• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 18, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Idris

by WAKILIN MU
April 23, 2025
in Nijeriya
0
Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Idris

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana magana da manema labarai jin kaɗan bayan saukar su a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja. A hagu, Gwamna Umaru Bago ne.

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce nasarar tashin jirgin kasuwanci na farko daga Filin Jirgin Sama na Bola Ahmed Tinubu da ke Minna alama ce ta haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi wajen bunƙasa cigaban ƙasa.

Yayin da jirgin ya sauka a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, Ministan ya jaddada cewa cigaban ƙasa mai ɗorewa zai yiwu ne kawai idan gwamnatoci a matakai daban-daban sun haɗa ƙarfi da ƙarfe tare da daidaita manufofi da haɗa albarkatu.

Ya ce: “Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da muke buƙatar tattaunawa a kan su shi ne irin haɗin gwiwar da Shugaban Ƙasa yake yawan yin kira a kai tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jihohi. Wannan shi ne babban misali da Jihar Neja ta nuna cewa jihohi za su iya haɗa kai da Gwamnatin Tarayya don kawo cigaba ga ‘yan Nijeriya.”

Shi dai filin jirgin saman, wanda gwamnatin Umaru Bago ta gina a Jihar Neja, an raɗa masa sunan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Jirgin kasuwancin na farko mallakin kamfanin Overland Air mai lamba 5N-CCN ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana.

Cikin fasinjojin akwai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, Minista Mohammed Idris, tsohon Gwamnan Neja Dakta Babangida Aliyu, Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, da wasu manyan jami’an gwamnati.

Hagu zuwa dama: Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Babangida Aliyu; Ƙaramin Ministan Aikin Gona Da Samar Da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi; Shugaban Kamfanin Overland Air, Mista Edward Boyo; Gwamnan Jihar Neja, Hon. Umaru Bago, da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, lokacin saukar jirgin farko na kasuwanci daga Minna zuwa Abuja a yau Laraba.

Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda samar da yanayin da ya bai wa filin jirgin damar fara aiki, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen inganta ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.

Haka kuma, Ministan ya jinjina wa Gwamna Bago bisa hangen nesa da jajircewar sa na buɗe Jihar Neja ga cigaban noma da kasuwanci da masana’antu da kuma inganta tattalin arzikin jihar.

Ya ce: “Dole ne mu yaba wa shugaban ƙasar mu kamar yadda gwamnan mu ya faɗa. Wannan haƙiƙa mafarki ne da ya zama gaskiya. Gwamnan ne ya sa hakan ya tabbata. Yana da kwaɗayin ganin Jihar Neja ta buɗe ƙofar cigaba ta fannin noma, kasuwanci, masana’antu da kuma bunƙasar tattalin arziki.”

A nasa jawabin, Gwamna Bago ya ce wannan jirgi na farko wani ɓangare ne na buɗe jihar zuwa ga duniya baki ɗaya.

Ya ce: “Shugabannin kamfanin Overland sun nuna karamci matuƙa wajen ba mu wannan sabon jirgi daga Legas zuwa Minna, sannan yanzu daga Minna zuwa Abuja, kuma hakan zai riƙa faruwa sau uku a mako – a ranakun Litinin, Laraba da Juma’a. Wannan jirgi ne na buɗe hanya – buɗe Jihar Neja ga sararin samaniyar duniya.

“Muna son gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda filin jirgin ya samu suna daga gare shi, saboda ya ba mu dukkan goyon bayan da muke buƙata.”

Gwamna Bago ya ƙara da cewa jihar tana da niyyar amfani da filin jirgin wajen fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje don haɓaka tattalin arzikin jihar da zama ɗaya daga cikin manyan masu fitar da kayan noma daga Nijeriya.

Loading

Tags: filin jirgin samaGwamna Umaru BagoMinnaMohammed Idris
Previous Post

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

Next Post

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

Related Posts

Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano
Nijeriya

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

July 5, 2025
Next Post
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

Ƙarshen tika-tika, tik! A'ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!