A JIYA Lahadi, 16 ga Yuli, 2023 aka yi shagalin bikin mawaƙin gambara (hip-hop) Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh Al-Ameen ko Kano State Material, da tsohuwar jaruma kuma furodusa a Kannywood, Sayyada Sadiya Haruna, bayan ta dawo daga aikin Hajji.
An gudanar da shagalin ne a wani ƙayataccen ɗakin taro da ke cikin garin Kano.

Ɗakin taron ya ciki maƙil da ‘yan’uwa da abokan arziki, inda aka yi nishaɗi da waƙoƙi irin na mutanen Maiduguri, wato garin da amaryar ta fito. Haka kuma wasu matasan mawaƙa sun nishaɗantar da mahalarta.
Sai dai kuma wani abu da ya ba da mamaki shi ne ganin jaruma Teema Makamashi a wurin bikin, inda ta yi ta zubar da naira, ta na yi masu liƙi. Duk wand ke bibiyar soshiyal midiya, ya san cewa Teema da Sadiya ba su ko ga maciji, domin an sha ganin su su cin mutuncin juna a soshiyal midiya.
Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ba da labarin ɗaurin aure a watan da ya gabata.

An ɗaura auren nasu a ranar Juma’a, 16 ga Yuni bayan sallar Juma’a a Masallacin Sheikh Isyaka Rabi’u da ke Goron Dutse cikin birnin Kano, a kan sadaki N200,000, wato a jiya su ka cika wata ɗaya cif da aure.
Allah ba su zaman lafiya, amin.


