• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kotu ta kulle jarumin fim shekara 5 saboda auka wa ƙaramar yarinya

by DAGA ALI KANO
July 14, 2022
in Labarai
1
Olarenwaju James, wanda aka fi sani da Baba Ijesha

Olarenwaju James, wanda aka fi sani da Baba Ijesha

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA Kotun Musamman Kan Laifuffuka da ke unguwar Ikeja a Legas a yau Alhamis ta yanke wa wani fitaccen jarumin fim hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan waƙafi saboda ta same shi da laifin auka wa ƙaramar yarinya.

Jarumin, wanda ya yi fice a finafinan Nollywood, Mista Olanrewaju James, wanda aka fi sani da laƙabin Baba Ijesha, ya auka wa yarinya ‘yar shekara 14 ne.

A yayin da ta ke yanke masa hukunci, Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo, ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun samu nasarar tabbatar da laifin auka wa ƙaramar yarinyar tare da aikata aikin assha wanda shi wanda ake zargin ya aikata.

Sai dai alƙalin ba ta kama shi da laifi kan zargi na farko da na shida da aka yi masa ba, kuma ta wanke shi a kai, wato shiga cikin jikin yarinyar ta hanyar al’aurar ta (wanda aka ce ya faru a shekarar 2014) da kuma ƙoƙarin yin fyaɗe ta hanyar shiga cikin al’aurar ta (wanda ya faru a cikin 2021).

Bugu da ƙari, ta bayyana cewa rahoton likita da aka kawo ba kammalalle ba ne domin likitan bai tabbatar da cewa karcewar da aka gani a jikin yarinya na tun shekaru bakwai da su ka shuɗe ne ko kuma na kwanan ne ba.

Ta ce: “Abin tambaya a nan shi ne ya shige ta shekaru bakwai da su ka gabata kafin wanda ya faru a cikin 2021 amma ba mu san waye ya aikata hakan ba ko kuma lokacin da abin ya faru.

“Wadda aka aikata wa laifin ba ta taɓa kai rahoton wancan al’amari ga uwar ta ba a wancan lokacin, saboda duk wani rauni da aka ji mata a farjin ta zai iya kasancewa ya ɓace shekaru bakwai da su ka gabata.

“Ita kan ta wadda aka aikata wa laifin ta faɗa wa kotu cewa samari na saurin jan hankalin ta har ma wani mai suna Kawu Damola ya taɓa kai mata farmaki.”

Mai Shari’a Taiwo ta ce a bayanin amincewa da aikata laifi wanda shi wanda ake zargin ya bayar akwai inda ya ce ya rungumi wadda ya aikata wa laifin shekaru bakwai da su ka gabata bayan abin da ya fara faruwa a tsakanin su inda ya tsotsi yatsun ta har ya tayar mata da hankali amma ya ƙaryata cewa ya tsira mata ‘yan makullai a cikin al’aurar ta.

“Wanda ake zargin ya amince cewa da gaske ne ya  shafa jikin yarinyar a cikin 2021.

“Kotu za ta iya yanke wa mutum hukunci a bisa furucin sa na amincewa da aikata laifi. Wanda ake zargin bai sauya maganar amincewa da aikata laifi ba a cikin fayafayen bidiyo guda biyu da aka gabatar.

“Zafin da mai bada shaida ta farko (wato Princess) ta bayyana na gaske ne. Yarinyar ta na cikin fargaba kuma mun ga tsoro muraran a cikin idanun ta a lokacin da ta ke bada shaida a gaban kotu. Ta ga tilas ne ta bada shaida.

“Bayanin da masu kare wanda ake zargi su ka yi na cewa wai masu gabatar da ƙara sun kasa bayyana ainihin shekarun wadda aka aikata wa laifi ba karɓaɓɓe ba ne domin abin da doka ta ce shi ne duk wani mutum ɗan ƙasa da shekara 18 ana ɗaukar sa a matsayin ƙaramin yaro ne.

“Ba lallai ba ne cewa wanda ake zargin ya yi tunanin ya yi lalata da wadda aka aikata wa laifi a wannan ranar, to amna ya tayar mata da hankali ta hanyar tsotsar mata yatsun hannu tare da shafa jikin ta. Bai tuɓe kayan sa ba a lokacin da ya ke tayar mata da hankalin.

“A nan ina bayyana cewa na samu wanda ake zargin da laifi a zargi na biyu zuwa na biyar amma an wanke shi kan zargi na ɗaya da na shida.

“Don haka a nan an yanke wa wanda ake zargi hukuncin ɗaurin shekara biyar a kan laifi na biyu, shekara uku a kan laifi na uku, shekara biyar a kan laifi na huɗu, da kuma shekara uku a kan laifi na biyar.

“Shekarun za su tafi tare da juna saboda roƙon da aka gabatar, kuma za su fara daga yau, 14 ga Yuli.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa kafin a yanke hukuncin sai da lauya mai kare wanda ake zargin, wato Mista Gabriel Olabiran, a roƙon da ya gabatar, ya buƙaci kotun da ta taimaka ta ba wanda ake zargin hukunci mafi ƙaranci saboda kada abokan hulɗar sa su juya masa baya.

Olabiran ya ce wannan shi ne karo na farko da aka samu wanda ake zargi da aikata laifi, ya ce kuma ya shiga mugun yanayin damuwa na tsare shi da aka yi a ofishin ‘yan sanda na Panti da kuma gidan yari na Kirikiri.

Ya ce: “Babu shakka wanda ake zargin ya yi nadama matuƙa. Mai girma Mai Shari’a, mu na roƙon ki da ki yi la’akari da cewa wanda ake zargin ɗan wasan fim ne wanda ya bada kyakkyawar gudunmawa ga al’umma ta hanyar sana’ar sa.

“Mu na kira ga mai girma Mai Shari’a da ta yi sassauci ga wanda ake zargin, wanda ya rasa kusan dukkan mutuncin sa a duk faɗin duniya kuma abokan aikin sa a masana’antar shirya finafinai za su juya masa baya.

“Ya na da iyaye da su ka tsufa, da matar sa ta aure, da ɗan sa waɗanda su ka dogara da shi kuma su na sa ran ganin sa ya dawo gida. Mu na tabbatar wa da kotu cewa wanda ake zargin mutum ne wanda ya sauya hali, wanda ba zai koma ya sake tafka ta’asa ba.

“Mu na kira ga kotu da ta tausaya masa ta yanke masa hukunci mafi ƙaranci.”

Sai dai su lauyoyi masu gabatar da ƙara, a ƙarƙashin jagorancin Daraktan Sashen  Ƙararrakin Jama’a (DPP), Dakta Babajide Martins, sun bar wa kotu damar yanke hukunci yadda ta ga dama.

Dakta Martins ya ce: “Shari’a ta kammala aikin ta. Laifuffukan da mai girma Mai Shari’a ta gano cewar wanda ake zargin ya aikata sun shafi hukuncin tsarewa a gidan yari ne.

“Laifi na biyu na ɗauke da shekara bakwai, laifi na uku na da shekara  huɗu, laifi na huɗu na da shekara bakwai, sannan laifi na  biyar na da shekara uku.

“Amma dai mu, mun bar yanke hukunci ga yadda kotu ta ga ya dace.” 

Mujallar Fim ta ruwaito cewa shi dai Baba Ijesha an fara gabatar da shi a gaban Mai Shari’a Taiwo ne a ranar 24 ga Yuni, 2019 a kan zargin laifi guda shida da su ka danganci rashin kyautatawa ga ƙaramar yarinya, da auka mata ta hanyar fasiƙanci, da ƙoƙarin yi mata fyaɗe ta hanyar shiga al’aurar ta.

A cewar lauyoyi masu gabatar da ƙarar, Baba Ijesha ya auka wa yarinyar ‘yar shekara 14 wadda jarumar barkwanci Damilola Adekoya, wadda aka fi sani da Princess, ta ke riƙo a gidan ta.

Masu gabatar da ƙarar sun kawo shaidu shida a kan Baba Ijesha a lokacin da ake tafka shari’ar. 

Shaidun sun haɗa da ita jaruma Princess, da yarinyar ‘yar shekara 14, da wata masaniyar halayyar ƙananan yara mai suna Misis Olabisi Ajayi-Kayode, da likita Dakta Aniekan Makanjuola.

Sauran su ne ɗan sanda mai binciken ƙara, ASP Wahab Kareem, da ‘yar sanda mai suna Sufeto Abigail Omane.

Masu gabatar da ƙara sun kammala bayanan su kan wanda ake zargi ga kotun a ranar 15 ga Disamba, 2021 yayin da lauyoyin Baba Ijesha su ka kawo shaidu huɗu kuma su ka rufe bayanan kare kai a ranar 1 ga Afrilu, 2022.

Shaidun wanda ake ƙarar su ne shi kan shi Baba Ijesha  (mai kare kai), da Mista Lawrence Ayeni, wanda gwanin shirya bidiyo ne da sanya kyamarar CCTV da kula da ita, da Olukayode Olugbemi, likitan halayyar ɗan’adam, da Mista Olukayode Ogunbanjo, abokin wanda ake zargi kuma abokin sana’ar sa.

A cewar masu gabatar da ƙarar, laifin ya saɓa wa tanade-tanaden sassa na 135, 259, 261, 262 da 263 na Kundin Dokokin Laifuffuka na Jihar Legas na 2015 (Gyararre).

Loading

Tags: Baba IjeshaBabajide MartinsFinafinaifyaɗeGabriel Olabirangidan yarijarumiJihar LegaskurkukulaifiMai Shari'a Oluwatoyin TaiwonollywoodOlanrewaju James
Previous Post

Matan Kannywood ne matsalar masana’antar, inji dattijo Auwalu Marshall

Next Post

Allah ya shiryi masu yaɗa labarin ƙaryar wai na mutu, inji Ali Artwork

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post

Allah ya shiryi masu yaɗa labarin ƙaryar wai na mutu, inji Ali Artwork

Comments 1

  1. Pingback: Kotu ta kulle jarumin fim shekara 5 saboda auka wa ƙaramar yarinya - LastNg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!