TA tabbata jarumin Kannywood Abdullahi Amdaz ya zama mai igiya biyu.
Amdaz ya ƙara aure a jiya Asabar, 30 ga Disamba, 2023 a garin Maiduguri, Jihar Borno.
An ɗaura auren nasa da abar ƙaunar sa A’isha Umar Timta da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan Sarkin Gwoza da ke Titin Gombale, kusa da makarantar Capital, Giwa Barracks.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.