JARUMAR Kannywood Fati S.U. Garba ta yi kira ga masu hannu da shuni da su sani cewa ciyarwa ya fi ɗaukar nauyin wa’azi a gidan rediyo ko talbijin a cikin watan Ramadan da za a shiga nan da kwanaki kaɗan masu zuwa.
Jarumar ta yi wannan roƙo ne a wani saƙon WhatsApp da ta tura wa dukkan abokan da ke da lambar ta inda ta ce, “In dai kai Musulmi ne nagari kuma Allah ya yi maka hali da arziki, don girman Allah kar ka ɗauki nauyin wa’azi a cikin Ramadan ɗin nan ko a gidan radiyo ko talbijin. Yi amfani da kuɗin ka wajen ciyar da al’umma, ba wai shirye-shiryen wa’azi ko sa kiran sallah ba, (Ramadan programs).
“A yanzu al’umma ba su buƙatar waɗannan ‘programs’ ɗin wallahi. Alhaji ka ciyar ya fi lada.
“Don girman Allah kar ka biya wa mutane aikin Hajji ko Umara a wannan shekarar, wannan miliyan 6 ɗin na zuwa aikin hajji raba ta ga mutane 60, kowa N100,000, wallahi za ka ga albarka a dukiyar ka fiye da yadda ka ke tunani.
“Mutane abinci su ke buƙata ba wai wa’azi ko kiran sallah ko zuwa aikin Hajji ba. Yunwa ake gagaruma, ƙasa ta rikice. Allah ta’ala ya kawo mana sauƙi a Nijeriya ƙasa ta.”
Fati ta yi ƙarin bayani da cewa, “Asalin rubutun da harshen Turanci ne, amma na fassara zuwa Hausa don ‘yan’uwa masu hannu da shuni su faɗaka.”
Jarumar ta na da gidauniya mai suna ‘Sulhatee Poverty Alleviation Foundation’, wadda ta ke taimaka wa, marayu, marasa ƙarfi da gajiyayyu.
Ga duk mai son taimakawa, ga lambar asusun gidauniyar nan: Sunan asusu: Sulhatee Poverty Alleviation Foundation. Lambar asusu: 1024995743. Banki: UBA.