FITACCEN darakta, furodusa kuma jarumi Falalu Ɗorayi ya yi kira ga masu kokwanton koronabairus da su daina, ya ce wannan cuta gaskiya ce.
A wani saƙon musamman da aika wa jama’a a shafin sa na Facebook a yau Juma’a, Ɗorayi ya ce: “Hakika da yawa daga cikin mutane har yanzu ba su yarda da sahihancin zancen da ake faɗa game da cutar nan mai sarƙe numfashi ba, wato ‘coronavirus’.
“Tabbas, babu ko shakka, wannan cutar gaskiya ce, domin ta yaɗu a ƙasashen duniya, ciki har da ƙasar mu Nijeriya.
“Kawo yanzu, kaɗan ne daga cikin jihohin mu wannan cuta ba ta leƙa ba.”
Jarumin ya yi nuni da cewa ta hanyar yi wa cutar taron dangi ne tare da bin umarnin gwamnati da masana ne za a magance cutar.
“Mu haɗa kai da tunani waje guda domin yaƙar wannan cutar mai barazana ga farin cikin mu, ta hanyar bin dokoki da sharaɗai da gwamnati ta gindaya mana, da kuma ɗaukar shawarwarin masana game da yadda za a daƙile wannan cutar,” inji shi.
Ɗorayi ya yi fatan alheri ga jama’a tare da kasancewa cikin bin tsarin Allah.
Ya rufe bayanin sa da addu’a kamar haka: “Allah, waɗanda su ka kamu da cutar ka ba su lafiya, waɗanda su ka mutu, ka yi musu rahama.”