• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 26, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumar Kannywood Ummi Rahab ta zama matar mawaƙi Lilin Baba ta biyu

by DAGA ABBA MUHAMMAD
June 18, 2022
in Ranar Murna
2
Ummi Rahab da Lilin Baba a ranar auren su

Ummi Rahab da Lilin Baba a ranar auren su

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHI KENAN, alƙawari ya cika. An ɗaura auren fitaccen mawaƙi, furodusa kuma jarumi Shu’aibu Ahmed Abbas (Lilin Baba) da fitacciyar jaruma Rahama Saleh Ahmed (Ummi Rahab), a yau Asabar, 18 ga Yuni, 2022.

An ɗaura auren nasu da misalin ƙarfe 11:00 na safe a wani masallaci da ke NEPA Office, daura da gidan Bala Kasa, a Tudun Murtala, Kano, a kan sadaki N200,000.

Fitaccen jarumi Ali Nuhu shi ne waliyyin Lilin Baba, wanda ya karɓi auren. Da ma shi ne wanda ya kai sadakin tun a watannin baya.

‘Yan fim sun yi wa abokan sana’ar tasu kara, domin kuwa kusan duk wani mai ji da kan sa a Kannywood da ya amsa sunan jarumi, furodusa, darakta, mawaƙi da sauran su ya halarci ɗaurin auren. 

Ango Lilin Baba (a dama) da aminin sa Umar M. Shareef a Bristol Palace Hotel, Kano, sun yi anko kafin su tafi wurin ɗaurin aure

Sai dai mujallar Fim ta lura da cewa Nazir M. Ahmad da Adam A. Zango, Yakubu Muhammad da Sani Danja ba su halarci ɗaurin auren ba.

Daga nan wurin ɗaurin auren an ɗunguma zuwa wurin cin abinci  wato ‘reception’, wanda aka yi a Meena Events Centre da ke Titin Lodge, Nassarawa, Kano. An ci, an sha, an kuma gyatse.

Kafin ranar ɗaurin auren an shirya wasan ƙwallon ƙafa a jiya Juma’a, wanda mata da mazan Kannywood da dama su ka halarta.

Wani furodusa ya shaida wa wakilin mu cewa lallai an jima ba a yi bikin da ya tara ‘yan Kannywood haka ba.

Cincirindon jama’a a wurin ɗaurin auren Lilin Baba da Ummi Rahab.

A cewar sa, ba komai ba ne ya jawo wa angon haka ba sai “irin zuciyar da ya ke da ita ta taimakon jama’a”.

Ya ƙara da cewa, “Lallai ta tabbata Lilin Baba mutumin kirki ne matuƙa. Don haka wannan kawai ya ishi waɗanda ba su taimakon mutane izina.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Lilin Baba mutum ne mai tattalin iyalin sa, domin duk wani mai mu’amala da shi a industiri, duk kusancin ka da shi ba ka isa ka ce ka ga matar sa ba.

Ya na da uwargida, wata ‘yar garin Jos wadda su ke da ɗa ɗaya da ita. Wata majiya ta ce yaron har ya girma, ya na zuwa makaranta.

Ummi Rahab dai ita ce matar Lilin Baba ta biyu a yanzu. 

Daga hagu: Muhammad Dabo, Abubakar Bashir Maishadda, Ali Nuhu, Alhaji Sheshe da Naziru Ɗanhajiya a wurin walimar cin abinci (reception)

Duk da kasancewar sa matashi, kuma mai ɗimbin arziki, bai yarda da a yi dina a bikin sa ba kamar yadda ‘yan Kannywood su ka saba yi.

Ummi Rahab dai za ta tare ne a Kaduna, garin da mijin ta ya ke da zama.

Wani makusancin sa ya shaida wa mujallar Fim cewa Lilin Baba ya gina wa Ummi gida a jikin gidan da uwargidan sa ta ke, kowacce da get ɗin ta. Kuma duk gidajen nasa ne na kan sa, ba haya ba ne.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

Daga hagu: Abdul M. Shareef, KB 2-Effects, Marafa, Alfazazi da Musty Fashion a wurin walimar cin abinci
Ummi Rahab ta yi shigar amarci

Loading

Tags: Ali NuhuaureKadunaKannywoodKanoLilin BabamawakiRahama Saleh AhmedUmmi Rahab
Previous Post

‘Soyayyar Facebook’: Hadiza Gabon ta faɗa wa alƙali: Ban san mai iƙirarin neman aure na ba

Next Post

Hotunan bikin Lilin Baba da Ummi Rahab (1)

Related Posts

MC Kabir Bahaushe zai ƙara aure ran Asabar
Ranar Murna

MC Kabir Bahaushe zai ƙara aure ran Asabar

July 22, 2025
Furodusa a Kannywood, Shu’aibu Yawale ya aurar da ‘ya’ya biyu
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Shu’aibu Yawale ya aurar da ‘ya’ya biyu

July 18, 2025
Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya

July 16, 2025
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli zai yi aure ranar Asabar

July 10, 2025
Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida
Ranar Murna

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida

June 29, 2025
Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani
Ranar Murna

Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani

June 19, 2025
Next Post
Hotunan bikin Lilin Baba da Ummi Rahab (1)

Hotunan bikin Lilin Baba da Ummi Rahab (1)

Comments 2

  1. Abubakar usuman dindima says:
    3 years ago

    Daga jahar bauchi Nima inayi masu fatan alkairi Allah ya basu zama lfy

  2. Maryam hussaini says:
    3 years ago

    CommentAllah yabasu zuri’ah dayyibah!!!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!