• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

KILAF AWARD 2024: An buɗe taron bajekolin finafinai na Afirika

by MUKHTAR YAKUBU
November 26, 2024
in Labarai
0
KILAF AWARD 2024: An buɗe taron bajekolin finafinai na Afirika
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

An buɗe taron bikin bajekolin finafinai na Afirika karo na 8 wanda aka saba gudanarwa a duk shekara, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market & Festival.’

An fara gudanar da bikin ne a jiya Litinin 25 ga Nuwamba 2024 inda za a shafe tsawon kwanaki 5 ana yi.

A rana ta farko dai an buɗe taron ne a ɗakin lakcoci a sashin koyar da aikin jarida na Jami’ar Bayero in da manyan masana akan aikin jarida da kuma harkar fim suka gabatar da jawabai na tsawon wuni guda.

Haka nan a wani ɓangare kuma an buɗe taron hosarwa akan harkar fim da kasuwancin sa wanda yake shi ɓangare biyu ne, akwai babban aji da kuma ƙaramin aji a sashin koyar da ilimin harkar kasuwanci na Dagote duk dai a cikin Jami’ar Bayero.

Da yamma kuma an gudanar da taron liyafar maraba da baki a gidan cin abinci na Gusto dake cikin Unguwar Nassarawa G R A.

A wajen liyafar cin abincin dai shugaban gudanar da taron.l, Malam Abdulkareem Muhammad, ya gabatar da jawabin maraba da baƙi inda a cikin jawabin yake cewa:

“Muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan rana da za a fara wannan taro na Kalankuwar Afirika wanda har ma ya zama al’adar mu a duk shekara Allah yana bamu damar gudanar da shi. Kuma abin farin ciki da alfahari baya ga ilimin da ake samu taron ya zama wani dandamali na sada zumunta a tsakanin mu, da kuma ƙulla abota.

“A yanzu ga shi mun haɗu a waje guda cikin jin daɗi da farin ciki tare da rungumar juna. Kuma ko ba komai wannan abin alfahari ne a gare mu mu ‘yan Afirika da muke yare da al’adu mabambanta yau ga shi mun haɗu domin musayar ra’ayi da kuma sada zumunta. Muna yi wa baƙin mu maraba da suka zo daga ƙasashe masu nisa da waɗanda suka zo daga kusa kamar maƙwaftan mu Nijar da Kwatano.

“Haka nan muna yin maraba da baƙin mu da suka zo daga jihohi daban-daban har ma waɗanda suke nan garin Kano. Mun gode Allah da ya sa a yi taro lafiya a gama lafiya, kuma Allah ya mayar da kowa gidan sa lafiya.”

Taron dai ya samu halartar Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, da Kwamishiyar Ma’aikatar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko, tare da sauran manyan baƙi.

Loading

Previous Post

Shugabannin Ƙungiyar Daraktoci ta PROPDA sun karɓi rantsuwar kama aiki

Next Post

Furodusa a Kannywood, Abdul Amart, ya zama shugaban kwamitin tantancewa na zaɓen MOPPAN

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Furodusa a Kannywood, Abdul Amart, ya zama shugaban kwamitin tantancewa na zaɓen MOPPAN

Furodusa a Kannywood, Abdul Amart, ya zama shugaban kwamitin tantancewa na zaɓen MOPPAN

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!