INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa kakar jarumi kuma darakta a Kannywood, Falalu A. Ɗorayi, rasuwa.
Hajiya Amina, wadda ake kira Nene ko Yakumbo ko Yadikko, ta rasu a yau a Kano, ta na da shekara 110 a duniya.
A sanarwar rasuwar da Falalu ya turo wa mujallar Fim, ya bayyana cewa za a yi jana’izar ta a yau d ƙarfe 12 na rana a Gidan Maƙera da ke unguwar Ja’en Ɗorayi.
Da fatan Allah ya yi mata rahama, ya kyautata makwancin ta, amin.