A JIYA Talata, 21/4/2020, ne Allah ya yi wa mahaifin fitacciyar jaruma Sadiya Muhammad Gyale rasuwa. Alhaji Muhammad Tukur ya rasu da misalin ƙarfe 6:30 na yamma a gidan sa da ke unguwar Sagagi Ƙofar Na’isa a cikin garin Kano.
Marigayin, mai shekaru 85, ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya 15 da jikoki 27, cikin su har da ita Sadiya.
An yi jana’izar sa a yau da safe.
‘Yan fim da dama sun yi wa Sadiya ta’aziyya.
Mu na fatan Allah ya jiƙan sa, ya bai wa iyalai da ‘yan’uwa haƙurin jure wannan babban rashi, amin.