• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, May 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumin barkwanci a Nollywood, Mista Ibu ya rasu

by ALI KANO
March 2, 2024
in Labarai
0
Jarumin barkwanci a Nollywood, Mista Ibu ya rasu

Marigayi John Okafor (Mista Ibnu)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN jarumin barkwanci ɗin nan a finafinan Kudu (Nollywood), John Okafor, wanda ake yi wa laƙabi da Mista Ibu, ya rasu a yau Asabar da yamma.

Ya rasu ne bayan an garzaya da shi sashen kulawar gaggawa (ICU) na Asibitin Evercare da ke unguwar Lekki a Legas kwanaki kaɗan da su ka gabata.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Mista Ibu ya rasu ya na da shekaru 62 a duniya sakamakon bugun zuciya bayan ciwon sa ya tashi kamar mako ɗaya da ya gabata.

Idan kun tuna, a watan Oktoba 2023 labari ya ɓulla na rashin lafiyar da ya yi har ya na neman agajin kuɗi.

A Nuwambar 2023 kuma iyalan sa su ka bayyana cewar an yanke masa ƙafa ɗaya don kada ya mutu.

Tsohon manajan sa, Emeka Chochoo, ya faɗa wa jaridar Punch a watan Nuwamba da ya gabata ɗin cewa tilas ta sa aka yanke ƙafar domin wani rauni ya cinye masa hanyoyin jini a ƙafar wanda ba a gano shi da wuri ba.

Iyalan mamacin sun tabbatar da mutuwar jarumin ga manema labarai.

Shi ma Shugaban Ƙungiyar Jarumai ta Nijeriya (AGN), Emeka Rollas, ya tabbatar da mutuwar.

Labarin wannan babban rashi ya girgiza ‘yan Nollywood da dama da kuma masoyan sa masu kallon finafinan sa.

‘Yan Nollywood na ta tura saƙonnin ta’aziyya a soshiyal midiya.

Jaruma Mercy Johnson Okojie ta ce, “Sai godiya… Allah jiƙan ka oga…”

Ita kuma Ruth Kadiri ta ce, “Allah jiƙan ka Baba.”

Wannan mutuwa ta Mista Ibu ta biyo bayan rasuwar wani jarumin na Nollywood, wato Tolani Quadri Oyebamiji, wanda aka fi sani da Sisi Quadri, wanda ya rasu a jiya Juma’a aka rufe shi a yau a garin su na Iwo, a Jihar Osun.

Loading

Tags: Emeka RollasJohn OkaforMr Ibumutuwanollywood
Previous Post

Kiran jaruma a Kannywood Fati S.U. Garba ga masu hali: Ku taimaka da abinci ba ɗaukar nauyin tafsiri ko kiran sallah cikin Ramadan ba

Next Post

Hajiya Sahuratu, mahaifiyar furodusa Musa Carlos ta kwanta dama

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Hajiya Sahuratu, mahaifiyar furodusa Musa Carlos ta kwanta dama

Hajiya Sahuratu, mahaifiyar furodusa Musa Carlos ta kwanta dama

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!