BABBAR Kotun Shari’ar Musulunci (Upper Shari’a Court) da ke Bichi, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Bello Musa Khalid ta aika wa kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano takardar umarnin gudanar da bincike a kan fitaccen mawaƙi Ado Isa Gwanja da wasu mutum tara.
Umarnin, wanda aka bayar a takarda mai ɗauke da kwanan wata 30 ga Agusta, 2022, ya biyo bayan ƙarar da wasu lauyoyi su ka su ka shigar kan shi Gwanja da mawaƙi Mubarak Abdulkarim (Mr. 442), Safeeya Yusuf (Safara’u), Ɗanmaraya, Amude Booth, Kawu Ɗansarki, Murja Ibrahim Kunya, Ummi Shakira, Samha M. Inuwa da Babiyana a kan zargin ɓata tarbiyya.
A takardar, wadda mujallar Fim ta samu kwafen ta, an lissafa sunayen lauyoyin kamar haka: Badamasi Sulaiman Gandu, Muhammad Ali Hamza, Abba Mahmud, Muhammad Nasir, L.T. Dayi, G.A. Badawi, Sanusi I. Umar da A.T. Bebeji.

Taken takardar da aka aika wa kwamishinan shi ne: “Neman gudanar da bincike a kan Mr. 442, Safara’u, Ɗan Maraya, Amude Booth, Kawu Ɗansarki, Ado Isa Gwanja, Murja Ibrahim Kunya, Ummi Shakira, Samha M. Inuwa da Babiyana.”
Binciken mujallar Fim ya gano cewa tun da farko dai wani lauya ne mai suna Barista Badamasi Sulaiman Gandu ya ba da wa’adin kwana uku ga hukumomin Hisbah da na Tace Finafinai da Ɗab’i na Jihar Kano a kan su ɗauki mataki a kan mawaƙi Ado Gwanja, game da sabuwar waƙa mai taken ‘Chass’, wadda ake zargin ya yi amfani da kalaman batsa a cikin ta, idan kuma ba haka ba zai garzaya kotu.
Abubuwan da aka yi ƙarar a kan su sun haɗa da yin wasu waƙoƙi da aka ce sun yi karo da addini da al’ada, masu taken ‘Warr’ da kuma ‘Chass’ waɗanda Gwanja ya yi, sai kuma sauran da ake zargin su da hawa waƙoƙi su na bidiyo su na tiƙar rawa na rashin mutunci da kamun kai, wanda zai iya ɓata tarbiyyar al’umma.
A wata sabuwa, shi ma Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Usman Alƙali Baba, ya umarci kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano da ya gudanar da bincike a kan Ado Gwanja da Safara’u.
Hakan ya biyo bayan koken da wani mutum mai suna Alhaji Muhammad Lawal Gusau ya gabatar wa da sufeto-janar ɗin a kan cewa Gwanja da Safara’u su na ɓata tarbiyya.
Sufeto-Janar ɗin ya aika wa kwamishinan da umarnin a takarda mai ɗauke da kwana wata 1 ga Satumba, 2022 inda ya ce a binciki mawaƙan biyu.
Takardar ta ce Muhammad Lawal Gusau ne ya kai ƙorafi a kan su a ranar 29 ga Agusta, ta ce shi ne mamallakin wata makarantar koyar da addinin Musulunci da ke garin Gusau mai suna Ma’had wa Nasjid Li Marhoom.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Lawal Gusau mutum ne wanda ya saba kai ‘yan fim kotu ko ya shigar da ƙara a kan su a wajen jami’an tsaro.
Wasu daga cikin waɗanda ya yi wa haka a baya sun haɗa da Fati Ladan, Rahama Sadau, Maryam Booth da Maryam Yahaya.
Ita duniya ba sai ka bayyana adan iska za kai popular ba ka bayyana mutumin kirki shine babba d tsoho zasu sanka km su soka. Abunda kuke yi dai dai y ke d izgilanci ga shugaba S.A.W d km Musulunci, km kun nunawa Duniya cewa baku yadda d Akwai Hisabi ba.
FATEE A.J.A
(Script writer)