• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mawaƙi El-Mu’az ya maka mawaƙiya Ummi BY a kotu bayan ta kai shi kotu

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
October 27, 2022
in Labarai
0
El-Mu'az Birniwa da Ummi B.Y.

El-Mu'az Birniwa da Ummi B.Y.

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAWAƘIN Kannywood, El-Mu’az Muhammad Birniwa, ya maka mawaƙiya kuma jarumar finafinai Amina Abdullahi, wadda aka fi sani da suna Ummi B.Y., a kotu a Kaduna, mako uku bayan ta kai shi ƙara a wata kotun.

Ya shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Majistare da ke NDA Bus-stop a Kaduna a ranar 18 ga Oktoba, 2022.

Idan kun tuna, mun ba ku labari a ranar 27 ga Satumba, 2022 na yadda taƙaddama ta ɓarke a tsakanin mawaƙan biyu. A labarin, Ummi ta zarge shi da kawalci, zargin da shi kuma ya ƙaryata.

Bayan kwana biyu, sai ta kai shi ƙara a Babbar Kotun Majistare da ke Rigachikun, Kaduna, bisa babban laifin barazana ga rayuwar ta (direct criminal complaint for the offence of intimidation) wanda ya saɓa wa sashe na 377 na kundin finalkod na Jihar Kaduna na shekarar 2017.

To, shi ma irin wannan ƙarar ya kai ta, a kan zargin ɓata suna da yi masa ƙarya. Kamar yadda ita ma ta faɗa a ƙarar ta, shi ma ya faɗa wa kotu cewa abin da ta yi masa babban laifi ne a kundin shari’a na finalkod na Jihar Kaduna na shekarar 2017.

Haka kuma a ƙarar tasa El-Mu’az ya maƙalo Editan Riƙo na mujallar Fim, Abba Muhammad.

A sammacin da kotun ta tura wa Abba, sanannen mawaƙin ya yi iƙirarin cewa Abba ma’aikaci ne a kamfanin shirya finafinai, sannan kuma ya na zaton ɗan jarida ne da ke aiki a wata mujalla mai suna ‘Film Magazine’ wadda ba a san adireshin ta ba.

Labarin da mawaƙin ya faɗa wa kotu kan dalilin sa na yin ƙarar kusan shi ne wanda mujallar Fim ta buga a kan taƙaddamar a ranar 27 ga Satumba, mai taken, “Taƙaddama: Mawaƙan Kannywood biyu, El-Mu’az Birniwa Da Ummi B.Y. Sun Lakaci Hancin Juna.”

A labarin, El-Mu’az ya shaida kotun cewa lamarin ya fara ne daga wani tes da ya ce Ummi ta tura masa a ranar 12 ga Yuli, 2021 inda ta roƙe shi da ya sanya ta a harkokin sa na shirya finafinai, shi kuma sai ya ce mata ta koma ta biyo ta hannun jarumar Kannywood ɗin nan Hannatu Bashir tunda ya na ganin su tare. Ya ce ita Hannatu, ita ce furodusar sa.

Ya ce bayan haka sai Ummi ta buƙace shi da ya kai wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna waƙar da ta yi masa, tunda ta san alaƙar su, shi kuma sai ya amsa mata da cewa sai dai ta jira domin akwai layin waƙoƙi waɗanda sai an gama da su tukuna kafin a shigar da ta wani.

Ya ce daga nan Ummi ta buƙaci ya ba ta lambar wayar da ya fi amfani da ita, shi kuma sai ya ba ta ba da son ran shi ba. Daga nan ta dinga damun sa da kira, shi kuma ya na ƙin amsawa.

Ya ce ta ci gaba da aika masa da waƙoƙin ta, har ta roƙe shi da ya tura su ga kakakin majalisar da kuma Manjo-Janar Buratai (ritaya), amma ya ƙi.

Ya ce a ƙarshe dai, a ranar 8 ga Janairu, 2022 sai ta ɓara, ta shaida masa cewa ita fa kuɗi ta ke so ta yi ko ta wace hanya, saboda haka ta na so ya samo mata ko ma waye da zai cika mata burin ta, ko da kuwa ta hanyar lalata ne, amma sai ya faɗa mata cewa shi ba kawali ba ne. 

Ya ce sakamakon haka, sai ta je ta na ɓata masa suna a gari, wanda hakan ya sa ya faɗa wa Hannatu cewa ta gargaɗe ta a kan kada ta ƙara kiran shi a waya.

Ya ce Hannatu ta isar da wannan gargaɗin amma Ummi ta ƙi ji, sai ma ta tura masa wani guntun bidiyo inda ta nuna masa cewa ta na neman taimako saboda mahaifiyar ta ba ta da lafiya, shi kuma sai kawai ya yi mata addu’ar samun sauƙi amma bai ba ta komai ba.

Ya ce daga nan, lokacin da ya yi wani rubutu a ‘status’ ɗin shi, ya na ba mutane shawarar su nemi na kan su, sai Ummi ta zaci da ita ya ke, don haka sai ta je ta yi masa raddi irin na cin mutunci kuma ta shiga ɓata masa suna.

El-Mu’az ya faɗa wa kotu cewa wai da ma shi da Abba Muhammad (Editan mujallar Fim) ba su shiri, don haka sai Abban ya je ya zuga Ummi kan yadda za ta fashe haushin ta kan El-Mu’az ɗin. Mawaƙin ya ce a lokacin ya goge dukkan maganganun da ta tura masa a wayar sa.

Ya ce Abba ya kira shi a waya ya nuna masa cewa shi zai iya sasanta shi da Ummi, amma bai sani ba wai ashe Abban ya na rikodin dukkan wayar da su ka yi ne. A cewar sa, sai Abban ya caccanza tattaunawar tasu, ya je ya buga ta a wata mujalla da ke yanar gizo mai suna ‘Film magazine’ ba tare da izinin sa ba.

Ya ce da aka nuna masa labarin da mujallar ta buga, sai ya sa Hannatu ta kira Ummi ta tambaye ta abin da ya sa ta ke so ta ɓata masa suna, amma wai sai Ummin ta zazzage su shi da ita.

El-Mu’az ya ce saboda haka ya na so kotu ta hukunta waɗanda ya ke ƙarar idan ta same su da aikata laifi.

Kotun ta buƙaci waɗanda ake ƙarar da su bayyana a gaban ta a ranar 21 ga Nuwamba, 2022.

Loading

Tags: 'shari'a.Abba MuhammadEl-Muaz BirniwaHannatu BashirKadunakotumajistaremawaƙaMujallar FimsammaciUmmi BY
Previous Post

Za a horar da ‘yan Kannywood dabarun shirya fim bisa haɗin gwiwar MOPPAN da TAFTA

Next Post

Dattijo ya sha alwashin agaza wa Kadawood idan ya zama sanata

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Lokacin da Dattijo ke amsa tambayoyi

Dattijo ya sha alwashin agaza wa Kadawood idan ya zama sanata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!