura auren Afakallah da Dawayya Juma’a mai zuwa

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Afakallah da Rukayya a wajen taron ƙaddamar da gidan kwalliyar da taAfakallah da Rukayya a wajen taron ƙaddamar da gidan kwalliyar da ta bude a Kano a makon jiya bude a Kano a makon jiya

Rana ba ta ƙarya: Za a ɗaura auren Afakallah da Dawayya Juma'a mai zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!